Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Shiru Omar ya ɗanyi na wani lokaci kafin yaci gaba da cewa "tun shekaran jiya da muka fita daga gida muna can wurin cetonsu,a asibitin nan aka kwantar da waɗanda suka raunata sosai daga cikinsu,gaba ɗayan mu babu wanda ya samu runtsawa adaren jiya saboda tashin hankalin kada mu rasa su,kuma a daren jiyan ne acikin asibitin nan saƙon ya shigo mun,duk nabi na rikice saboda narasa yarda zanyi, Major shine babban na hannun dama na, shi na kira na nuna mashi saƙon da aka turomin game daku, koda ya gani sai cewa yayi dama ya jima yana son ce mun wani abu, amma ba zai iya sanar dani ba saboda bayason shiga tsakanina da matar yayana, sai abun ya ɗaure mun kai jin abunda yace,a lokacin ban matsa masa ba akan son sanin wani abu ne yake son sanar dani ba,a time ɗin duk da halin da nake ciki burina kawai inzo in ganku, Major shine yace nabar masa komai a hannunsa kar na damu, sai a washe gari major ya sanar dani cewa mu shirya mu tafi, sannan kuma yaban wata number yace mu bi diddiginta, atare dashi muka fito mu biyu kawai muka miƙi hanya, da wayata nayi amfani wurin bindiddigin numbar daya bani har muka ƙaraso titin da dajin nan yake,mu ka shiga cikinsa kai tsaye, muna cikin tafiya naji an kwala mun kira ta waje "yalla6ai," cikin sauri na zuge glass ɗin motar don naga wanene, shine naga wani saurayi zuƙunne a ƙasa, ga ki kuma kwance a sume duk jini a goshin ki, hankali atashe na zabura zan fito daga cikin motar, kawai sai saurayin nan yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar acikin motarsa, gashi can ya miƙi hanyar da tayi dama don Allah ku ceto rayuwarta, " jin haka yasa gaba ɗaya na rikice, cikin sauri major yaja motar mu da gudun gaske muka bi motar wannan tsohon mutumin da gudun gaske har cikin gidan gonarsa, ina shiga najiyo kukan hossana hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, tuni na makance na afka ma ƙopar ɗakin gidan gonar na tarwatsa ta, ina shiga naga hossana a lokacin har yayi nasarar yage mata rigarta ya ruƙe ta a hannunsa, raina yayi mugun 6aci abunda ya hanani yin motsi a lokacin saboda bansan wane irin hukunci zan yanke masa ba,yanzu haka da nake baki labarin nan babu wannan tsohon a duniyar nan saboda na kashe shi,kuma na ɗauko hoton gawarsa don na nuna ma hossana,"
Wani irin murmushi jahad ta saki har ta gaza rufe bakinta don murna,shima Omar É—in murmushi yakeyi yana kallonta,
Nasan dayawa za suyi mamakin yarda akai hakan ta kasance,abun da ya faru shine cikin sojojin dake gadin gidan general ishaq akwai wani matashi Abokin major ne, a lokacin da suka kawo su hussana da jahad gidan Omar ya shiga tare da su ciki , A nan major suka haÉ—e da wannan saurayin abokinsa ne tun suna yara ,sunan Shi Osman bayan sun gaisa Osman ke cewa "Abokina waÉ—ancan yaran fa? dana ga ka shiga ciki dasu Æ´a'yan wanene? ko dai ogan naku ne yayi aure matar ta haihuwa,
Dariya Major yayi tare da cewa "Wai dama Osman har yanzu kana nan da shegen sa idon nan naka? Haba no wonder shiyasa Allah yabarka a matsayin mai gadi, in banda abun ka ina ogan mu yakai shekarun da zai iya ajiye ƴa'ƴa kamar waɗancan? shima fa ba wani babba bane duka shekarunsa bazasu wuce 28 years, matsayi ne kawai Allah ya bashi," jin haka yasa osman ɗan zaro ido tare da cewa "ka ce ashe shima ɗan shila ne, amma dan Allah tun yaushe nake ta fama dakai ka taimaka ka sama mun aiki a ƙarƙashinsa amma ka ƙiya, kafi son kaita ganina a matsayin mai gadin gidan genar, kalli fa yarda na rame nayi baƙi, kai kuwa har wani tumbi kafara ajiyewa saboda jin daɗin rayuwa, wlh abota bata ce haka ba," ya faɗi yana tsuke fuska, dafa kafaɗarsa Major yayi tare da cewa "Ina sane da wannan Osman, kuma insha Allah zanyi ƙoƙari na sama maka gurbi a kusa dashi, mutumin kirki ne sosai yana da sauƙin kai kuma ina jin daɗin aikin dashi,yana kyautatamun domin kuwa kafin ƙarshen wata yayi ina samun ninkin ba ninkin abunda nake samu a albashina wurinsa," jinjina kai Osaman yayi zugudun yayi masa fuskar tausayi kafin yace "Kaji daɗi mutumina,ni dai zan jira naji daga wurinka don Allah karka manta kasa ma mun kusanci dashi, nima na dangwali arxiki,"
Major yace"baka da damuwa, yanzu ma haka ga wani aiki ka samu, waɗancan yaran da kake gani ogan mu yana sonsu sosai, bashi da alaƙar komai dasu hasalima a asibiti ya taimake su,ya kawo su nan ne domin su zauna tare da matar yayansa ishaq, to ni hakan bai kwanta mun araina ba, shi ne nakeso ka sanya mun ido akansu! ka zama tamkar ɗan leƙen asiri duk da nasan hakan ya sa6ama dokar aikin ku amma inaso kayimun wannan Osman,ka lura da duk wani motsinsu acikin gidan nan, so nake kayi aiki tamkar jami'in sirri! dalilin dayasa nayi hakan saboda bana son duk wani abu da zai cutar dasu don na lura da yadda ogan mu ke tsananin ƙaunar yaran,ni kuma bana son duk wani abu da zai 6ata masa rai, ta6a yaran nan tamkar ta6a masa zuciya ne," ya ƙarasa maganar yana kallon osaman da yayi kasaƙai, daga bisani yace "Na amince zanyi hakan, amma wlh ka sani duk ranar da asirina ya tonu, sunanka na ciki ! don ba zan shiga haɗari ni kaɗai ba,"
dariya major yayi sannan yace"Ai ni babu wanda ya isa ya ta6ani muddin ina tare da Marshal, don haka kaima ka kwantar da hankalinka, ba abunda zai same ka face alkhairi,tunda ka amince zaka yi É—in, inaso duk wani hali da suke ciki ka tabbatar da ka kira wayata ka sanar mun,"
Osman ya amsa masa da "toh," daga nan su kayi sallama, a lokacin marshal Omar ya fito daga cikin gidan jikinsa asanyaye suka shiga cikin mota su ka tafi,
tun daga wannan lokacin Osman ya zaman ɗan leƙen asiri duk wani hali da su hossana ke ciki yana sane dashi kaf, kuma duk rana yana kiran major ya sanar dashi halin da suke ciki, Major bai ta6a sanar da marshal Omar ba, saboda gudun karya shiga tsakanin shi da matar yayansa ishaq,kullum yana sanar da osman cewa yaci gaba da sa musu ido,
Idan har masu karatu zasu iya tunawa akwai lokacin da Aunty babba tayima su hussana da jahad bugun mutuwar nan, har suka kaisu asibiti bayan sun dawo suka shige cikin gida ita da hafsat suka bar jahad tsaye gaban motar tana kuka saboda hossana na'a cikin motar kwance rai hannun Allah gashi bata iya ɗaukarta bare tashiga da ita cikin gidan, a lokacin idan zaku tuna akwai wani soja daya zo yana tambayarta meke faruwane, take ce masa ƴar uwartace acikin motar kwance bata lafiya kuma bazata iya ɗaukarta ba, sai sojan yace maza "Can i help," take ce masa eh, yasa hannu ya ɗauki hossana ya shigar mata da ita ciki, ya kwantar da ita saman doguwar kujera, yayin da jahad tabisu, to wannan sojan ba kowa bane face Osman abokin major ɗan leƙen asirinsa, ko lokacin da zai fita daga falon bayan ya kwantar da hossana sai da ya ɗan tsaya daga bakin ƙopar ya juyo yana kallon jahad dake zukunne saman guiwarta agaban hossana tana yi mata addu'a tana kuka, jinjina kansa yayi tare da fuce wa bayan yafita, ya ɗauko wayarsa tare da buga ma major kira, bayan ya ɗaga kiran yake sanar dashi abunda ke faruwa, nace wa shifa yana zargin cewa Matar ishaq tayima yaran mugun bugu har ma ɗaya daga cikinsu ta jigita sosai tamkar ba zata rayuwa,don haka ya hanzarta sanar da ogansu Omar yazo ya kwashi yaran tunkan ta kashe su, har lokacin major bai sanar da Omar ba game da wannan ma, saboda yana tunanin koya faɗi masa daker ya yarda kuma yasan makircin mata, abun zai iya dawowa kansa,
tun fa lokacin da su jahad da hossana ke wanki abayan gidan ita da jahad, Osman yake ganinsu sai yazo ya gifta ta wurinsu tamkar yana yin waya alhalin su yake kallo, har video yake yi masu yana turawa major donya gani," Major ya tsorata da ganin irin uƙubar da yaran suke sha,
Bayan wannan lokacin kuma sai salon ya canza, duk osman na zuba ido yana kallon ikon Allah yarda hafsat ke nuna ma yaran soyayya, aduk lokacin da hafsat ta fita dasu cikin motarta, sai osman ya bisu da machine É—insa dom yaga ina zata dasu, dashi suke yin yawo abayansu batare da sun sani ba, duk inda zasu osman na biye dasu a sirrince,
daya kira Major ya sanar dashi abunda ke faru na cewa yaran fa yanzu suna samun kulawa sosai a wurin mutanen gidan, sai major yace mashi "Wannan salon da suka canza,alama ce dake nuni da cewa sun kusa salwantar da yaran,ina da tabbacin cewa so suke su zubar dasu kaci gaba dasa musu ido,daga yanzu banaso ko bacci ka dunga yi osman, saboda wannan lokacin ne mafi haɗari, aduk lokacin da maƙiyin ka ya canza maka salo na soyayya to kaji tsoransa halakar dakai zaiyi,"
Tun daga lokacin da Major ya sanar dashi haka, bawan Allah osman bai ƙara yin bacci ba, koda bashi ke akan duty ba, yana nan yana lura da shige da ficen da hafsat keyi dasu hossana,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.