Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
turo ƙopar azmee ta ƙara yi hannunta ɗauke da tea set ta miƙa ma sehrish cikin sauri sehrish tasa hannu ta kar6a tana cewa "Nagode aunty azmee,"
Azmee tace "ki hanzarta fa kada kiyi late dayawa,"
 "Toh," ta amsa mata sannan ta shiga shan tea ɗin,
. har azmee zata fita sehrish tayi saurin cewa "Aunty azmee dama inaso nakaiwa babban yaya nashi kafin natafi school,"
  tsayawa azmee tayi hannunta ruƙe da door handle ta juyo ta kalle ta tana ɗan murmushi tace "i knew, raina sai da ya bani cewa sai kinyi magana akan RAFAYET,
,É—an sunnar dakai sehrish tayi tana kallon tea É—in dake hanunta yana faman tiririn zafi
  "Ni nake maki magana ba tea ɗin dake hannunki ba, naga kin zuba mashi ido,' guntun murmushi sehrish ta saki kafin ta ɗago tana kallonta daƙer ta iya cewa "aunty azmee baya jin daɗi jiyan nan that's why nake so nakai masa breakfast ɗinsa,nasan zai buƙace shi,"
 Sakin baki azmee tayi irin mamakin nan tace "to ko dai kece ALEXANDRA ban sani ba,'
 shiru sehrish tayi tana sakin murmushi saboda tagane cewa wannan sunan mommynshi ne,shiyasa azmee ta kirata da sunanta,
  fuce wa azmee tayi tana cewa "shikenan kiyi sauri kizo ki kai masa breakfast ɗin," tana jin haka tayi saurin ajiye tea ɗin hannunta asaman bedside drawer inda kayan tea ɗin suke,
  hijab ɗinta ta ɗauko ta zura ajikinta yar dai² shoulders ɗonta, sannan ta wuce kitchen ɗin tayi mamakin ganin yarda azmee tayi uban aiki duk ita kaɗai, da alama ma tun bayan sallar asuba bata koma bacci ba,saboda tasan cewa dole manyan baƙi su hallara saboda zuwa duba fawan,
..shirya ma sehrish tayi breakfast ɗin SGR acikin ƙayataccen tray sannan ta miƙa mata, ruƙo wa tayi a hannunta sannan ta miƙi hanyar zuwa part dinsa, tana cikin tafiya taji anyi gyaran murya juyowa tayi da sauri don taga wanene junaid ne tsaye jikinsa sanye da shirt pulover tare jeans,
......har ya kammala shiryawar shi cike da ɗaukin kaita makaranta ya fito, sai faman zabga murmushi yake yi sam baida wata damuwa, ɗan dawowa baya tayi dai² saitinsa sannan tace "junaid ! Ya akai naga kana ta faman zabga murmushi, kai bakasan meke faruwa ba acikin gidan nan"? tayi maganar tana kallon shi,
..cikin mamaki junaid yace "kamarya kenan? meya faru ne ni bansan komai ba,"
 Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"jiya wani abu ya faru mai matuƙar raxanar wa, zan faɗi maka amma bari nadawo," ta faɗi tare da saurin haye wa upstairs tana murmushi, taso ta faɗama junaid abunda ya faru amma azmee dake tsaye daga kitchen tayi mata alamar karta kuskura ta faɗa masa, shine dalilin dayasa tace mashi ya bari tadawo,
. tuni jikinsa yayi sanyi a ƙagare yake daya ji mai reesh zata sanar dashi,
 Kitchen ya wuce wurin azmee da sallama ya shiga sannan ya gaishe ta yana cewa "Aunty azmee a shirya mun breakfast a yunwace nake, gashi inaso nayi sauri nakai sehrish school,
 Sakin baki azmee tayi tana kallon shi kanta ya gama ɗaure game da lamarinsu su duka biyun, ita tagaza samun natsuwa saboda son takaima babban yaya breakfast ɗinshi, shi kuma junaid damuwarsa yakaita school,kowa da wanda ya damu dashi kenan,
 Zama yayi saman dining chairs yana jiran azmee dake shirya mashi bf ɗinsa ta kawo mashi yaci,
Acan ciki kuwa bayan sehrish ta isa part É—insa da sallama ta shiga baya cikin falonsa don haka ta wuce bedroom É—insa tsayawa tayi daga bakin door É—in sannan tayi masa sallama, da wannan sexy voice É—in nashi ya amsa mata, tare da bata permission din shiga daga ciki,
.a hankali tasa ƙafarta ta shiga ciki tsayawa tayi zuciyarta na faman bugawa ba ƙaramin kyau yayi mata ba,
ya juya bayansa yana tsaye a agaban mirrow jikinsa na sanye da bathrobe white colour wadda ta tsaya mashi dai² guiwarsa,a buɗe rigar take bai ɗaure igiyarta ba, amma akwai shorts ajikinsa,sumar kan nan tashi ta zubo mashi tayi irin Curly ɗin nan dark brown very smooth ta rufar masa abayansa, da alama bai jima da fitowa daga wanka ba,
...gaba É—aya jikin sehrish ya gama mutuwa murus cos aduk time É—in da tayi arba da wannan kyakkyawar surar jikin tashi rasa hankalinta take yi gaba É—aya duk ta bi ta susuce,tana hangen shi ta cikin mirror saboda madubin yana facing dinta,
 tabbas yaji alamar shigowar mutun tun da harya bada iznin shigowa daga ciki amma har yanzu baiji an motsa ba, a hankali ya ɗago da blue eyes ɗinsa ta cikin mirror ɗin karaf suka sauka akan na rishi dake tsaye jikinta na rawa ɗan zaro idanun nata tayi tana kallon nashi dake kallon cikin nata ta cikin mirror, hankali atashe cikin tsananin tsoro tayi saurin sunnar da nata ƙasa gabanta na faɗuwa,
 gyaran murya ya ɗanyi kafin yace"a ajiye mun shi a palor, sannan agyara mun bedroom dina,' amsa mashi tayi da "toh" sannan ta juya ta fuce tana faman sauke ajiyar zuciya, a saman table ta ajiye masa sannan ta ɗan tsaya tana jiran ya kammala kimtsawa,after some minutes ya fito jikin shi sanye da tunic shirt milk colour tare da trouser, sai ƙamshi yake fitarwa, shiga cikin falon yayi ya samu wuri ya zauna saman royal sofa ɗin sannan ya shiga yin breakfast ɗinsa anatse,
Wuce wa sehrish tayi cikin bedroom É—insa ta shiga gyara masa shi komai agyare yake,bedsheet É—inne kawai da yayi squeezing ya tattare inda ya kwanta, cire shi tayi sannan ta musanya masa wani sabo mai kyan gaske ta shimfiÉ—a masa, bayan ta kammala gyara ko'ina cikin sauri tafito saboda tunawa da school karta yi late, a lokacin da ta fito samun shi tayi yana yin waya da alama kan fawan suke magana da mutumin daya kira shi awaya,Â
   Kama hanyar fita tayi har takai baƙin ƙopa ta ɗan juyo tana kallon shi gudun kar ace yana buƙatar wani abu gashi zata tafi batare daya bata izni ba, ganin alamar mutun ta wutsiyar idonshi yasa shi ɗan juyawa karaf suka haɗa ido da sehrish dake tsaye tana kallon shi cikin sauri tace "Can i go"? tayi maganar aɗan tsorace,
 Lumshe idonshi yayi tare da ɗan jinjina kai alamar eh,
 Murmushi sehrish ta saki sannan ta fuce cikin sauri aranta tana cewa "Sannu bata hana zuwa,"😇
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.