Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
yanayin salon nata ya nuna cewa hada ɗaukar fansa take yi,' 😳😳😳
A asibiti marshal omar ya barsu hussana a hannun Camila kafin zuwa da safe zaisa a sallame su,
shi da major suka wuce izuwa gida saboda kiran wayarsa da ake ta faman yi ga kuma tsananin damuwar daya shiga game da halin dasu Fawan ke ciki,
daker sehrish tasamu ta fito sam tagaza samun natsuwa ta ko ina, ta damu da yanayin da taga Sgr da kuma halin da fawan ke ciki, a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya sannan ta kwankwasa tare da jiran ta buɗe mata,
  tana tsaye azmee ta bude ƙopan tana kallonta tace "kin gama kukan?
 Shiru kawai tayi tana wasa da yatsun hannunta,Â
"hmmmm me kike yi ma kuka ne É—azu"?
Cikin sanyin murya tace"babu komai Aunty azmee kawai nadamu ne da halin dana ga fawan,'
 Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "gsky yaji jiki sosai, nima na tausaya masa bawan Allah, Yakamata muje mu duba shi, dama na jira ne mutane su ɗan rage sosai,"
Sehrish tace "ae nagama babu kowa a falon bansan inda suka kai shi ba,"
"Sun kwantar dashi ne, a É—akin da suke kwantar da mara lafiya, bari nazo mu tafi tare, inyaso in mun dawo sai mu jera masu dinner É—in duk da nasan abune mai wuya ma a samu wanda zai iya cin abincin, don duk suna cikin damuwa," tana fadin haka tashige cikin É—akin bada jimawa ba ta fito sanye da mayafi, sannan suka jera da sehrish izuwa É—akin dake anan downstairs,
A buÉ—e suka same shi don haka su kayi sallama, muryar kanal yusif ce ta amsa masu tare da cewa "ku shigo ciki mana,"Â
  shiga ciki sukayi sehrish har tsoran kallon jikin fawan takeyi, wanda ke kwance saman gadon idonshi arufe alamar ya samu bacci,
Ayaan da jahad ne zaune daga gefen gadon sai kanal yusif dake atsaye,
Azmee tace "Yusif ashe haka abu ya faru? Mu ba mu sani ba"!
 Kanal yusif yace "Wlh kuwa aunty azmee abun babu daɗin ji, ƴan ta'adda ne su kayi masu kwanton 6auna, amma anci nasarar Cafke wasu daga cikinsu,"
 Cikin nuna jimami aunty Azmee tace "Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin waɗannan mutanen, wlh duk jikina ya mutu dana ga fawan acikin wannan halin bawan Allah, Allah dae ya tashi kafaɗunsa,"
 Suka amsa mata da ameen, sai lokacin sehrish tace "Yaya yusif ya mai jiki"?
 Yace "Alhamdulillah da sauƙi sosai harma ya samu bacci,"
  Tace "Allah ya bashi lafiya,"
 "Ameen ," suka amsa mataÂ
Kanal yusif yace "Aunty azmee ku matso kusa dashi kuyi mashi addu'a yana buƙatarta sosai," matsawa su kayi atare kusa da fawan suna yi masa addu'a tare da tattofa masa, daga bisani su kayi masu sallama suka fito waje
 Kitchen suka wuce atare don sun shirya abincin dining azmee tace "bari na haɗa maki, ki kaima babban yayansu nasan zai buƙaci wani abun,"
  "Toh," ta amsa mata, suna cikin kitchen ɗin haroon ya shigo cikin babban falon daga waje ya shigo ciki hango sehrish da yayi yasa shi wuce wa cikin kitchen ɗin, kamar yarda ya saba fado masu batare da sallama ba haka ya shiga,
  ɗagowa su ka yi suna kallon shi hankalin shi kwance tamkar baisan meke faruwa ba, azmee tace "haroon me kake buÆ™ata ne"?Â
 tsoki ya ɗan ja tare da cewa "tun yaushe nake ta faman zarya ina jiran a jera mana abincin dare amma shiru babu, so ake akashe ni da yunwa ne"? yayi maganar fuska aɗaure yana kallon sehrish wadda tuni ta kawar da kanta,
 Azmee tace "kayi haƙuri haroon, saboda halin da su fawan ke ciki ne ga kuma mutane shiyasa ba mu samu damar fitowa ba mun jera,"
 Uban tsoki ya kuma bugawa wanda har sai da suka ɗan razana suka kallesa yace "And then so what? Mutuwa fawan ɗin yayi ne da zaku fake da cewa halin da yake ciki ya hana ku jerawa mutane abincinsu"? Ya tambaya a ƙule
 Mamakine ya kamasu jin abunda yace yadda ya nuna ko ajikinsa halin da fawan ke ciki,
  nuna sehrish yayi da hannu tare da cewa "Ke! ki kawo mun abinci na yanzun nan a bedroom ɗina ina jiran ki,
 Cikin sauri sehrish tace "Ni babban yaya zan kai mawa yanzu, sai dai ko in aunty azmee ta jera a dining ka zauna ka ci,'Â
 Zaro ido haroon yayi afusa ce yace "Ke! Ni kike fadama cewa wani wai babban yaya zaki kaima abinci"? Ke ga futsararra ko"? ya tambaya yana faman huci
  da ido azmee tayi ma sehrish alamar tayi shiru da bakinta, tsit tayi bata kuma cewa komai ba,
 cike da bada umarni yace "Ina jiran ki ki kawo mun idan kuma ba haka ba zaki ga mai zai biyo baya," yana faɗin hakan ya fuce daga kitchen ɗin,
 Murya tamkar zatayi kuka tace "Aunty azmee nifa bazan kai masa ba Allah,"
 Azmee tace "sehrish ki daure ki kai masa, nikaina na tsorata da yarda yake mana magana, ina tunanin kamar yayi shaye-shaye ne baya cikin hayyacinsa,"
  "Aunty azmee nifa bazan kai masa ba,kema da kan ki kince baya cikin hayyacinsa yanzu in naje zai iya kai mun bugu,"
  ganin ta dage akan cewa ba zata je ba yasa Azmee cewa "to shikenan bari ni nakai masa, ke kuma ki kaima Sgr nasa," ajiyar zuciya sehrish ta saki tare da cewa "to,"
bayan sehrish ta kammala shirya masa a tray ta wuce upstairs part É—insa, sallama tayi ba'a amsa ba don haka tashiga daga ciki, babu kowa acikin falon alamar yana a cikin bedroom É—insa,
  takawa tayi izuwa ƙopar bedroom ɗin nasa tayi masa sallama kusan sau uku sannan ya amsa mata da cewa"Come in,"
 Shiga ciki tayi zuciyarta na dar-dar lokacin da ta aza idonta akanshi yana zaune gaban dressing mirror saman chair din dake gaban madubin, ya sanya tafin hannayensa ya tallabo gefe da gefen fuskarsa ya zabga tagumi agaban mirror, sam babu riga ajikin shi daga shi sai short green colour, da alama ma daga wanka ya fito yagaza yin komai shine ya zabga tagumin, Sumar kanshi duk ta barbazo ta rufe masa gefen face dinsa, da wasu siraran gashi da suka sauko ta saman fuskarsa idonshi na arufe saboda gajiyar da ta lullu6e ga66ansa da kuma baccin da yake ji ga kuma yunwa duk shi kaɗai
tsayawa sehrish tayi jiki asanyaye tana kallon shi tsananin tausayin shi ne yakamata ganin yarda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, alamar baya jin daÉ—i
 Ta jima tana kallon shi kafin ta ɗanyi gyaran murya tace "dama abinci ne na kawo maka, bansan ko kana buƙata ba," ta fadi adan tsorace gudun kar tayi kuskure a maganarta,
  daker ya buɗe bakinsa tare da cewa"keep it on the table, then i wanna see u," gabanta ne ya faɗi rass ! jin abunda yace na yana son ganinta ƙarasawa tayi ta ajiye masa dinner din saman table ɗinsa, sannan ta matsa kusa dashi ta tsaya sannan tace "gani,"
 Hannu yasa ya ɗauko wata ƙaramar kwalba ta magani daya ajiye a saman mirror din sannan ya miƙa mata tare da cewa "rub it on my back," ya fadi tare da kifa kansa saman gaban mirror ɗin yadda zata samu damar murza masa maganin,
tama rasa ta ina zata fara shafa masa shi, gaba daya duk tabi ta rikice wai yau itace sgr da kansa ya bata magani don ta shafa masa abayansa, jikinta har kerma yakeyi tsoranta kar ta fasa masa fatar bayansa saboda hasken fatar fes tamkar in kasa yatsa jini zai fito,
 Matsawa ta Æ™ara yi dab dashi sosai sannan ta buÉ—e mufin kwalbar, tasa yatsa ta lakuto maganin tare da É—an russinawa ta lakuta masa shi abayan, sannan tasanya hannunta a hankali tana shasshafa masa shi, tun da Allah ya halicce ta bata ta6a jin skin mai tsananin laushi da daÉ—in tabawa ba irin fatar bayan sgr,Â
Shi kuwa ajiyar zuciya kawai yake saukewa saboda relief daya fara samu sosai na ciwon da ga6o6insa suke masa, tun sehrish nayi masa da hannu É—aya har takai ga ajiye kwalbar maganin ta sanya duka hands É—inta a faffaÉ—an bayansa tana yi masa massage, a tunaninsa in ta kammala zata cire hannunta ne, amma sai yaga ta zarce gaba É—aya babu alamar zata daina shafa masa gashi kuma yaji ko'ina na bayansa yaji maganin sosai, shiru kawai yayi bai ce komai ba, almost one hour kenan sehrish na shafa masa magani har sai da ya É—an É—ago da kansa daga kwancen da yake tare da cewa "Har yanzu maganin bai shafu bane"? Cikin sauri ta janye hannunta tare da É—agowa tana kallonsa suka haÉ—a ido ta cikin mirror,
 gabanta ne taji ya Æ™ara faÉ—uwa rass ganin yarda kwayar idonsa ke shining sai taga tamkar tana canza launi ne daga blue zuwa green,. Â
 sunnar da kanta tayi ƙasa tana faman haɗe yatsun hannunta dake dankare da maganin data shafa mashi,
lumshe idonsa yayi tare da sake buɗe su yace "kin haɗo mun da coffee ne? ya tambaya a kasalance hakan ba ƙaramin kashe ma sehrish jiki yayi ba, tuni ta nemi natsuwarta tarasa sai ta kama en ena tana faman wurwurga ido
 "Its ok, idan babu akawo mun shi," ya faɗi tare da mayar da idonshi ya lumshe su,
Juyawa sehrish tayi cikin sauri ta fuce izuwa kitchen donta haÉ—o masa, a lokacin har azmee ta kammala shirya masu abincin dinner É—in a dining amma babu kowa asaman shi alamar basu kaiga fitowa ba,
 tayi mamakin hakan duk da tasan cewa duk suna cikin damuwa ne,bata ji daɗin hakan ba, tasa ba ganin mutanen gidan cikin raha suna nishaɗi suna cin abinci yau kuma wayaam babu kowa, Yau da gobe kenan,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.