Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
 Sehrish~
Â
Koda ta fito daga part ɗin omar, wuri ta samu anan upstairs ɗin ta zuƙunnna tana shan kuka ba don komai ba sai don baƙin cikin kasa furta sunan haroon da tayi, taso ta sanar ma Omar kodan ta fita zargi amma hakan yaci turo saboda maƙoshinta da taji an shaƙe mata shi, babban abunda take fargaba shine kada su fara zarginta akan abunda ba laifinta bane, yanzu kuma duk ranar da sgr ya tuna da wannan abun daya faru a tsakaninsu dole ya tuhume ta, batasan wane irin kallo zaiyi mata ba,😖
 "Ashe so yayi ya kashe ni !" ta furta cikin sanyin murya, "ni bansan me nayi mashi ba, ya Allah ka kare ni daga sharrin shi, ya Allah kada ka bashi nasara akaina,"Â
 tana cikin wannan tunanin sam bata ji takon tafiyarshi ba, fitowarshi kenan daga part dinsa ya kimtsa cikin suits farare ba Æ™aramin kyau suka yi mashi ba,Â
 tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yarinyar da yake ta faman jira ta gyara mashi bedroom dinshi itace zuƙunne tana shessheƙar kuka, cike da mamaki ya ƙarasa har inda sehrish take sam bata zaci ganin shi ba, sai dae taga ƙafafunshi masu sanye da haɗaɗɗun takalma, gabanta ne taji yayi wani irin bugu duk da bata san wanene ba amma tana da tabbacin cewa shi neeee saboda ƙamshin turaren nan nashi,
  ƙara Æ™anÆ™ame jikinta tayi tana faman zazzare ido a tsorace, muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa"ke tashi tsaye,"Â
 cikin sauri sehrish ta miÆ™e tsaye jikinta na kerma kamar wadda taga wani horror sam taÆ™i yarda ta kalli fuskarshi saboda ta tsorata dashi,Â
  shiru ya É—anyi baice komai ba tamkar mai nazarin wani abu, hannunta yabi da kallo sai faman kerma yatsun hannun suke yi,Â
 "Are u okey"? ya tambayeta,cikin sauri tace"eh"Â
  "Okey agyaramin bedroom ɗina," yana faɗin hakan ya kama hanya ya wuce,
 Sam takasa janye idanunta daga kallon bayanshi har sai da ya 6ace ma ganinta, sannan ta wuce part din nashi, lokacin data shiga bedroom dinshi ba komai ta tuna ba face abunda ya faru atsakaninsu daren jiya, bin shimfiɗeɗen gadon shi tayi da kallo har yanzu zanin gadon a cukuikuye yake, saboda damben da suka sha jiya, hannu takai tare da yaye bedsheets ɗin nashi ta rungumo shi a kirjinta tana shinshina ƙamshin turarensa, ita kaɗae tasan irin yanayin da tashiga a wannan lokacin duk da firgicin da take ci amma hakan bai hanata jin wannan yanayin ba.............💋😉
*💋Boss💖Batureâ?*âœï¸
A galabaice take hura wutar murhun wani irin uban hayaƙi yake fitowa baƙiƙƙirin duk ya cika kitchen din, idanunta sunyi jawur kamar na mai shan taba, matashiyar yarinyace da bazata wuce shekara goma sha huɗu ba aduniya, a wani matsakaicin gida na masu rufin asiri, jikinta na sanye da koɗaɗɗen zani na atampha tayi ɗaurin gaba dashi, duk ya yayyage jikinshi yayi baƙiƙƙirin saboda dauɗa, gaba ɗaya ita kanta yarinyar abun ban tausayi ce, ta bushe ta rame ta ƙanjame yadda kasan skelaton haka take, saboda kasusuwan wuyanta da suka firfito mata waje kamar zasu fito daga fatar jikinta saboda tsabar rama, saboda koɗewar da fatar jikinta tayi baza ma a iya tantace launin fatarta ba, fara ce ko baƙa 😢
sai faman goho take yi agaban murfin tana hura wutar da bakinta amma wutar taÆ™i kama wa, zuÆ™unnawa tayi gaban murhun ta zabga uban tagumi hawaye na faman kwararowa daga idanunta, cikin murya kuka ta soma cewa"Ya Allah ka kawomin karshen wahalar da nake sha acikin gidan nan........'Â
  Muryar mammynsu ce ta katse ta da cewa"AMAL!! wai uban wa kike so yayi wankin nan ne? zaki fito kiyi shi ko saina maki dukan tsiya ne? Hankali atashe tace"mammy iccen girkin ne É—anye baya ci, tun É—azu nake faman wahalar hura shi amma yaÆ™i ruruwa,"Â
 Uban tsoki matar ta buga tare da cewa"wannan ba damuwa ta bace ba, ki tabbatar da kin hura wutar ta kama,sannan ki fito ki wanke mana kayan mu, bayan kin gama kuma ki share gidan,"Â
  cikin ƙunar rai ta amsa mata da "toh,"
Sannan taci gaba da hura wutar don ta kama,Â
  cigaba da magana matar tayi tana cewa"Yayarki nacen gidan huta, ta manta dake gaki nan a wulaƙance kin zama tamkar baiwa a wurin mu, da ace tana sonki ae bazata barki a hannun mu ba,"
  Shiru Amal tayi hawaye na zuba daga idonta, har yau tagaza yarda cewa yayarta zata iya yi mata hakan, saboda me zata tafi tabarta hannun waɗannan mugayen? Ta tambayi kanta,
  muryar mammyn tasu ce ta sake katse ta da cewa"hmmm dama tsiyar talaka kenan anyi mata hanyar arziƙi amma ta manta da mutane, baƙin halinku iri ɗaya dana uwarku, ae duk laifin laila ne ko uban waya faɗa mata ana yiwa ƴa'ƴan kishiya abun arziƙi," tana zaune saman gujera ƴar tsugunno sai faman sambatu takeyi kamar zautacciya, wata tsamurarriyar mata ce fara siririya ta fara tsufa don gashin kanta harya fara hurhura, jikinta na sanye da atampa riga da zane, ta tsoge ɗaurin ɗankwalin nan ture kaga tsire, hannunta na ruƙe da aswaki sae faman kwalkwalar haƙoranta takeyi wadanda sukayi jawur saboda tsabar cin goro, kai kana ganin ta zaka shaida cewa ba ƙaramar jarababbiya bace, irin tsaffin nan da basa gajiya da mita,
  daÆ™er Amal tasamu wutar ta huru, sannan ta fito agalabaice, kai tsaye ta wuce inda uban kayan wankin suke dila guda,gaba É—aya kayan sawarsu ne su duka dana uwar dana su abra da hayam, ga zannuwan gado da barguna duk sun tara mata su don ta wanke, abun babu imani acikin shi, babu irin wahalar rayuwar da yarinyar bata shaba,uÆ™uba iri iri suke yi mata, ko bacci bata samu, in ma tayi baccin da duka suke tashinta, ko kuma taji saukar ruwa bokiti guda ajikinta, fatar jikinta duk cizon sauro ne gashinan ruÉ—u ruÉ—u, saboda awaje take kwana, su kuma su shige É—aki sai ita kaÉ—ai ga tsora da Allah yayi mata, kullum cikin zullumin mai zai faru da ita take yi, duk yarda taso su haÉ—u da yayarta abun yaci tura, a halin da ake ciki ita kanta Amani batasan cewa yarinyar na raye ba, tun wani zuwa da tayi suka sanar da ita cewa yarinyar ta 6ace an neme ta an rasa, hankalinta ba Æ™aramin tashi yayi ba, a lokacin tasha kuka sosai wurin neman yarinyar amma babu ita babu alamarta, tun tana sanyawa a nemo mata ita har tagaji ta daina saboda kullum babu labarin anga yarinyar shiyasa ta fidda rai da ita, ashe lokacin 6oye yarinyar sukayi a gidan makwabtansu acikin wani É—aki aka rufe ta kamar akuya, duk in amani zataso maiduguri sai su kaita can gidan ajiya har tazo ta tafi bazata sani ba, hakan yasa basu ta6a haÉ—uwa da ita ba tun auranta da Abbas na wata takwas a lokacin abun ya faru, taso ta É—auki yarinyar ta zauna a wurinta amma saboda baÆ™in hali irin nasu sun hanata ganin Æ´ar uwarta....ðŸ˜
  "Maza ki hanzarta ki wanke mana kayan," muryar mammynce ta katse ta,
  Hannu tasa ta ɗauki bokitin dake ajiye awurin kayan, sannan ta wuce izuwa inda fanfonsu yake,ruwa ta tarbo acikin shi sannn ta ɗauke shi tadawo ta ajiye, ledar klin ta dauka tare da fasawa ta zazzaga aciki sannan tashiga tsoma kayan aciki tana wankewa idonta na zubar da kwalla,
   suna cikin wannan zaman suka ji ƙarar dirar mota a ƙofar gidan, washe baki mammy tashiga yi tana cewa"ƴar albarka ta iso, nasan tadawo mana da abun arziƙi, ni dae naji daɗi ƴa'ƴana badae farin jini ba........' bata ƙarasa maganar ba Hayaam tashigo cikin gidan ba ƙaramin wanka ta ɗauka ba, jikinta na sanye da swiss lace ash colour, doguwar riga akayi mata dashi, ta matse ta tsam tamkar in tayi motsi rigar zata yage saboda yarda tayi tighting ɗinta, ta kashe ɗaurin kallabi nan, mayafin kuma ta aza shi a kafaɗa,
  fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa wurin mammyn tasu, tashi tayi ta rungumeta tana cewa"ƴar albarka sai yau zan saki a idona"?
 Murmushi hayamm tasaki tare da cewa"Ammi yau ɗin ma sa'a kika ci, ki gode ma Allah da kika ganni yau, domin kuwa gobe zan wuce abuja nazo ne nayi maki bankwana saboda zan koma can da zama ina fata Aunty laila ta sanar dake game da komawa ta can? Ta tambaya tana kallonta,
  gaba ɗaya Amal ta kasa kunne tana sauraronsu,
  Washe baki tayi tare da cewa"ta sanar dani mana, ae ba ƙaramin daɗi naji ba kwara ki tattara ki tafican kema ki shafo mana arziƙi,"
  Fari da ido hayaam tayi tare da cewa"baki da damuwa in dae nice mommy, arziƙi mun gama yin shi, muddin burina ya cika tuni zan canza maku tamfatsetsen gida na kece raini, na siya maku manyan motoci na alfarma sannan na biya maki aikin hajji, mommy kuɗi fa har sai kin gaji dasu wlh," ta faɗi tana faman sakin murmushi,
  Cike da farin ciki mammy tace"Allah?
 "wlh kuwa mommy," hayamm ta bata amsa,Â
  ganin amal na kallonsu yasa mammyn kwatsa mata tsawa tace"zaki mayar da hankalin ki kan kayan da kike wankewa ko saina zo nan na karya maki wuya, magulmaciyar banza ƴar sa ido," jiki na rawa amal ta mayar da hankalinta kan kayan da take wanke wa,
   ruƙo hannun hayamm mammyn tayi sannan tajata suka shige cikin ɗakinsu, don kar taji me zasu ce,
  a hankali take wanke kayan tunani iri iri na zuwa mata aranta, tana yawan jin suna ambaton abuja abuja, kodai can aunty amani take zaune ne? Ta tambayi kanta, jinjina kai tayi tare da cewa"ina da tabbacin cewa auntyna tana zaune acan itama, dole na nemi mafita bazan zauna su kashe ni ba, zan gudu ne batare da saninsu ba," ta fadi tare da tsame rigar da ta sanya acikin ruwan wankin..........'😳
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.