Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Bacci sosai sehrish tasha, har wuraren Æ™arfe biyar da wani abu babu alamun zata farka kamar matatta, kusan sau huÉ—u azmee na leÆ™owa don taga kota farka saboda ta lallashe ta akan abunda ya faru amma duk in tashigo sai ta same ta tana ta faman shan bacci,Â
Ƙarar jiniyar motocinsu ce tasa sehrish farkawa a gigice, fuskar nan tayi jaga-jaga da ita saboda kukan da tasha,ko da ta farka zuciyarta nata faman bugawa, a kasalance ta tashi zaune saman gadon tana faman sauke ajiyar zuciya, idonta takai kan agogon bangon dake manne, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin cewa har lokacin sallar magrib yayi, gashi ba tayi la'asar ba, cikin sauri ta sauko daga saman gadon ta wuce cikin toilet donta ɗaura alwala,
ï¿?
Yau da wuri suka dawo, Abbansu tare da marshal Omar da kuma Sgr sai kanal Yousouf, a nan main palour É—in suka rarrabu, Abbansu tare da kanal yousouf suka wuce bedroom É—insu dake a nan down stairs, Omar da Rafayet atare suka haye upstairs,Â
Tuni azmee ta kammala jera masu dinner ɗinsu a dining, duk anan suka hallara suka ci abincin, banda sgr da bai fito ba, bayan sun kammala ita tashiga kwashe warmers din da sauran tarkacen da sukayi amfani dashi tana kaiwa kitchen, ganin tana ta faman ɗawainiya ita kaɗae ba sehrish yasa junaid kama mata kayan suna kaiwa kitchen atare ba ƙaramin daɗin hakan taji ba,barin shi tayi a cikin kitchen ɗin ita kuma ta wuce don ta gyara masu dining area ɗin, kafin ta dawo har junaid ya kammala yin wanke wanken kayan da sukayi amfani dashi, tare da gyara kitchen ɗin tsaf tamkar ba'ayi amfani dashi ba,
  tsayawa tayi tana kallon shi yana ƙoƙarin haɗama sehrish cornflakes acikin kofi,
 Juyowa yayi ya kalle ta tare da cewa"aunty azmee irin wannan kallo haka"?
 Murmushi tayi tare da cewa"junaid kai na musamman ne,kana bani mamaki yanzu kai da kanka kayi wanke wanken nan?kuma ka gyara kitchen ɗin nan?
 Murmushi yayi tare da cewa "menene aciki aunty azmee?nifa ba aikin da bazan iya yi ba,kuma aiyukan mata suna burge ni sosai, naji ma ina shawa'ar inga ina wanke wanke girki da shara,"
  dariya sosai azmee tayi tana girgiza kai tace"gsky baka da dama junaid, koda yake abune mai kyau ka koya,yana da amfani hakan saboda wata rana zaka taimaki matarka ne da wasu aiyukan cikin gidan,Ko ba haka ba?" ta tambaya tana kallon shi,. Â
 ɗaga mata kai yayi alamar eh, sannan yace"aunty azmee ki tayani da addu'a Allah ya cikamin burina,inaso nayi aure very soon insha Allah end of this year.....' kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azmee ta saki baki galala tana kallon shi,
 fashewa da dariya yayi a lokacin har ya kammala haÉ—a ma sehrish cornflakes É—in,Â
 "Joking aside pls faÉ—amun gaskiya amma dae wasa kake mun ko"?Â
 girgiza mata kai yayi alamar a'a sannan yace"just keep praying for me, insha Allah soon i wll get marriage," yana faɗin hakan ya kama hanyar fucewa daga kitchen ɗin hannun shi ɗauke da Cup sai faman tiriri yake,
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
 shiru azmee tayi tana kallon bayanshi har ya 6ace mata, lamarin ya ɗaure mata kai tabbas tasan halin junaid tunda harya iya furta mata aure yakeso to kuwa fa auren zaiyi dagaske, kuma duk abunda ya nuna yanaso sai abbansu ya mara mashi baya,
 "Ashe zamu sha biki," ta faÉ—i da dariya a fuskarta,Â
  Knocking kopar ɗakin sehrish ya shiga yi, a lokacin har wani baccin ya soma ƙoƙarin ɗaukarta asaman sallayar,tana jin bugun ƙopar a firgice ta tashi tana faɗin "Waye"!
  daga waje junaid yace"Mijinki ne insha Allah," ita kanta batasan lokacin da tasaki murmushi ba,
ï¿?
 "Ka shigo ciki," ta bashi amsa, tura kopar yayi tare da sa kai yashiga ciki yana faman zabga mata murmushin nan nashi, wuri yasamu kusa da ita anan ƙasa ya lankwashe ƙafarsa ya zauna tare da miƙa mata cup ɗin yace"nasan zaki buƙaci wannan,haɗine na musamman daga mijinki insha Allah,"
 fashewa da dariya tayi tana kallon shi, kafin ta zuro hannayenta daga cikin hijabin jikinta ta kar6a, jikinta har rawa yake yi wurin ɗaukar spoon ɗin dake aciki tashiga ɗebowa tana kaiwa bakinta, ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
 Tun tana sha da cokali har ta tsame cokalin daga cikin kofin ta miƙa mashi tare da cewa"ruƙe mun," hannu yasa ya kar6a, kafa cup ɗin tayi abakinta tashiga kwankwaɗarshi harta shanye duka,
 tausayi ta bashi saboda ya lura ba ƙaramar yunwa take ji ba, cikin sanyin murya yace"nasan kina jin yunwa sosai,bari naje na kawo maki dinner ɗinki," yayi maganar tare da yunkurawa zai miƙe cikin sauri tace"a'a nagode da wannan ma,ba yunwa bace damuwata ba, abunda ke damu na shine Har yanzu aunty azmee fushi take dani"? fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar,
  "Kada kisa damuwa aranki, nayi ma aunty azmee magana kuma ta fahimce ki,tun É—azu ma take ta son tayi magana dake,"Â
 Cike da farin ciki tace"dagaske Aunty azmee bata fushi dani kuma nema na take"?
  jinjina mata kai yayi alamar eh, cikin sauri ta miÆ™e tana naÉ—e dardumar don taje ta ganta,Â
  ɗaukar cup din da ta ajiye yayi sannan yayi mata sallama ya fuce daga ɗakin,
  cire hajib É—in tayi, sannan ta É—auko mayafi mai girma ta rufe jikinta dashi, buÉ—e Æ™opan tayi sannan ta fito tare da wuce wa É—akin azmeen, kwankwasa mata Æ™opa tayi, a lokacin azmee bata jima da kammala salla ba,Â
 tasowa tayi tare da sanya hannu ta buɗe mata ƙopan, jikinta na sanye da dogon hijabi hannunta na ruƙe da cazbaha,
  Zuba ma sehrish ido tayi tana kallonta, cikin en ina tace"Aunty azmee dama junaid ne yace kina son gani na," ta ƙarasa maganar tana sunnar dakai cike da fargabar amsar da Azmeen zata bata,
 murmushi azmee tayi tare da cewa"hakane tun É—azun nake ta son in yi maki magana amma duk in nazo saina same ki kina bacci," jinjina kai sehrish tayi sannan tace"nasan na 6ata maki rai aunty azmee, ki yafe mun,"Â
 hannu azmee tasa tare da shafa gefen fuskarta tace"just forget about the past komai ya wuce ki manta kawai, yanzu ma nake shirin zuwa in shirya maki abinci don nasan kina jin yunwa sosai,
 Murmushi sehrish tayi ba Æ™aramin kwanciyar hankali tasamu ba,Â
   Sannan tace"bari na barki ki huta nasan kinyi aiki sosai kin gaji,banji daɗi ba ɗazun da kika hanani tayaki aiki," cikin sanyin murya ta ƙarasa maganar,
  Azmee tace"ki manta da wannan, yanzu kije ki haɗa abincin ki ci," amsa mata tayi da toh,sannan ta juya zata fita,
Muryar azmee ce ta sake katse ta da cewa"Au na manta ban sanar dake ba, babban yayan ku fa ya dawo, yau da wuri suka shigo, shi kaÉ—ae ne ma ya rage bai ci abincin shi ba, ki fara kai mashi pls,"
 Amsa mata tayi da toh sannan tasa kai ta fuce daga ɗakin nata,
 *SGR*
gaba É—aya hankalin shi na akan Laptop dinsa da yake dannawa, yana a hakimce saman royal sofa mai mazaunin mutun biyu, jikin shi na sanye da kimono robe ta cotton,green colour jikinta akwai zane zane masu kyan gaske, rigar bata rufe faffaÉ—an Æ™ijinshi ba,hakan ba Æ™aramin kyau ya Æ™ara mashi ba,ya É—aure igiyar rigar adai dae saitin shafafen cikin sa, a natse yake danna laptop din da zira ziran yatsun hannun shi, Æ™amshi ta ko'inaÂ
 da sallama sehrish ta shiga falon nashi, batare da ya ɗago ba ya amsa mata sallamar,
ï¿?
  Shiga ciki tayi hannunta na É—auke da Æ™aramin tray mai É—auke da fruits tare da coffee,Â
 koda ta Æ™arasa dab dashi murya na rawa tace"sannu da aiki,fatan kana lafiya,"Â
 "Alhmdllh," ya amsa mata har time É—in bai É—ago ba, ajiye mashi tray É—in tayi daga gefen laptop É—insa, sannan tace"kana buÆ™atar wani abu"? hannu yasa ya É—auki cup of coffee É—in yakai bakinsa ya É—an kur6a, janye shi yayi daga bakin shi sannan anatse yace"na manta phone É—ina asaman pillow a É—aukomin ita," juyawa sehrish tayi da sauri zata kama hanyar zuwa bedroom É—in nashi kamar daga sama taji gaba É—aya mayafin jikinta ya sulale Æ™asa daga jikinta, cikin sauri ta juya tare da kai hannu zata É—auki mayafin daya faÉ—i Æ™asa, ganin Æ™afar sgr tayi asaman mayafin ya take shi da farar Æ™afarshi, kasa É—aukar mayafin tayi saboda fargabar da tashi ga, ranta ne ya bata cewa ba dagangan yayi hakan ba, da alama baisan ya take mata mayafin ba,Â
 A É—an tsorace tace"mayafi na" batare da ya É—ago ya kalle ta ba yace "ina Sane," jiki asanyaye ta juya tare da nufar É—akin nashi, tsoranta kar ace alluran nan ta jiya bata sake shi ba,Â
 faÉ—awa cikin É—akin nashi tayi tare da nufar saman pillow É—insa wayar na ajiye asama,hannu takai zata É—auki wayar kwatsam taji motsin mutun abayanta hakan ya sanyata juyowa a firgice gaba É—aya sumar kanta ta watso harta gaban fuskarta, tsananin tsoro ne yakamata ganin mutumin da tabaro yana shan coffee tsaye agabanta, a wani irin yanayi yake bin jikinta da kallo tundaga kan Æ™afarta har izuwa saman Æ™irjinta, ganin haka yasa sehrish ta soma ja da baya a tsananin tsorace saboda tunawa da abunda ya faru jiya atsakaninsu hakan na nufin cewa Allurar bata sake shi bane, har yanzu akwai saura ajikin shi,Â
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.