Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
 shiga gaba yayi su hossana suka bi bayanshi, daker jahad ke taka Æ™afarta da taimakon hossana take tafiya saboda ta dafa kafaÉ—arta gudun karta fama ciwon Æ™afarta,Â
  A haka har suka ƙaraso harabar asibitin wurin ajiye motocinsu, hannu major yasa tare da buɗe masu ƙopar back seat don su shiga su zauna,har jahad tasa kai zata shigo suka jiyo muryar nurse camila tana cewa "wait !! Wait !!,
 Dakatawa su kayi gaba dayansu suna kallonta dama kuma sun so su tambaye ta,ɗan zaman da su kayi da ita ba ƙaramin shiga ransu tayi ba, ƙarasowa tayi kusa dasu tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta na ruƙe da jakar kaya, daga bisani ta ɗago fuskar nan ɗauke da murmushi tace"ba sallama twins?yanzu da banzo ba shikenan zaku tafi ko? Ku barni da kewarku,
 murmushi sukayi gaba ɗayansu jahad tace "a'a bamu ganki bane shiyasa,"
  kallon major tayi tare da cewa "tare dani zaku tafi, saboda already mun yi magana da marshal omar, ya dauke ni amatsayin wadda zata cigaba da kula da lafiyarsu,inaso naga gidan saboda in na tashi zuwa,
 wani irin farin ciki ne ya rufe su hossana da jahad saboda sun lura da irin mutuncin dake gare ta, ba ƙaramin kula zasu samu a wurinta ba,
 Murmushi major yayi tare da cewa "naji daÉ—in jin hakan sosai,saboda na lura da yadda kikeson yaran ina fata zaki kasance tare dasu,kuma zaki riÆ™e su amana,". Â
 Jinjina kai Camila tayi tare da cewa "NA RIƘE AMANA,"
 daganan suka shiga cikin motar jahad da hossana suna a back seat,major na a mazaunin driver yayin da Camila ke Zaune a other seat É—in,"Â
  a hankali yake driving dinsu harya fuce daga asibitin,ya miƙi shantalelen titi dasu, ajiyar zuciya kawai suke sauke wa ga wani farin ciki daya baibayesu, ba don komai ba sai don sanin cewa Ƙarshen wahalarsu yazo, yanzu lokacine da zasu huta ma rayuwarsu,suyi rayuwa ta ƴanci kamar kowane ɗan adam, batare da an ƙuntata masu ba ko an cutar 😇
 Lokacin da suka ƙaraso gidan Uncle Abusufyan nan fa hossana ta zaro ido tare da buɗe baki alamar mamaki yarda kasan ƴar babyn roba haka ta koma sam bakinta yaƙi rufuwa don murna, ita kanta jahad bakinta a buɗe don murna fararen hakoran nan nata kamar gonar auduga, adai dai bakin gate ɗin major ya tsayar da motar sannan ya danna horn da ƙarfin gaske,
 sai gashi an buɗe masu gate ɗin ta ciki, ba kowa bane face abokin Major ɗan leƙen asirin shi, acikin gidan ya kwana saboda omar ya dauke shi aiki, bayan alherin da yayi masa na kyautar mota sabuwa mai kyau da tsadar gaske, ga kuma uban salary daya yanka masa,😇
  A hankali major ya shigar da motar cikin gate ɗin ɗan dagatawa yayi da driving ya zuge glass ɗin motar ya kalli osman yace "Shege mutumina, ka ga yarda ka canza jiya izuwa yau har wani haske ka fara? Cike da zolaya yayi maganar,
 Dariya Osman yayi tare da cewa "ba dole kaga canji ba,an gaya ma yin karin kumallo da farfesun kaza wasa ne? mutun ya kwana a ac,sannan yayi wanka acikin kwami haba ae dole ma ne in canza,"Â
 gaba ɗaya suka fashe da dariya jin abunda yace,
  Major yace "nifa wasa nake maka malam, taya zaka canza kawai daga jiya zuwa yau don ka kwana a ac, kayi breakfast da farfesun kaza? Nace sannu ko uban son banza ae sai nan da irin one month haka,nan zamu ga canji,
 Murmushi osman yayi tare da cewa " ka shiga ciki ka sauke su,in ka dawo zamuyi magana dakai, akwai labari mai daɗi,"
ï¿?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.