Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Bayan azmee ta tafi dasu Jahad,anan su abba suka tsaya suna ƙara tattaunawa atsakaninsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,lamarin ya rikirkitasu,bakomai yafi tsaya masu aransu ba,face yarda Sehrish ta nuna batasan ƴan uwanta ba,bayan ga shaidunan sun bayyana karara nacewar ƴan uwanta ne su,kome yasa haka!?
"Wai ni ina Uncle abusufyan yake ne!ko kun lura da yanayin da ya shiga lokacin da yayi tozali da Sehrish!"Khaleed ne yayi maganar yana kallon fuskar Abban nasu,
 Fawan yace"Nima nayi mamakin razanar da naga yayi lokacin daya ganta,"
 Jahan yace"ku ka sani ko kwalliyar da tayi ne,yasa ya tsorata da ganin kyawun fuskar.....'bai ƙarasa maganar ba saboda kallon da Sgr yayi mashi,tsit yayi da bakinshi,
 "Gaskiya bana tunanin haka jahan,!sae dae wani abun na daban ne yasa shi firgita,"acewar Ayaan,kowa dae da abunda yake tunani acikin ranshi,
 Marshal Omar yace"Kowa ya wuce yayi shirin sallah,kafin a fara kira,"
 Amsa mashi sukayi da toh,sannan suka kama gabansu kowa ya nufi room dinshi,jikinsu duk a mace,sun jima basuji tausayin wani ɗan adam ba kamar yarda sukaji tausayin su sehrish,sun tausaya masu sosai ganin irin halin rayuwar da yaran suka shiga,
 Bayan tafiyarsu,falon ya rage daga Abbansu sai Omar da Sgr sai kuma kanal yousouf,
  "Ni fa ina zargin Uncle Abusufyan abba!kamanninshi da yaran nan yayi yawa abun is over,komai na fuskarsu irin nashi ne!kuma tun daga kan yarda ya firgita da ganin sehrish yasa na tabbatar da cewa akwai wani abu aƙasa,bayan wannan kuma akan idona uncle abusufyan yabar wurin nan agigice jikinshi na rawa ganin ƴan uwan yarinyar nan,ya kamata muje muga a wane hali yake ciki,sannan kuma muji dalilin dayasa ya razana da ganin yaran,"!
 Jinjina kai Abbansu yayi jin abunda kanal yousouf yace,Tabbas ya yarda da maganarshi,don shi kanshi ya lura da halin da ƙanin nashi ya shiga,yana son jin meyasa shi firgita da ganin yaran!
 Batare da 6ata lokaci ba,Suka nufi ɗakin Abusufyan atare,
Lokacin da suka tura ƙopar ɗakin nashi suka shiga ciki,samunshi sukayi zaune dirshen a ƙasa gefen gado yana ta faman sharar hawaye hannunshi dafe da kanshi,sae faman sambatu yakeyi shi kadae,
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,musamman Abbansu,da sauri ya ƙarasa wurinshi,tare da zubewa kasa daga gefenshi yace"abusufyan meya same ka ne!meya faru!me yasaka zubar da hawayenka har haka ne?dan Allah ka faɗamun wlh hankalina ya tashi sosai........'gaba daya duk ya ruɗe ganin halin da abusufyan ke ciki,
 Daga gefen gadon Sgr da Omar suka zauna suna kallonsu,yayin da kanal yousouf yake tsaye ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,turo ƙopar aka kumayi,Hajiya azeema ce tabiyo bayansu,
"Subhanallahi Meya faru ne!naga Abusufyan na kuka?wani abu ya sameshi ne"?fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar ayayin da take ƙarasawa ciki ta samu wuri saman stool na gaban dressing mirror ɗinshi ta zauna tana fuskantar su,
gaba daya suka haÉ—u suna tambayarshi dalilin yin kukan nashi,
Sai faman share hawaye yake yi,ya gaza buÉ—e baki yayi magana,
 "Uncle dan Allah kadaina kukan nan,duk ka sanyamu acikin damuwa,idan akwai wani abu dake damunka dan Allah ka sanar damu,koda bamu da maganin damuwar taka,zamu taya ka da addu'a akan Allah ya yaye maka ita,"Marshal omar ne yayi maganar cikin tausasa murya,
Hajiya azeema tace"Ƙanina dan Allah ka sanar damu mana,meyasa ka ware kanka anan kana kuka kai kaɗae kamar wani ƙaramin yaro?mu fa nan danginka ne wanda baka da kamarsu aduniyar nan,dan haka kada kaji komai ka faɗa mana damuwarka insha Allah,zamu nemi mafita atare,'
 ɗagowa yayi da idanuwanshi wadanda sukayi jawur suka kumbura saboda kukan da yasha ya kalli yayan nashi la66ansa na kerma yace"ƴa'ƴana yaya,Su ne damuwata,saboda su ne nake zubar da hawayen nan,na cuci rayuwarsu akan idona rayuwarsu ta wulakanta batare da na ɗauki mataki ba.........'
 Hankali atashe Abba da Azeema suka haɗa baki wurin cewa"Ƴa'ƴa kuma!wasu ƴa'ƴa kake magana akai kenan!"
 ganin yarda suka razana da jin maganarshi yasa jikinshi yin sanyi dama yasan dole suyi mamakin jin cewa yana da ƴa'ƴa,
Sgr da Omar kuwa shiru sukayi suna sauraran abunda Uncle É—in nasu ke cewa,
Â
Jin yayi masu shiru yasa ran Abban nasu 6aci a fadace yace"ba zaka buÉ—e baki kayimana magana ba!
Sam ya rasa ta yarda zai fara sanar dashi game da ƴa'ƴan da yake magana akai,tsoranshi karya ƙi amincewa da zancen shi,yana fargabar abunda zai biyo baya in ya sanar dasu cewa yaran nan ƴa'ƴanshi ne,
 "Kai nake sauraro abusufyan!ka sanar mun akan wasu ƴa'ƴa ne kake magana!'wannan karan a rikice abba keyi mashi magana,
 cikin sanyin murya Abusufyan yace"Yaya hossein,ina magana akan ƴa'ƴana ne,waɗanda na haifa,na haifi ƴa'ƴa batare da saninku ba...........'
A razane abbansu junaid ya miƙe tsaye yana kallonshi yace"What!!abusufyan kai da kanka kake faɗamun cewa kana da ƴa'ƴa naka na kanka!?Anya ba kunne na ne ke jiyomun ba dai dai ba,"yayi tambayar fuskarshi da alamun ruɗu acikinta, jiki na rawa abusufyan ya miƙe tare da
ruƙo hannun abban acikin nashi yace"dan Allah ka zauna yaya,zanyi maka bayanin komai,tabbas dagaske ne ina da ƴa'ƴa abba,kuma suna nan araye,jini na ne su,'
 dafe kai Abba yayi saboda wani irin jiri daya ji yana niyar kwasar shi,dakyar ya iya buɗe baki yana ambaton"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!abusufyan ka cuce mu Kuma ka yaudare mu ka zubda ƙimar family dinmu!ashe dama abunda ka aikata kenan shiyasa ka gudu kabar ƙasar nan!?saboda kayi ma wasu ciki kana tsoran asirinka ya tonu shine ka tattara kabar ƙasar nan!"ƙarasa maganar yayi yayin da hawaye ke gangarowa daga cikin idanunshi,abun ba ƙaramin gigita su yayi ba gaba dayansu,basu ta6a tunanin cewa abusufyan dinsu zai iya aikata wannan mummunan abun ba,
A faÉ—ace yaci gaba da magana"ka faÉ—amun gaskiyar lamarin tun kafin ranka ya 6aci!tun yaushe wannan abun ya faru baka sanar mun ba!wacece ko kuma suwa kayi ma ciki har aka haifa maka Æ´a'Æ´a!kuma ina Æ´a'Æ´an suke,
 gaba ɗaya abusufyan yasha jinin jikinshi ƙoƙari yake yayi mashi bayani amma ya kasa,
Marshal Omar ne yace"Abba,pls mubi komai asannu har mu samu uncle ya warware mana komai,Ni ina da tabbacin cewa Uncle abusufyan bazai ta6a aikata abunda muke zarginshi dashi ba,dole akwae wani dalilin.
 Girgiza kai Abbansu ya shiga yi ranshi atsananin 6ace yace"Kabarni Kawai Omar,abusufyan ya gama da mu,bansan iya zunubin da ya aikata ba,da yasa harya gudu yabar ƙasar nan tsawon lokaci,
Amman tunda ni bazai sanar dani gaskiyar Lamarin ba, bari na kira Ammi a waya na sanar da ita abunda ya aikata,may be ita zai iya yi mata bayani tunda ni bazaka faÉ—amun ba!"
 Yana ƙarasa maganar ya zura hannu acikin aljihun wandon shi yana ƙoƙarin curo wayarshi don ya kira ammi,
 Cikin sauri abusufyan ya ruƙo hannunshi muryar shi har kerma takeyi wurin cewa"ya..ya hossein ka saurareni dan Allah,ina ƙoƙarin na fahimtar dakai ne,muddin ka sanar ma ammi wannan maganar zan tattara kayana nabar gidan nan ne!saboda bazata ta6a fahimtata ba,kamar yarda kai zaka fahimceni.......'
 jikin Abbane yayi sanyi ganin yarda Abusufyan ke ta faman zubar da hawayenshi,
 Sassauta muryarshi yayi cikin lallami yace"ka sanar dani Abusufyan!taya akai ka samu ƴa'ƴa"?
 Hannuwanshi duka biyun yasa ya rike kanshi da yake jin kamar zai fashe,ga wata uwar zufa da ke zubo mashi har ta jika wuyan shaddar jikinshi,sai faman girgiza kanshi yake ya rasa ta ina zai fara komae ya dagule masa,da ka kalle shi zaka fahimci bai cikin hayyacin shi,
  Kanal yousouf ne ya dan yi gyaran murya kafin yace"Abba ni ina ganin muje muyi sallah kilan uncle zai samu natsuwa yayi cikakken bayani don na fahimci kaman bai acikin hayyacin shi ma" jinjina kai Abban yayi don shima ya fahimci hakan,ya mika masa hannu tare da cewa"taso muje muyi sallah amman in muka dawo dole kayi mana cikakken bayani" daga masa kai Uncle Abusufyan yayi alamar ya amince daga haka suka fito gaba dayansu suka nufi masallaci kowa da abunda yake sakawa a ransa.
Zamu so muji yarda wannan al'amarin ya faru,taya akai abusufyan da bai ta6a aure ba ya samu Æ´a'Æ´a',taya akai yayi aure batare da sanin Danginshi ba?suwaye Æ´a'Æ´an nashi da yake magana akai,amsoshin duka wadannan tambayoyin na a bakin Abusufyan,batare da 6ata lokaci ba zamu nutsa cikin labarin da Abusufyan zai ba yayan nashi hossein da zarar sun dawo daga masallacin.
A6angaren su Sehrish kuwa,tunda azmee ta shigar dasu hosana da jahad a ɗakinta,gaba ɗaya ta takure kanta saman gado,jikinta sae kerma yakeyi ko son ganinsu bata yi,hakan ba ƙaramin raunata zuciyoyinsu yayi ba,zuba mata ido kawai sukayi suna kallonta yayin da hawaye ke zuba a fuskokinsu,a gefen gadon nata suka zauna,
 Jahad tace"banta6a tunanin cewa zakiyi mana haka ba sehrish,nayi tunanin zakiyi murnar ganinmu bayan tsawon lokaci da bamu haɗu ba,amman sae gashi kin juya mana baya,agaban mutane kika nuna cewa baki san mu b....!"
 Tunkan takai ƙarshen maganar Sehrish ta kwatsa mata tsawa tana cewa"Karki ƙara yi mun magana!ni ko muryoyinku bana son ji wlh,bansan su wanene ku ba,kawai kunzo don ku takura ma rayuwata ne..,...'
 Cikin shessheƙar kuka hosana tace"dan Allah sehrish ki daina faɗin hakan!bana jin daɗi,meyasa zakiyi mana haka?Yanzu kin manta da hosanarki?ga kuma jahad?rishi dan Allah kidaina yi mana wannan wasan,'
Hannu sehrish tasa tare da toshe kunnuwanta alamar bata jin ma abunda suke cewa........'
   Duk wannan budurin da akeyi Hayaam na kumshe aɗakinta batasan meke wakana ba,tsoranta karta fito su haɗu da Babban yaya awaje,don tasan muddin yaganta acikin gidan sai yasa an wurgar mashi da ita waje,wannan dalilin ya hana ta fitowa,
Amani kuwa har sun kammala kimtsawa ita da Amal zasu zo gidan,sai ga Abbas ya shigo gidan,a lokacin suna tsaye ita da Amal acikin falon gidan,
tarar shi tayi tare da cewa"Kai fa muke ta jira tun É—azu mun kammala shiryawa,"
 Abbas yace"sai dai kuyi haƙuri,yanzun nan Abba ya kira ni awaya ya sanar dani cewa wani babban al'amari na faruwa agidan,inyi sauri inxo Suna jira na,bana tunanin cewa suna yin wannan walimar ma,"
 Jiki asanyaye tace"Allah yasa dae ba wani abunne ya faru ba,bari mu hakura to in komai ya dai dai ta munje,"daga haka Abbas ya shige ciki yayi abunda zai yi ya fice.
 Wannan ne abunda ya hana su Amani zuwa gidan,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.