Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
sam bai lura da mutum a cikin bedroom ɗin nashi ba,gadan gadan ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,cikin rashin sani tafin ƙafarshi ya hau saman 6awon ayabar daya ci ɗazu,ya maƙale masa a jikin shirt ɗinsa saida zai shiga wanka ne ya lura dashi yasa hannu ya ka6e shi ya faɗi anan ƙasa,aikuwa nan take wani irin mugun sul6i ya kwashe shi bazato ba tsammani gaba ɗaya ya tafi a burkice zai faɗi,a firgice sehrish ta juya tare da yin ƙoƙarin taimaka mashi cikin sauri ta ruƙo shi nan take ƙarfin shi ya rinjayi nata gaba daya suka faɗa saman shimfiɗeɗen gadonshi a manne da juna,tashin hankali da ba'a sama shi date,
 wata irin nauyayyiyar azuciyar zuciya Sgr yashiga saukewa,tabbas ya ɗan firgita saboda bai tsammaci hakan ba,bai ta6a yin irin wannan gangancin ba,hada ƙarin sam ya manta da 6awon ayabar a wurin bai jefa shi dustbin ba,da ace sehrish bata ruƙo shi ba awannan lokacin da ba ƙaramin buguwa zaiyi ba yanda yake dogon nan,
  atare zuciyoyinsu suka shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,gaba ɗaya sehrish ta gama tsorata abun tamkar a amafarki take ganin shi,ta gaza yarda cewa itace tare da Surgeon general Rafayet kwance asaman gado ɗaya kuma amanne da juna,
  gaba ɗaya jikinshi ya rufe nata hatta face ɗinta tana a saitin wide chest ɗinshi,tana jin yarda yake ta faman sauke ajiyar zuciya,da kuma yarda heart ɗinshi ke beating very fast,
  tsit kake ji daga ita harshi an rasa mai wani kwakkwaran motsi,danshin ruwan dake ajikinshi ba ƙaramin sanyaya mata jikinta yayi ba,daƙyar take iya breathing saboda hancinta daya manne da fatar ƙirjinsa,haka la66anta ma suna manne da fatarshi,
 Boss man ɗin fa ya gaza ɗago da jikinshi daga nata,ba don komai ba sai don yarda abun yazo mashi unexpected,ba ƙaramin jinjinawa lamarin yayi ba shi kanshi,
  Jin yarda yarinyar keta kokawa wurin fitar da numfashinta,yasa ya daure tare da yunkurawa zai tashi daga jikinta,baiyi wani aune ba towel din dake ɗaure a qugunshi ya shiga warwarewa gaba daya dama daurin ya saki,
 Shi kanshi baisan lokacin daya mayar da jikinshi asaman nata ba ya kwantar da kanshi a saman left shoulder dinta,bakomai ne yasa yayi hakan ba face gudun kar towel din jikinshi ya saki agabanta,don muddin hakan ta faru tofa wannan karon ba sume mashi zatayi ba,zuciyarta ce zata buga tabar duniyar saboda tsabar firgici don ya lura yarinyar ba ƙaramar matsoraciya ba ce,
   wani irin yanayi mara misaltuwa taji atattare da ita,jikinta yayi wani irin sanyi sanyi kasala kasala haka,sam bata jin nauyin jikinshi akan nata sai ma yanayin da hakan ya jefa ta,
   idanunta na'a rufe sam tagaza buɗesu ba don komai ba sai don tsoran abunda zai biyo baya,a matuƙar tsorace take hakan yasa ko kwakkwaran motsi tagaza yi,lumshe idanunshi yayi yayin da hancinshi ke gogar fatar wuyanta,fragrance ɗin turarenta ne yake kaimashi ziyara acikin hancinshi,ƙamshin ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,har lokacin tana jin yarda numfashinshi ke fita afatar jikinta,
 almost 15mins suna cikin wannan yanayin,tajiyo hannunshi a hankali ya zura shi adai dai saitin waist ɗinshi don ya gyara ɗaurin towel dinshi,wannan moving ɗin da ya runka yi da hannunshi awurin yana gogar jikinta ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,amace ta mace gaba ɗaya tashiga wani irin yanayi na daban....,
  sai da ya samu ya ɗaure towel ɗin sannan a ƙaro na biyu ya ɗago da kanshi don ya raba jikinshi daga nata,nan take sehrish ta saki wata irin razananniyar ƙara gaba ɗaya ta gigita shi,ashe raɗaɗin Earring ɗinta ne daya sargafo gashin kanshi ya harɗe acikin ɗan kunnan,wannan ɗagawar da zaiyi ajikinta shine sumar kanshi taja ɗan kunnan nata da ƙarfi wannan ne dalilin dayasa ta fasa ƙara,cikin sauri Sgr ya mayar da kanshi tare da kwantar dashi agafen fuskarta,fashewa da kuka sehrish tayi sosai saboda ba ƙaramin zafi taji ba,don wurin harya fara fidda ɗigon jini,a hankali ya buɗe blue eyes ɗinshi tare da bin kunnan nata da kallo yarda sumar kan nashi ta harɗe acikin earring ɗin shine yafi komai bashi mamaki,tunani ya soma yi taya za'ai ya cire gashin nashi acikin ɗan kunnan nata?dole akwai buƙatar yabi a hankali wurin zagayo da hannun na dama don ya cire shi,
  A hankali ya ɗago da fuskarshi daga gefen fuskarta,ya kasance cewa suna facing ɗin juna sosai,hatta numfashinsu yana haɗewa dana juna,wannan shessheƙar kukan da takeyi ne yaja hankalinshi wurin kallon fuskarta,la66anta har kerma sukeyi yayin da idanunta ke arufe,
 Muryar shi ce ta katseta da cewa"I don't wanna hear that sound again,"
 Cikin sauri sehrish ta tsagaita dayin kukan gaba daya,ta koma tana faman sauke ajiyar zuciya,
 buɗe idanunta tashiga yi waɗanda ke cike tab da ruwan hawaye,tun kafin ta ƙarasa ware idanun nata take hangen hasken blue ɗin kwayar idanun shi,a hankali ta ƙarasa buɗe idanun sosai akan kyakkyawar fuskarshi dake fuskantar tata,duk da irin bugun zuciyar da take ji amma hakan baisa ta mayar da idanunta ba ta rufe su,
  A natse ta soma bin pink lips ɗinshi da kallo shape ɗinsu ba ƙaramin kyau ne dasu ba,tausasan gaske,mayar da eyes ɗinta tayi akan dogon hancin shi da tsinin ke dab da nata hancin,ta jima tana kallon hancin nashi daga bisani kuma a hankali ta aza idanunta acikin nashi nan take taji wani irin bugun zuciya,
   sai faman lumshe idanunshi yake yana kuma opening ɗinsu saboda baccin da yake ji,dama agajiye ya dawo cikin gidan,a hankali yake ɗan waresu akan idanunta,anatse yake bin long eyes lashes din idonta da kallo,har yanzu akwai sauran tears dake dripping a cikin idonta,sun jiƙa eyes lashes ɗin nata sharkaf,
  Eyes balls ɗinta yabi da kallo a lokacin itama nata na'a kan kwayar idon tashi tana ƙarewa launin idon nashi kallo,kasa janye idanunshi yayi acikin nata,kamar yarda itama tagaza janye nata acikin nashi duk da tsoran kwayar idon nashi da take ji,
  Suna cikin wannan yanayin a hankali ya zagayo da right hand ɗinshi ta saman kanta,ya ƙaraso dashi wurin ɗan kunnan nata sannan ya haɗa da hannun shi na hagu ya shiga ƙoƙarin cire gashin nashi daga jikin earring ɗin nata,
       runste ido sehrish tayi saboda zafin da take ɗan ji a wurin,ganin hakan yasa ya haɗe fuskokinsu awuri guda,jin yarda lips ɗinsa suka manne da nata tamkar zaiyi kissing ɗinta hakan ba ƙaramin rikitar da ita yayi ba,
  duk yarda yaso ya cire gashin daga jikin ɗan kunnan abun ya gagara ganin hakan zai 6ata mashi lokaci yasa yayi deciding tsinka gashin kan nashi daya sargaho earring ɗinta,
  Cikin sa'a ya katse gashin nashi yabar mata sauran siraran da suka ruƙo dan kunnan nata,
  Sai da ya raba ɗan kunnan sannan yaji wata irin kasala ta baibaye shi,lokaci guda ya rasa karfin janye jikinshi daga nata,ya dai samu ya ɗan janye face ɗin shi daga nata,sai kan head ɗinshi ya koma asaman boobs ɗinta,lamo yayi yana jin wani irin yanayin da bai ta6a ji ba arayuwarshi har wani bacci sosai ya dinga fisgarshi,sehrish kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita don bazata iya jurewa wannan yanayin ba,hannunta na asaman waist ɗinshi ta ƙankame shi sosai ajikinta,hada ƙarin hakan ya ƙara kashe mashi nashi jikin,
 Mamakine ya kama hayaam ganin cewa har yanzu Yarinyar bata fito daga part ɗin sgr ba,ashe tun bayan da sukayi magana da sehrish ta koma bedroom ɗinta sam tagaza samun natsuwa shine ta dinga leƙowa don taga ko yarinyar ta fito daga part ɗin nashi,amma shiru babu alamar cewa ma zata fito,hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,nan tashiga zargi kala kala acikin zuciyarta tana cewa"ko uban mi ya tsayar da ita ɗakin shi a irin wannan lokacin,ni dama banyarda da yarinyar can ba,daga ganinta irin sumu-sumu kasau ɗinnan ne,wlh saina yi maganinta bazan bari taci gaba da shiga sashen shi ba,
   tun tana sa ran fitowar sehrish harta haƙura ta koma bedroom ɗin data sauka,shiga ciki tayi tana ta faman sambatu kamar wata zararra duk akan sehrish ne take wannan 6acin ran,
Â
  ******************
*Junaid Romeo*
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.