Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
lokacin kiran sallar magrib,abusufyan ya fito daga cikin toilet,jikinshi da danshin ruwa alamar alwala yayi,a lokacin abu na zaune gefen gadonsu tana jiran fitowarshi,jin alamar buɗe ƙopar shi yasa ta ɗan dago ta kalleshi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Sannu da fitowa hayatyna,"
Ƙarasawa yayi wurinta tare da zama daga gefenta yace"me kika tanadar mun yau idan nadawo gida da daddare?
Abu tace"komai kakeso,"
"To ki tanadar mun kan ki,yau zan baki mamaki,awashe gari zaki haifa mun babies bama É—aya ba....'
 Dariya tayi sosai jin abunda yace kafin ya tashi yayi mata sallama tare da fucewa,'
Lokacin da aka kira sallar isha'e bayan tayi wanka ta ɗauro da alwala,sai da ta kammala sallar sannan ta shiga shirya kanta,tun tana shafa mai ajikinta take tunano kalamam abusufyan nacewa zata haifa mashi babies awashe garin ranar,ta lura ba ƙaramin son ƴa'ƴa gare shi ba,kusan kullum ne sai yayi mata maganar yaushe zasu haihu,wani lokacin har cewa yakeyi wai ko dae basu isa haihuwa bane shiyasa bata samu ciki ba,duk irin ƙoƙarin da yakeyi, don ba ƙaramin jarababbe bane,
Murmushi tayi tare da cewa"Nikaina aƙagare nake dana ga ƴa'ƴan da zamu haifa ni da abusufyan ɗina,nasan yaran zasu zama kyawawan gaske in dai suka ɗauko kyawun fuskar kowannanmu,amma ni dae nafi son su ɗauko fuskar shi,saboda koda wata rana in yayi tafiya mai nisa,zan dinga kallon fuskarsu a matsayin tashi,hakan zai ɗebe mun kewa,
Gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren da abu ta feshe jikinta dashi,bayan ta gama shafe shi da haɗaɗdun mayukan jikinta,komawa tayi gaban wardrobe ɗin kayansu ta buɗe tana tunanin wasu kaya zata sanya waɗanda zasu zautar da abusufyan,ta jima atsaye tana ruwan ido kafin ta hango wata rigar bacci Babby doll black color,net ne ajikin rigar shara shara ana kallon komai na jikin mutun,tamkar ma mutun bai sanya kaya bane saboda yadda take fitar da tsiraici,ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,zubo da gashin kanta tayi ya sauko har wurin waist ɗinta,komawa tayi gaban mirror ta shafa jan baki red abakinta,
Bayan ta kammala shirin nata,ta shiga zagayen ɗakin tana jiran dawowar abusufyan,tana yi tana kallon wall clock dake manne a bango tana duba time,abu kamar wasa har ƙarfe 10 na dare babu abusufyan,shi da ya saba dawowa da zarar an kammala isha'e,baiwar Allah har ta fara gajiya da yawon,komawa tayi ta zauna gefen gadon tana sa ran dawowarshi,da zarar taji motsin mutun ya shigo cikin gidan sai ta miƙe jiki na rawa ta leƙa taga wanene ashe Haris ne ya dawo,na biyu kuma data leƙa Abbansu ne ya dawo,ƙarshe dae bacci ya kwashe ta,wuraren goma sha biyu ta farka,ganin har lokacin bai dawo ba,yasa hankalinta yayi mugun tashi,saukowa tayi daga saman gadon ta ɗauko hijabi ta zura ajikinta,sannan ta fito daga ɗakin ta wuce bedroom ɗin haris,
 A ƙofar ɗakin ta tsaya tana kwankwasawa,
 Cikin bacci haris ya jiyo bugun ƙopar ɗakin nashi,muryarshi akasalance yace"Wanene,"
 Abu tace"ni ce Zainab,'
Saukowa yayi daga saman gadonshi yazo bakin ƙopar ya buɗe mata tare da cewa"lfy,meya faru ne abu?
 Abu tace"ɗan uwanka abusufyan har yanzu fa bai dawo cikin gidan nan ba,hankalina ya tashi sosai,bansan ko kana da masaniya akan inda yaje ba,"
 Cike da mamaki Haris yace"wai kina nufin bro ɗina bai dawo gida ba?tare dashi fa muka je masallaci,amma ba tare muka dawo ba,saboda yace mun yana sauri yazo wurinki ne,ni kuma na biya gidansu abokinmu ne,"
 Jin wannan maganar yasa hankalin abu ya ƙara tashi haikam,tuni idanunta sun cicciko da kwalla,dama bata da wuyar yin kuka,fargabarta kar ace wani abu ne ya faru da mijinta,
 Lallashinta haris yayi tare da cewa"just calm down ur mind,duk inda abusufyan yake yana atare damu,bana so ki tashi su mommy daga bacci game da maganar nan,hankalinsu zai tashi ne,bari na jaraba kiran numbar shi muga in zata shiga,"ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya shiga cikin ɗakin nashi,
 Sai gashi ya dawo hannun shi ruƙe da wayarshi yana dannata,numbar shi ya kira,tana fara ringing abun mamaki akayi picking kiran,
 Da sauri haris ya kara wayar a kunnan shi yace"bros kana ina ne wai?har 12 baka dawo gida ba?duk ka tayar mana da hankali,"
 Gaban haris ne ya faɗi rass jin muryar mace tana cewa"mai wayar ya shiga wanka ne,'
 rejecting kiran yayi cikin sauri gudun kar abu tajiyo muryar macen da yaji,don ya santa da kishi,
 "Me ya ce maka"! Ta tambaya tana kallonshi,
 Daƙyar ya iya cewa"Am..um...kin gane wani aiki ne ya tsayar dasu a company,sai zuwa gobe ko da asuba zai dawo,dan Allah ki ƙara hakuri....'
 Tunkan yakai ƙarshen maganar tashi abu ta watsa da gudu ixuwa ɗakinsu ta faɗa saman gado tana kuka,tasha kuka sosai a ƙarshe bacci ya ɗauke ta,
Koda ta farka sallar asuba,abusufyan bai dawo ba,bayan tayi salla ta zauna tana karatun al'qur'ani don kar bacci ya kuma ɗaukarta,wuraren ƙarfe 7:30 tayi shirin zuwa islamiyya,duk da halin da take ciki na damuwar rashinshi,
  batare da sanin kowa ba ta fice ko breakfast ba tayi ba,a bakin gate suka haɗe da baba buzu,
  Zuƙunnawa tayi tare da gaishe shi"ina kwana baba,kun tashi lafiya,"
 Baba buzu yace"me ya faru abuna?naga fuskarki tayi jawur ta kumbura kamar kinsha kuka"?
 cikin sauri tace"a'a babu komai baba,lafiya ta lou,'ta bashi amsa tare da miƙewa tsaye,
 "Ina abusfyan ɗin yake ne yau bazai kai ki makarantar bane"?
 Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,
  Bai kawo komai aranshi ba,yace"kada ki makara ki wuce ki tafi,"
Amsa mashi tayi da toh sannan ta fito waje ta kama hanya tana tafiya ita kaÉ—ae cike da damuwa,
 Kwatsam!kamar ance ta waiga ta hango Motar abusufyan yayi parking ɗinta a gefen hanya,mamaki ne ya kamata,
Jiki na rawa ta nufi wurin motar tare da sanya hannunta ta kwankwasa glass É—in shi,
 Zuge glass ɗin akayi a slow,a gigice Abu ta zaro ido waje tana kallonsu,abun tamkar a mafarki, sun manne da juna abusufyan ɗin da take ta haukan nema tare da wata matashiyar budurwa cikin motar,budurwar ko kayan kirki babu ajikinta,inners ne kawai ta bari,da alama ma basu acikin hayyacinsu sunyi nisa cikin harkar tasu,
 Hankali amatuƙar tashe abu ta aza hannunta akai tana fadin"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una....!'
Tana ƙarasa faɗar hakan ta yanke jiki ta faɗi a sume ƙasa,zubewarta ƙasa ke da wuya,Motar nan tabar wurin tamkar bata ta6a bayyana ba,
 Adai dai lokacin kuma Motar Abusufyan ta shigo layin da gudun gaske,tunkan ya ƙaraso ya hangi abu sume a ƙasa cikin uniform dinta,gabansa ne ya faɗi rass,da sauri ya tsayar da motar tare da buɗe ta ya fito yana faɗin"kai!me nake gani haka?kodai idanuna ne suke nuna mun ba dai dai ba!abuna ce kwance a ƙasa!taya akai hakan ya faru!"
 ƙarasawa yayi tare da zuƙunnawa agabanta yana shafa fuskarta,ya jima yana mamakin yadda akai abu ta sume ƙasa,kuma tabbas itace,
 Hannu yasa ya ɗaukota ya nufi mota da ita bayan ya kwantar da ita abayan motar ya shiga gaban motar ya tashe ta suka nufi gida,
Lokacin da abusufyan ya shigo da abu a hannunshi,Hajiya Ameena suna xaune saman dining chairs ita da alhaji da kuma haris suna yin breakfast,
Hankali atashe suka nufo shi suna tambayarshi lafiya!meya faru da ita!
Hajiya tace"Yaushe kuka fita tare da ita batare da sanina ba!?
Abusufyan yace"mommy ba atare muka fita ba,ni jiya ban kwana agida ba,bacci ya ɗauke ni acikin mota ban ƙara sanin inda kai na yake ba sai da safen nan,kuma wayata ma an sace ta banganta ba,"
Mamaki ne ya kamasu su duka,musamman Haris kanshi ya É—aure jin cewa an sace wayar abusufyan hakan na nufin cewa jiya wayar bata a hannunshi wasu ne suka É—auke wayar,to garin yaya hakan ya faru,
 Hajiya tace"Haba abusufyan ɗina garin yaya har bacci ya ɗauke ka acikin mota,kuma aka sace maka waya,duk ta yaya hakan ya faru"?
 Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"wlh mommy ni kaina bansani ba,wayata tun a masallaci aka sace ta,ban tashi ankara ba sai da na shiga cikin motata bayan mun rabu da haris,na kamo hanyar zuwa gida na dinga ganin biji biji acikin idanuna,dalilin dayasa na dakatar da driving ɗin nayi parking na motar,tun daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba,sai yanzu dana farka,na biyo hanyar gida kenan naga abu a kwance ƙasa,ina tunanin wani abune ya tsoratar da ita shiyasa ta sume'
Alhaji yace"kaÉ—an daga cikin sakarcin kane sufyan!in ba shashasha ba taya zaka bar bacci ya É—auke ka acikin mota har ka kwana awaje,ko tsoron wani abu ya faru dakai baka ji!salon kaja ma mutane bala'e ko!?
 Ganin ya rufe shi da fada yasa mommy ta 6ata fuska tare da kallon Abusufyan tace"Ka shiga da ita ciki"
 Amsa mata yayi kafin ya wuce da abu cikin ɗakinsu,
 "Dama ae kin saba goya mashi baya!yaron nan yayi laifi me yasa ba zaki bari ayi mashi faÉ—a ba!ke kina da tabbacin cewar baccin ne ya kwashe shi akan hanya har ya kwana waje?ni ban yarda da zancen nan nashi bama,akwai dae inda yaje,".Â
 Rai a6ace Hajiya Ameena tace"ya isa haka Alhaji!kasan irin kalaman da zaka dinga faɗi akan abusufyan ɗina,in ba haka ba,ranmu xai 6aci ne gaba daya,
Tamkar zasuyi faÉ—a atsakaninsu,ganin haka yasa Haris cewa"pls mommy dan Allah kudaina mana,banaso inga kuna faÉ—a akan abusufyan,wai meyasa kuke haka ne?daddy kaima ka daina sanya baki akan lamarinshi mana tunda mommy bataso,ba shikenan ba,'.
 Jinjina kai kawai Alhaji yayi tare da kama hanya ya wuce upstairs,haris ya ruƙo hannun mommynshi suka koma don su ƙarasa yin breakfast ɗinsu,
A6angarensu abu da abusufyan kuwa,bayan ya kwantar da ita saman gadonsu,ruwa ya dauko a roba ya É—ebo ya yayyafa mata a saman fuskarta,a hankali ta shiga mutsu mutsun buÉ—e idanunta,zuba mata ido yayi yana kallon fuskarta cike da tausayinta don yaga alamar jirwayen hawaye a fuskarta kuma ta É—an kumbura,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.