Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
A katafaren gidan nan nasu inda sukayi rayuwa shi da abu,tare dasu hajiya Ameena anan yakai yaran,cikin gidan ya shiga tare dasu,ya rage kayan jikinshi,sannan ya bisu ɗaya bayan ɗaya da kanshi yayi masu wanka acikin toilet,ya wankesu tass ya kuma wanke masu gashin kansu da shampoo,bayan ya kammala yi masu wankan,anan bedroom ɗinshi,ya shafe masu jikinsu da mai,ya gyara masu sumar kansu,sai da yabi kowaccensu yayi mata kalaba guda biyu akanta,ba ƙaramin kyau sukayi ba,bayan ya gama yi masu kitson ya hau saman gadon tare dasu ya kunna masu cartoon awayarshi na tom and jerry suna kallo,
Shigowa haris yayi cikin ɗakin hannunshi ɗauke da manyan ledoji guda biyu,lokacin daya samu abusufyan kwance saman gadon tare da ƴan ukunnan duk sun manne mashi suna kallo,abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba,sae yaji aranshi dama a wurin abusufyan yaran suka taso,da sun ji daɗin rayuwarsu,
Ƙarasawa yayi tare da miƙa mashi ledar kayan,ya taso ya kar6a,kayan sawa ne daya siyo masu,sai kuma ledar abincin da yayi masu take away a restaurant,
Bayan haris ya fito daga É—akin ya fito falo yana jiran Abusufyan ya kammala shirya yaran su tafi asibitin,
Sanya masu kayan abusufyan yayi,sannan ya fiddo masu da take away É—in abincin suka zauna suna ta turawa a bakunansu,zuba masu ido yayi yana kallonsu,ganin ya kura masu ido yasa Hosana ta É—ebo abincin a hannunta takai mashi abakinshi don yaci shima,
Murmushi abusufyan yayi ya buÉ—e bakinshi ta sanya mashi abincin,a haka har suka kammala cin abincin,
Yayin da suke nan,Abu nacan tana haukan neman Æ´a'Æ´anta,gida gida haka ta dinga bi tana neman su hosana,har sai da Allah ya haÉ—a ta da Mijin maman sadeeq shi ne yake sanar da ita cewa wani matashin saurayi ne mai kama da yaran yazo ya É—aukesu,tunda taji hakan ranta ya bata cewar Abusufyan ne,jiki asanyaye ta koma cikin gidan,gefen gadonta ta zauna addu'a tashiga yi Allah yasa shine,in ma dagaske shinen Allah yasa karya dawo mata dasu hosana ya tafi dasu kawai duk inda zaije,tabar mashi su,
Lokacin da sukaje asibitin akayi masu gwajin jini,result É—in ya nuna cewa yaransa ne,nan fa suka shiga murna shi da haris,duk da sunyi mamakin taya akai yaran suka kasance nashi!hakan na nufin da cikinshi abu tayi aure,
Haris ne ya bashi shawarar su ɗauke yaran kawai karsu maidasu gidan nan,Abusufyan shima ya amince da hakan,bai maida su sehrish ba ya koma dasu gidansu,kusan kwana uku su sehrish sukayi awurin Shi,acikin waɗannan kwanakin sun samu kyakkywar kulawa a wurinshi,kullum sai sunce mashi yaje ya ɗauko oummansu itama ta dawo gidan,sai yace masu su ƙara haƙuri zai kawo masu ita,
Ana haka sayyadi yadawo tun bayan da aka sallami su sehrish da jahad daga asibiti bai ƙara leƙo gidan ba sae a wannan lokacin yayi ma abu zuwan bazata,tun aranar ya soma tambayarta ina ƴa'ƴanshi suke,banza takeyi mashi bata bashi amsa,jinjina kanshi yayi tare da cewa duk ma inda takai su zasu dawo ne da ƙafafunsu,
Aranar da yayi maganar,tsakar dare suna kwance abusufyan ne tsakiyarsu,hosana da jahad suna gefe da gefenshi,Sehrish kuma na kwance saman jikinshi duka ya sanya hannunshi ya dafe su,
Kwatsam yaji kukansu acikin kunnuwanshi,a firgice ya farka nan fa yaga tashin hankalin da bai ta6a gani ba,sai birgima sukeyi idanunsu sun canza launi,kowacce ta dafe kunnanta sae ihu takeyi,saboda sunansu da ake ambata da wani irin sauti mara daɗin ji,hankalin abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kar yaran su mutu,wata irin zufa ce ke tsastsafowa daga jikinsu,sharkaf suka jiƙe,
FaÉ—owa cikin É—akin haris yayi jikinshi na kerma,abusufyan na ganinshi muryarshi na rawa yace"Haris kalli yaran nan ka gani wlh bansan me ya same su ba,ko zamu kai su asibiti ne"?
Girgiza kai haris yayi tare da cewa"Ko mun kaisu asibiti babu abunda zasu iya yi masu!yanzun nan sayyadi ya kirani awaya ya sanar dani cewa mu dawo mashi da Æ´a'Æ´anshi in ba haka ba zasu mutu a hannun mu ne,kuma zaiyi shari'a damu akan laifin mun kashe mashi Æ´a'Æ´anshi,ina da tabbacin cewar duk shirinshi ne wannan,"
Jiki na rawa abusufyan ya sauko daga saman gadon ya É—auko hosana da jahad a hannnunshi,haris kuma ya É—auko sehrish,
Cikin mota suka sanyasu,sannan haris yaja motar suka nufi gidan Ya sayyadi,wuraren ƙarfe sha biyu kenan na dare,tun kan su ƙarasa ƙopar gidan suka hango sayyadi atsaye jikinshi sanye da jallabiya,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,
Parking ɗin Motar sukayi,da sauri suka ɗauko mashi yaran suka kai mashi,abun mamaki suna ƙarasawa inda yake sai gashi sun dawo cikin hayyacinsu,tun daga nan kowa yasha jinin jikinshi,
koda suka saukesu ƙasa,suna ta faman murza idanunsu,suna yin arba da sayyadi,jikinsu na kerma suka ƙanƙame abusufyan suka manne mashi tamkar zasu koma jikinshi,
Hasken fitilar kwan dake a kopar gidajensu da kuma hasken motar su abusufyan dake ajiye,shi ya taimaka masu wurin ganin junansu da kyau,
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Sayyad da kuma Abusufyan,maƙiya sun haɗu,
Haris ne yace"kaji tsoran Allah,laifin me abu tayi maka ita da yaranta da har kake son cutar da rayuwarta?
Murmushi kawai sayyadi yayi yana kallonsu yace"nagode sosai,da irin kulawar da kuka ba Æ´a'Æ´ana,naga an canza masu kaya,an kuma saya masu takalma,abu yayi kyau,kaga masu Ji da naira,ba kamar mu ba Æ´a'Æ´an malam shehu.......'
. afusace abusufyan ya katse shi da cewa"Kai malam!ka faÉ—amun taya akai ka auri abu da ciki na!don bincike ya nuna cewa yaran nan Æ´a'Æ´ana ne!ba naka ba!dama najima ina zarginka wlh!kai ba mutumin kirki bane!"
shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"Oh kanaso kasan yadda akai na auri abu da cikin ka"?
Har suna haÉ—a baki shi da haris wurin cewa Eh,
Dariya sayyad yayi kafin ya matso dab da Abusufyan suna fuskantar juna ido cikin ido yace"tabbas Ƴan ukun nan ba ƴa'ƴana bane!naka ne halak malak,tun lokacin da kuka rabu da abu ta sanar dani cewa tana jin tashin zuciya,anan nagane cewa tana ɗauke da cikinka,shine na kwantar da cikin ta hanyar yin amfani da sihiri na,babu wanda yasan cewa tana da ciki har na aureta,sannan na bayyanar da cikin a jikinta,don su taso amatsayin ƴa'ƴana.......'
Katse shi haris yayi da cewa"meyasa kayi hakan toh"?
Sayyadi yace"bana faÉ—in dalili sai dae kawai in bada amsa,'
Jiki asanyaye abusufyan yakai idanunshi kansu hosana dake manne ajikinshi sun ƙankameshi,alamar basu so yabarsu anan,tuni yaji hawaye sun cicciko mashi a idanunshi aranshi yace ashe dae dagaske jini na ne su,
"Amma meyasa ka auri abu?yanzu nake kokwanton cewa anya don kana sonta ka aure ta"?
sayyad yace"ina fa?ni sam mace bata gabana!namiji kawai,da maza nake mu'amalata,Na auri abu ne duk don saboda in samu hanyar da zan shiga rayuwarka,kuma na samu,'yayi maganar yana nuna su sehrish dake ƙankame da jikinshi,
Rae a6ace haris ya cakumi wuyan rigar sayyadi yana cewa"wlh bazamu ƙyaleka ba,mugu azzalumi!zamuyi ƙararka kotu akan yaran nan,'
Dariya yayi tare da cewa"nafi ƙarfin kotu haris!babu abunda zasu iyayi mun,'
""Idan ka fi ƙarfin kotu ae baka fi ƙarfin Allah ba,zamu kai ƙararka wurinshi,kuma insha Allahu sayyad ba zakayi kyakkywan ƙarshe ba,sae kayi mummunan mutuwa kamar yadda mahaifinku kakah yayi......'
Buge hannun haris yayi daga cakumar wuyan rigarshi da yayi,cike da mamaki yace"Oh ashe ka gane ni!"
jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"bangane kaba,amma tunda ka ambaci cewa kana son shiga rayuwata na gane cewa kai daga family ɗinsu kakah kake,Azzaluman mutane,mugaye waɗanda suka mayar da zalunci hanyar cin abincinsu,masu tada ƙayar baya a ƙasarmu,asannu asirinka zai tonu kamar yadda na ubanku ya tonu kuma insha Allah,Abbana da kuma yayana Hussein,kai bama su kaɗae ba nayi maka alƙawarin cewa a hannun ɗaya daga cikin jikokin Amminmu zaka Mutu,mummunar mutuwa kuma a wulaƙance kamar dabba haka zakayi ta,idan Allah ya nuna mun wannan ranar ni kuma zan tuna maka waɗannan kalaman da nayi maka,
Hannu Abusufyan yasa tare da dafa kawunansu sehrish dake manne da jikinshi yace"idan Allah yasa su kayi tsawancin kwana basu mutu a hannunka ba,A gabansu za'ayi komai,"
Fashewa da dariya sayyadi yayi hada dafe cikinshi,lokaci guda kuma ya tamke fuskarshi tamkar bai ta6a yin dariya ba yace"kai fa ƙaramin ɗan iska ne mai kwana da wando,har yanzu bakasan wanene sayyadi ba,labarina kawai kake ji,nafi ƙarfin duk wanda kake tunanin zai iya ɗaukar fansa akaina!danginku gaba ɗaga babu wanda zai iya ɗaga mun yatsa,kuma inaso na sanar maka cewa muna nan muna shirin tarwatsa farin cikin zuri'arku,muna nan muna shirya maku maƙarƙashiya,bani kaɗae bane yawa gare mu kuma muna nan kewaye daku,'
Kallon juna haris da Abusufyan sukayi kafin su mayar da idanunsu kan Sayyadi,
"Daga rana irin ta yau!ina mai gargaɗinka da cewa kada ka kuskura ka ƙara yunƙurin zuwa ɗaukar yaran nan!wlh in har ka ƙara takowa kazo inda suke!ko kuma ka turo wani naka da niyyar ya taimakesu!koma wanene sai ya Mutu!!!!na sanya katanga a tsakaninku dasu,zaku iya tafiya,"
Ya ƙarasa maganar tare da nuna masu hanyar inda motarsu take da hannunshi,hannu abusufyan ya sanya yana ƙoƙarin raba su hosana da jikinshi kuka suka fashe dashi suna roƙonshi akan karya tafi yabarsu a hannun wannan mutumin basu son zama dashi........'wata irin tsawa ya sayyadi ya daka masu a gigice suka raba jikinsu dana abusufyan suka shige gida da gudu suna kuka,ashe Abu tana a la6e a zauren gidan tana sauraronsu,tun lokacin da abusufyan yazo da su hosana,tasha kuka kamar taje ta rungumoshi ajikinta haka ta dinga ji,kamar ta zauce tayi hauka,su hosana na shigowa ta haɗasu duka ta wuce dasu ɗakinta,anan suka zauna suna ta sharar kwalla,
Jiki asanyaye abusufyan da haris suka shige cikin motarsu,tun daga wannan lokacin ne abusufyan yabar Nigeria ya koma Turkey gaba ɗaya,bai ƙara leƙo nigeria ba,ya nesanta kanshi da kowa ne saboda bazai juri zuwa nigeria ba,yayin da ƴa'ƴanshi suke rayuwa awulakance baida ikon taimakonsu ko ya sanya a taimakesu,sai dae Addu'a da yake binsu da ita.
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.