Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  Major yace "okey bari nazo," yayi maganar tare da sauke glass din motar ya wuce dasu ciki, adai adai stairs ɗin da zai sadaka da main palour ɗin gidan ya sauke su,   Buɗe motar Camila tayi ta fito, sannan suma su jahad suka fito daga ciki suna ƙarewa katafaren gidan kallo ya haɗu iya haɗuwa abun ba'a magana, Omar yasa an canza mashi komai nashi an ƙara ƙawata gidan sosai,   gaba dayansu sun ƙame suna kallon haɗuwar gidan, ganin basu da niyyar shiga daga ciki yasa major cewa "let's go in pls,"  Cikin rashin sani jahad ta take ƙafarta ba don komai ba sai don hankalinta daya tafi wurin ƙarewa gidan kallo,ƙara tasaki tana yarfa hannu tana faɗin "wash Allah na," jin haka yasa camila tayi saurin dawowa ta inda suke, ta taimaka mata wurin yin tafiya don su shiga ciki, Major ne yayi masu jagora su kuma suna abayan shi, har suka shiga cikin haɗaɗɗen jigunannan falon,nan fa suka baza ido suna kallon haduwarshi, wasu irin matsiyatan royal sofa set ne acikin sa masu numfashi ɗunɗuma ɗunɗuma a jere launin su brown colour,ga wasu set na Cushions Jere asamansu difference colour,duk gasu nan ba ƙaramin ƙawata kujerun su kayi ba, daga tsakiya wani ƙayataccen table ne legs dinshi brown ne, while daga saman glass ne, an ajiye flower asaman shi, ga fruits basket mai dauke da kayan mar mari, ba komai yafi tafiya da hankalin hossana ba face tanƙameman kwan filitar dake bama ɗakin haske tamkar zai faɗo ma mutun akai haka yake, sai kuma tv stand din dakin faskekiyar plasma ma ce mai dauke da speakers na jin sauti, ga wani telephone table dage a gefe, bari dae in taƙaice maku zance komai wannan da kuka sani a palour an zuba masu shi,  Sai faman yarfa hannu hossana take yi, yarinya fa takusa zauce wa ganin irin gidan da yaya Omar dinsu ya gwangwaje su dashi, wani abun ma sai mun shiga bedroom,   Jahad kuwa murmushi kawai take saki tana bin ko'ina da kallo,ita kanta Camila gidan ba ƙaramin burgeta yayi ba komai tsaf a natse ba tarkacen hauka,   Can dae hossana tace "Allah yasa ba mafarki nake yi ba,dan Allah koma mafarki nake yi jahad kada ku tashe ni," ta fadi tana faman hadiyar yawu, Dariya su kayi gaba ɗayansu, Major yace "wannan zahiran ne ba mafarki ba ne, kaɗan daga cikin irin son da ya'ya omar dinku yake yi maku kenan,zai iya yin komai akanku more than u think, ni dae fatana agare ku shine ku kasance masu yi mashi biyayya, ku bishi sau da ƙafa kada kuyi amfani da son da yake yi maku wurin karya mashi zuciya,ko ku ce zaku canza halayyarku saboda wata dama da kuka samu, yanzu lokaci ne da zaku more rayuwarku bayan duk wahalar da kuka sha,"  Sosai major yashiga yi masu nasiha, duk sun kasa kunne suna sauraronshi,sannan kuma suna amsa mashi da insha Allah,  Bayan ya kammala daga ƙarshe yace "ku samu wuri ku zauna mana,nasan kuna jin yunwa yanzu zan sa ayi maku oder na abincin da zaku ci, sannan ga bedroom nan zaku iya shiga ciki ku huta,"  A natse suka ƙarasa tare da samun wuri suka zauna fuskar nan fa awashe,  Mayar da idonshi yayi kan Camila yace "zamu tafi tare ne? Na sauke ki a asibitin ko kuwa,"  cikin sauri tace "no i will stay here wit them,cos i ave done my work bani da sauran duty till tomorrow,"  Murmushi kawai major yayi sannan yace "okey," sannan yasa kai ya fuce, A jiyar zuciya ta sauke tare da samun wuri itama ta zauna, bayan ta ajiye jakan kayan data zo da ita,  kallon juna suka shiga yi suna murmushi,yanayin iskar falon badae daɗi ba yadda sanyin ac ke ratsa sassan jikin mutun,   Ganin sun zauna shiru yasa Camila cewa "ba ku buƙatar shiga daga ciki ne? ta tambaya tana kallonsu  Jahad ce tafara cewa "inason nayi wanka, hossana ma tace "nima,"  tashi camila tayi tare da cewa "mu shiga daga cikin ɗakin to, nima inason nayi wankan," tayi maganar tare da ɗaukar jakar kayanta,  gaba tayi suka bi bayanta ɗaya daga cikin bedrooms ɗin suka tunkara, ƙoparsa a rufe take amma bada key aka datse ta ba, hannu tasa ta tura nan take ƙopar ta buɗe, shiga ciki su kayi atare, haɗaɗden bedroom mai ɗauke da tafkeken gado fankacece, yaji lumbutsetsiyar katifa lallausar gaske ga wasu matassan kai masu laushi asama an jera su, irin gadon da kana hawa saman shi ko bakayi niyyar yin bacci ba nan take zai ɗauke ke saboda daɗinsa 🥱 an gyare komai an shimfiɗe shi da bedsheet,side by side na gadon akwai side drawers, masu ɗauke da lamps, daga can ɗayan bangaren ɗakin kuwa wurin Closet dinsu ne, ga wani haɗaɗɗen Dressing mirror an cika masu front dinshi da kayan make up da tsadaddun mayuka na jiki, komai an sanya masu, jerin wurin takalmansu,hand bags da sauran abubuwa da dama ba abun da omar yabari komai ansa masu,   jahad ce tafara shiga toilet ɗin don a ƙagare take da tayi wanka,lokacin da ta shiga cikin toilet nan fa taga zallar haɗuwa ta jima tana bin ko'ina da kallo kafin daga bisa ni tayi wankar daker tare da yin alwala saboda in an kira sallah tayi, fitowa tayi a hankali waist dinta daure da towel mai ɗan tsayi wanda ta samu acikin toilet ɗin, hannunta na ruƙe da doguwar rigarta da ta cire, samun su tayi zazzaune daga gefen gadon suna fira da hossana da Camila,  Ganin ta fito yasa camila tashi ta shiga toilet ɗin, a cikin laundry basket ta turo rigar, sannan ta ɗan juya ta kalli hossana dake ta faman lumshe ido alamar bacci tace "karfa kiyi bacci don na son halinki, ki bari kiyi wanka ke ma,"  Murmushi tayi kafin tace"ae bazan iya bacci ba jahad, saboda gani nake kamar in na kwanta zan farka na ganni a gidan wannan matar da ta azabtar damu,nakasa yarda cewa wai mune acikin wannan katafaren gidan nan mu kaɗai abun mu,gsky yaya omar ba ƙaramin ƙaunarmu yake yi ba,"   Jahad tace"nikaina ina mamakin hakan hossana,ashe akwai wata rana da zato mana irin wannan,mun samu yaya mai son mu tamkar ƙannensa duk don saboda mu ya Omar yabar komai nasa don ya ceci rayuwarmu,har yanzu ina mamamkin hakan hossana, yaya omar ya sanar dani cewa ɗan uwanshi yana kwance rai hannun Allah babu tabbacin cewa zai rayu,amma a hakan ya tsallake shi yazo wurin mu wannan wane irin mutun ne?samun mai iri Kyakkyawar zuciyarshi zaiyi wuya a faɗin duniya (shiyasa Hafsat bature take kamu) 🙄   ta yi maganar ne a lokacin datakai wurin closet tana neman ta inda zata buɗe shi,tana aza hannunta a jikin closet din nan take doors din dake jiki suka zuge da kansu, har sai da jahad ta ɗan tsorata tayi baya,tasowa hossana tayi itama tana kallon wurin kayan nasu, yadda suke tagwaye haka omar yasa aka jera masu komai kala biyu, jerin wurin pyjamas ɗinsu daban, jerin wurin dogayen riguna daban,jerin wurin jeans da t shirt daban, ga jerin under wears shima daban, komai nasawa ajiki an zuba masu shi,har sun wuce iyaka,  "jahad har naji inason nayi wanka wlh,saboda in canza kayan jikina," acewar hossana dake ta faman yarfa hannu tana kallon kayan,  Hannu jahad tasa tare da curo wasu pakistan masu kyan gaske,tana shafa jikinsu tunkan tasa har ta gano kyan da zasu mata,    a gefen gado ta ajiye su, sannan ta koma gaban mirror tana shafe jikinta da ɗaya daga cikin mayukan da tagani ajare, bayan ta kammala ta kuma feshe jikinta da turare mai ƙamshin gaske,   Sannan ta dawo ta tsaya a gefen gadon tana zura kayan ajikinta, duk hossana na can tsaye wurin closet ɗin tana ƴan ta6e ta6e,ji take tamkar tabi kowannansu ta gwada ajikinta,  Bayan jahad ta gama kimtsawa cikin pakistan din komawa tayi gaban mirror tana kallon jikinta,riga ce mai dogon hannu har guiwar ƙafarta sai wandon burgujeje irin nasu,ta yafa mayafin asaman kafaɗarta, sumar kanta kuma ta zubo a bayanta, murmushi kawai takeyi tana kallon kanta a cikin mirrow,  Muryar hossana ce ta katse ta da cewa"kinyi kyau sosai jahad saina ga kin koma mun tamkar ketrina kef,"   Jahad tace"sannu shugaban makaryata ni bada ketrina nake kama ba sai dae helen,oumma tace kamannin mu sak irin nata,' tayi maganar tana gyara gefen gashinta da hannunta,  Hossana tace"wacece helen kuma"?  "Ƴar film ce mana ta ƙasar ethiopia," Jahad ta bata amsa atakaice, kafin hossana ta ƙara cewa wani abu, sai ga Camila tafi to daga toilet din daga ita sai ɗan pant da bra, cikin sauri suka sanya tafukan hannayensu tare da rufe fuskokinsu cikin jin kunya,  tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki take cewa"why are u hidding ur face pls? Can i know  Jahad tace"mun ji kunya ne,"  Murmushi camilla tayi tare da girgiza kai tace"kuna da kunya sosai,in dae haka ne kam ba zaku iya rayuwa a ƙasar mu ba,"   "Wata ƙasa ce"? Hossana ta tambaya,  Camila tace "Mexico," Jinjina kai tayi tare da cewa"ni ko sunan ƙasar ma ban ta6a ji ba gsky...."jahad ce ta katse ta da cewa "hossana zoki wuce kije kiyi wankan kema," Amsa mata tayi da toh sannan ta wuce cikin toilet ɗin,  Ita kuma jahad ta kama hanyar fita daga ɗakin har lokacin fuskarta na rufe da tafin hannayenta, abun sai ya ba camilla dariya sosai,  Sai da ta fita daga bedroom ɗin sannan ta soma sauke ajiyar zuciya, shiga cikin falon tayi, tana ƙare masa kallo, zagaye shi ta shiga yi tana tatta6a dogayen curtains ɗin dake kewaye dashi,   Sallamar Osman ce ta dakatar da ita, cikin sauri ta amsa mashi da wa'alaikum salam,sai da ya fara tambayar iznin shiga daga ciki, ta amsa mashi sannan yasa kai cikin falon,   Hannun shi na ruƙe da manya ledoji na abincin da yayi masu oder a restaurant,yarda yaga jahad ta kimtsa tamkar
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.