Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
A fusace Amstrong ya zabura zai É—auke shi daga saman gadon don ya rugurguzashi dasauri Sgr ya dakatar dashi"Ka barni dashi,Na ishe shi,"
 "Bansan wanene yake tunzuraka ba haroon,Amma inaji araina cewa Sanyaka akeyi kana yi,Laifin me muka aikata maka?da har muka cancanci hakan a wurinka?me junaid ya aikata maka da har kayi silar mutuwarshi?duk irin halarcin da akayi maka acikin gidan karasa dame zaka saka mana sai wannan?Da wani ido kake tunanin Abbanmu zai kalleka?Ya ta6a banbantamu dakai ne"?
 "Banbanci kuma na yaushe?babu mai sona acikin gidan nan,ba ku damu dani ba,bakusan halin da nake ciki ba,kowa kuna nuna mashi so da ƙauna acikin gidan nan,Ni kaɗaine kuka ware kamar wani bare,"yana magana yana kuka
 "Nikaina bada son raina nayi silar mutuwar junaid ba,ɗacin raɗaɗin ƙuncin da kuke cusa munne yasa har nasa aka bi takanshi da mota,Yanzu bana jin tsoran kowa yaji cewa Na kashe junaid,Saboda nima so nake na mutu,tun ranar dana kashe Junaid na gaza samun kwanciyar hankali,duk wani mugun abu da nake aikatawa na daina duk don saboda shi,haƙƙinshi kaɗai ma bazai barni inyi rayuwa cikin salama ba,Duk ni najawa kaina wannan masifar da nake ciki........"sosai ya fashe da matsanancin kuka,gaba daya basu yarda da kalamanshi ba,Yana yin magana tamkar wanda yayi danasani,
 "Ka fadamun wanene yake baka Command kana aikata hakan?idan har ka faɗamun zan ƙyaleka kayi tafiyarka,"
 Girgiza kai Haroon ya shiga yi yayin da hawaye ke kwaranyowa daga cikin idanuwanshi"Wlh bazan iya faɗa maka ba!bazan iyaba,da ace zan iya dana fada maka,Amma bazan iya ba,"
 Jinjina kai Sgr yayi tare da miÆ™ewa tsaye yana kallonshi"its okey,tunda baza ka faÉ—amun ba,Amstrong É—aukarshi ka mayar dashi É—akin horon nan,".Â
 Fashewa haroon yayi da matsanancin kukan Yana ƙoƙarin dakatar da Amstrong akan karya ɗaukeshi,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai Yayi ba,
 "Leave him,"Ya ambaci hakan tare da dakatar da amstrong daga ɗaukarshi,"
 Allura Sgr ya ɗauko,Aikuwa a firgice haroon ya shiga girgiza mashi Kai yana fadin"kada ka kashe ni dan Allah,kabarni da raina,inason Na nemi yafiya a wurin Abba kafin nabar duniya...."
 "Kasan daɗin ranka meyasa shi junaid ka kashe shi baka bari ya gana da iyayenshi ba?Haroon Rayuwarka bata da amfani"Turmushe shi Amstrong yayi,Sgr ya Caka mashi allurar a wuyanshi,lokaci guda jikinshi ya saki gaba ɗaya,Lokaci guda idanuwanshi suka kakkafe,daga bisani ya sanƙare babu numfashi,
Tashin Hankali!Haroon Zai rayu Koya mutu?Ya sehrish ƙare acikin toilet ɗin Azmee ga futsari ya matse ta,Junaid Yana raye Koya Mutu?Am confused
*Ga duk maison Abban sojoji ya tuntu6i Layina whatsapp message kawai banda call 08103884440*
💋ð”¹ð• ð•¤ð•¤ ð”¹ð•’ð•¥ð•¦ð•£ð•–💋
ð‘—ð‘œð‘–ð‘› ð‘¡ð’‰ð‘–ð‘ ð‘™ð‘–ð‘›ð‘˜ ð‘¡ð‘œ ð‘“ð‘œð‘™ð‘™ð‘œð‘¤ ð‘šð‘¦ ð‘‡ð‘–ð‘˜ð‘¡ð‘œð‘˜ ð´ð‘ð‘ð‘œð‘¢ð‘›ð‘¡ðŸ‘‡
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة ØØ¨ رومانسية بين Ø³ØØ±ÙŠØ´ ÙˆØ§Ù„Ø¬Ø±Ø§Ø Ø§Ù„Ø¹Ø§Ù… Ø±ÙØ§ÙŠØªâ¤ðŸ¤â¤
ð¹ð‘Žð‘¡ð’‰ð‘’𑟠ð‘‚ð‘“ ð‘†ð‘œð‘™ð‘‘ð‘–ð‘Žð‘Ÿð‘
*🔥ð•‹ð•’ð•œð•¦ð•Ÿ ð•‚ð•’ð•£ð•¤ð•™ð•–🔥*
Not edited
.Anan suka barshi saman gadon batare da sun kawar dashi ba,
Har zasu fita daga É—akin sgr ya kalli Amstrong"Wayarshi nakeso ka É—auko mun,Nasan dole akwai wasu mahimman bayanai da yake ajiyewa acikinta,"
Juyawa Amstrong yayi tare da nufar Haroon dake kwance magashiyan saman gadon,Hannu yasa cikin aljihun wandonshi Ya lalubo wayarshi tare da key É—in Motarshi,dawowa yayi ya mika mashi su duka,hannu Yasa ya kar6esu daga hannun Amstrong,
Bayan sun fito daga ɗakin,Sgr Yayi Locking ɗin ƙopar,Sallama su kayi da Amstrong ya wuce upstairs part ɗinshi,
Gaba ɗaya ƙyanƙyamin jikinshi ya ke ji,blood ɗin Haroon daya fallasar mashi duk ya 6ata Shirt ɗin jikinshi,quickly yake taka staircases ɗin harya haura Sama,Lokacin daya ƙarasa Cikin Falonshi,yayi expecting ɗin zai sameta aciki,yaji daɗin ganin yadda ta gyara ko'ina gwanin ban sha'awa,kullum furniture ɗin ɗakin kamar sabbi suke komawa duk in suka sha gyara,
A hanzarce ya wuce cikin bedroom É—inshi,
Ya zancen sehrish da take ƙumshe cikin toilet ɗin Azmee,Ta shiga matsanancin tashin hankali,ba laifi bane idan ta shiga toilet ɗin Azmee,matsalar da aka samu shine Wayar da tayi picking,in Azmee ta ganta zata gane cewa itace ta ɗaukar mata waya,
Jiki na rawa ta sauko daga saman bucket ɗin,Tasa hannu ta ɗago shi cikin sanɗa ta mayar dashi inda ta ɗauko shi,komawa tayi bakin ƙopar toilet ɗin ta tsaya,Duk tabi ta tsorata,fitsarin da take ta faman matsewa ne ya kufce mata nan take ya shiga fitowa Ziiir ta tsakankanin cinyoyinta,Runtse idanuwanta tayi sosai Cikin zuciyarta tana ambaton"Allahumma Ajirni filmasibati aklifni khairan minha'
Tana cikin wannan yanayin Kwatsam Ba zato ba tsammani tajiyo Muryar Azmee daga cikin É—akin tana cewa"Sehrish idan kin gama la6e la6en naki,ki fito kizo ki kwanta dare nayi,"
 Gabanta ne taji yayi wani irin mugun bugu,Zuciyarta tamkar zata 6allo daga ƙirjinta,Idanuwanta sun Zazzaro waje kamar ƙwayar idon zata faɗo ƙasa
 Jin tayi shiru yasa Azmee ta ƙara ɗaga muryarta"ke fa nake Jira!"
Wani irin wahalallan Yawu ta haɗiya abakinta,Tashin Sense,kenan duk wannan la6e la6n da take yi Azmee tasan da zamanta acikin Toilet ɗinta How that Can be possible?Bayan batasan Lokacin da ta shiga cikinshi ba,Wannan ya ƙara firgitar da ita,
 "Ko saina Shigo cikin toilet ɗin nan"?
 Muryarta na kerma tace"A'a gani nan zuwa,"
 Tayi maganar tare da nufar tap ta kunna ruwa ya shiga kwararowa,Ɗebo ruwan tayi ta yayyafa shi a jikinta sosai Ta wanke fitsarin,'
Gabanta na faɗuwa ta nufo ƙopar,Yatsun hanunta na kerma ta buɗe ƙopar ta fito,
A bakin ƙopar toilet ɗin ta tsaya,kamar an dasa mata Aya,Idanuwanta na kallon ƙasa,
Juyowa Azmee tayi tare da kallonta,Sam babu wani sauyi akan fuskarta,Sai ma cewa tayi"Ya akai naga wandon jikinki a jiƙe"?
 La66anta na rawa tace"Fitsari ne ya matse ni,ina ƙoƙarin nayi shi ne ya zubo mun,Amma na wanke shi,"
 "Eyya,duk kin bi kin jiƙa jikinki,Sanyi zai iya kamaki,bari na ɗauko maki kaya ki sanya,"
 Da sauri Sehrish ta dakatar da ita"A'a aunty Azmee,Zan koma ɗakin mu ne,"
"Why"?tayi tambayar da É—an mamaki akan fuskarta,
 "Ba'anan kike kwana ba"?
"Eh,Zan dawo akwai abunda zanyi acan"tana magana jikinta na kerma,
 Gyaɗa kai Azmee tayi"its Okey,Sai kin dawo,".
 Da sauri da sauri sehrish ta lalla6a ta nufi ƙopar fita daga ɗakin Harta ruƙo handle ɗin ƙopar zata buɗe,muryar azmee da katse mata hanzarinta"Take care of ur self"shi ne abunda taji tace mata,Ai ko waiwayonta bata yi ba,gudu gudu sauri sauri ta fito daga ɗakin Azmee,A haukace Ta faɗa bedroom ɗinsu,tana shiga ta fara jin ƙaiƙayi ajikinta,Hannu tasa tana sosa wuyanta,Abu kamar wasa bayanta ya ɗauka,cinyoyinta duk suka ɗauka ko'ina na jikinta,da gudun gaske ta faɗa cikin toilet,After some minutes ta fito ɗaure da towel,Ƙaiƙayin ya rage amma akwaishi kamar lafawa yayi,wadrobe taje ta buɗe tare da ɗauko Ƴar rigar bacci shara shara rigar haka take,Zura ta tayi ajikinta,har lokacin tana sosa jikinta,Burinta taje part ɗin Sgr don tasan Zai jirane ta kawo mashi coffee,turaren nan nata ta fesa ko mai bata tsaya shafawa,duk jikinta ba daɗi,
Slipper ta zura a kafarta,quickly ta nufi ƙopar ɗakin ta buɗe,Ta yafa mayafi akanta,Kitchen ta shiga shaf shaf within mins ta fito hannunta ɗauke da Cup of coffeee hada Fuits ta haɗo mashi,Don ya jima bai shasu ba,
Gadan gadan ta nufi cikin babban falon,tun tana tafiya ta soma jin wani irin kuka kuka Kamar na namun dawa,hakanan ta dake don bata kawo aranta ba,lokacin da ta ƙarasa Part ɗinshi,ta shiga falon da sallama bata same shi aciki ba,Bedroom dinshi ta shiga,Tana aza ƙafarta karaf idanuwanta suka sauka Akan Sgr wanda ke zaune Tsakiyar gadon jikinshi sanye da Sleeping dress ɗinshi,Yana daddana Laptop ɗinshi gaba daya ya mayar da hankalinshi akanta,gabanta ne ya faɗi Rass Lokacin da idanuwata suka fara nuna mata danƙara danƙaran kunamai A kewaye dashi suna ƙoƙarin Harbinshi,
Waro ido tayi waje tare da Sakin tray din dake hannunta,Ta fasa wata irin razananniyar ƙara wadda ta firgitar dashi,A hanzarce ya ɗago yana kallonta,Ta toshe kunnuwanta jikinta sae kerma yake yi,A ruɗe ta dinga nuna shimfiɗarshi tana fadin"Ya Rafayet Majici!kunama!zasu ɗalle ka gasu nan gasu nan Ya rafayet ka tashi....."Gaba daya gizan tsoranta sun tashi,To Fa,
Abun yayi matuƙar ɗaure mashi,Shi dai baiga komai ba,A wurinda yake zaune,Janye laptop ɗin yayi saman mattress ɗin,Gently ya sauko daga saman gadon ya tunkareta,Fashewa ta sake yi da uwar ƙara kamar maƙoshinta zai 6allo waje,Macijan nan ta gani tare da kunaman sun sauko daga saman gadon sun biyo Sgr suna ƙoƙarin sarin Kafarshi,
 Muryarta na kerma ta shiga fadin"Ka janye ƙafarka ya rafayet!gasu nan wlh gasu nan wurin ƙafarka zasu sare ka,Zasu cinye maka ƙafafunka....."
 Ƙarasawa yayi tare da ruƙo ƙafaɗunta,girgiza ta yayi"Hey!what's wrong with u?A ɗan tsawace yayi maganar,aikuwa nan take ta sume mashi Asaman wide chest dinshi ta faɗa,hannunshi yasa sosai yayi hunging ɗinta,Still abun ya bashi mamaki ya kuma ɗaure Mashi kai,wurga idanuwanshi yayi ƙasa saman tiles ɗin ɗakin mai kama da glass,Kayan marmarin da ta kawo mashi ne yashe a ƙasa sun tarwatse hatta cup ɗin Ya fashe,sigh yayi tare da mayar da idanuwanshi Kan sehrish dake sume a ƙirjinshi,bin fuskarta yayi da kallo,jiƙe take sharkaf da hawaye,la66anta duk sun bushe,tafin hannunshi ya sanya a saman kanta ya ɗan shafa sumar kwantacciyar sumarta,mayafinta tuni ya jima da sulalewa ƙasa,ɗaukarta Yayi gaba ɗaya saman kafaɗarshi Ya juya da ita izuwa wurin Katafaren gadonshi,Ya Kwantar da ita,kafin ya miƙa hannu ya dauke laptop ɗinshi Ya wuce da ita Palour don bai kammala aikinshi ba,
Almost 30 mins Yana zaune saman Sofa Yayin da yake daddana laptop É—inshi,after Ya kammal aikin,Ya rufe ta,anan ya barta ya nufi fridge ya dauko Bottle water mai sanyi,walking slowly ya shiga bedroom É—in,
Saman gadon Ya haye har izuwa saitin inda take akwance,emotionally yake kallon kyakkyawar fuskarta,expcially soft brownish lips ɗinta,tausasan gaske masu matuƙar fisgarshi,cire murfin bottle din yayi,ya tarfa ruwan a hannunshi,Ya yayyafa mata nan take ta soma sauke nauyayiyar Ajiyar zuciya,Ajiye robar yayi Saman side drawer ɗinshi,Still yayi yana kallonta,Yadda numfashinta ke fita duk in taja shi sai ƙirjinta yayi sama,da alama ta zarce da yin bacci ne,
Saukowa Yayi daga saman gadon sai da ya fara tsince Fruit ɗin da ta zubar mashi a ƙasa tare da cup ɗin data fasa duka ya tattarasu W cikin ƙaramin tray ɗin data zubo su, Ya kaisu palour,saman table ya ajiye plate ɗin,bayan ya ɗauki Laptop ɗinsa daya bari,bedoom ya koma bayan ya ajiye laptop ɗin,Ya ƙarasa wurin switch Ya kashe Hasken dakin,Nan take furniture ɗin suka fara haskaka ɗakin
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.