Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
daker suka samu suka yi wanka suka canza kaya izuwa jeans da t-shirt suka fito wuraren ƙarfe 5 na yamma, tafiya suke yi gabansu na faduwa tsoransu kar suci karo da haroon don yanzu ya zamar masu tamkar dodo, suna cikin tafiya sai ga Junaid ya fito daga upstairs yana ganinsu ya ɗan zaro ido cike da murna yace "Yaya Jahan ina kuka shiga inata neman ku, naga da safe ko breakfast ba kuyi ba, duk na shiga damuwa," ya yi maganar tare da ƙarasa saukowa down ɗin yayi ya tunkaresu, suna tsaye baki asake suna kallon shi saboda neman shi suke yi ruwa a jallo,
yana ƙarasawa yabi su ɗaya bayan ɗaya yayi hugging ɗinsu tare da manna musu kiss a gefen fuskarsu, irin gaisuwar da suka saba,
Ganin sun zuba mashi ido batare da sunyi mashi magana ba yasa shi bubbuga ƙafarsa tare da cewa "Dan Allah wai menene haka duk kun Canzamin, ko magana ma ba zaku iya yi mun ba why pls? ya faɗi tamkar zaiyi kuka,
gyaran murya jahan yayi tare da cewa "no ba haka bane junaid, ba mu jin daÉ—i ne, ni da Ayaan shiyasa ka ganmu a haka, yanzu haka ma kai muka fito nema akwai maganar da muke son yi dakai, amma ba'a nan ba, acikin É—akin ka,"
junaid yace "magana kuma dani? Allah yasa ba laifi nayi ba"
Murmushi Ayaan ya saki tare da cewa "ba laifi kayi mana ba junaid taimako ne ma zakayi mana,"
ruƙe ƙugunsa yayi sannan yace "Naji toh, amma kafin nan sai naga kun ci abinci tukunna, saboda baku ci komai ba tun safe ina sane da hakan, bayan na hana ku zama da yunwa,"
Yadda yayi maganar tamkar wani yayansu, alhalin sun girme shi,
Murmushi suka saki atare sannan jahan a ruƙo hannunsa tare da cewa "Zamu ci abincin ne,amma kafin nan, mu shiga daga ciki muyi magana,
tasa ƙeyarshi su kayi har cikin ɗakinsu, suka tsaya daga tsaye suna fuskantar shi, gaba ɗaya sun rasa ta inda zasu soma neman alfarmar nan a wurin junaid,
Ganin sun tsayar dashi sun zuba mashi ido yasa shi hasala tare da cewa "Yaya Jahan nifa bansan menene ma'anar zuba mun idon nan da kuka yi kuna kallona ba," ya faÉ—i yana hura hanci,
Ayaan ne ya soma magana "am...junaid ka gane, dama wata alfarma ce muke nema awurin ka,
"Am listening to u," junaid ya faÉ—i yana kallonsu
Jahan ya daura da cewa "junaid sabo da mu zakayi wannan abun, so muke ka kira Mommy a waya video call ka bata haƙuri sanna ka ambaci sunanta ka kirata da Mommy, dan Allah junaid.........' tunkan jahan ya ƙarasa maganar tasa junaid yabi ta gefensu zai fuce daga ɗakin yana cewa "da nasan wannan alfarmar zaku nema awurina, wlh da ban 6ata lokacina wurin sauraronta ba,
Cikin sauri suka ruƙo rigar jikinsa har suna haɗa baki wurin cewa "Janaid dan Allah ka taimaka ma rayuwarmu, kai kaɗai ne a yanzu zaka iya fitar damu daga halin da muke ciki pls junaid do this favour for us"
a fusace junaid ya fusge rigar shi daga hannunsu yace "Wlh bazanyi ba, ni bazan ta6a kiran wannan matar da sunan mommyna ba, saboda bata sona ta tsane ni, Yana faɗin hakan ya kama hanyar fita, Ayaan yayi sauri sake cafko rigarsa, aikuwa a fusace junaid ya sanya hannunsa tare da buge na Ayaan, rai a6ace jahan ya janyo shi tare da kwashe shi da mari, zaro ido junaid yayi yana kallonsu yayin da ya sanya hannunsa ya dafe kuncinsa saboda zafin marin da jahan yayi masa, tunda yake arayuwarsa zai iya cewa ba'a ta6a bugunsa ba, ko da wasa wani bai ta6a yin gigin ta6a fatar jikin junaid ba da sunan bugun, amma sai gashi yau an samu wasu daga cikin yayyansa da yake matuƙar ƙauna yasa hannu ya mare sa, tuni idonsa sun ciko da kwalla red lips ɗinsa har rawa suke yi wurin cewa "Yaya jahan ! Yau kai da kanka, kasa hannu ka mare ni? Saboda na bijire ma buƙatarku? akan abunda yake haƙkina nifa aka cuta, abun har yanzu yana yi mun ciwo azuciyata bana faɗi ne kawai..............' kuka ne yaci ƙarfinsa har ya gaza ƙarasa maganar tasa yaci gaba da sharar kwalla, tuni jikinsu yayi mugun sanyi musamman jahan daya mare sa, baisan lokacin da shima ya fashe da matsanancin kuka ba, hakan yasa junaid dakatawa da kukansa ganin yarda Yayansa jahan ke kuka agabansa tamkar ƙaramin yaro, nan take hankalinsa ya tashi cikin sauri yasanya hannayensa a fuskar jahan yana share masa hawayensa yana cewa "dan Allah yaya jahan ka daina kuka, bana son ganin hawayen nan naka, in dai ni ne na sanya ka, yin kuka wlh zan baka hakuri ka yafe mun bazan ƙara,
Cikin shessheƙar kuka jahan yace "junaid naji na tsani kaina fiye da tunaninka, wai yau ni ne na kasance mutun na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ka, da wannan mummunan hannun nawa, ina danasanin wannan ranar kuma bazan ta6a yafe ma kaina ba..........' gaba ɗaya tausayin jahan ya gama kama junaid cikin sauri ya janyo shi ajikinsa tare da rungume shi sosai yana ɗan bubbuga bayansa, cikin muryar rarrashi yake cewa "Ba laifinka bane yaya jahan, Laifina ne nayi rashin kunya, na buge hannun ayaan duk da raina ne a6ace bansan nayi hakan ba, amma ku yafe mun abisa kuskuren da nayi maku bazan ƙara ba,'
gaba É—ayansu sun shiga cikin wani kalar yanayi, Ayaan kam tuni jikinsa ya gama mutuwa saboda tausayin junaid da kuma kansu daya kama shi,
Bayan sun tsagaita jahan ya janye jikinsa daga na junaid sannan yace "Junaid dan Allah kayi mana wannan alfarmar na roƙe ka kai kaɗae ne zaka iya fidda mu cikin halin da muke ciki, kuma nason kana tsananin son mu ba zaka so wani abu ya cutar damu ba,' ya ƙarasar maganar yana kallonsa da idanunsa da suka gama runewa,
Jiki a mace Jahan ya kalli Ayaan cikin tsananin damuwa, ganin junaid yayi shiru baice komai ba yasa su yin saurin zubewa agabansa saman guiwowinsu suna roƙonsa,
Cikin tsananin tashin hankali shima junaid ɗin ya zube saman guiwowinsa agabansu tare da fashewa da wani sabon kukan yana cewa "meyasa zakuyi mun haka?yaya Ayaan da ya jahan saboda me zaku duƙamin nifa ƙaninku ne, ku kuma yayyena ne dan Allah kudaina mun hakan banaso! banaso!!bana so!!" ya ƙarasa maganar tare da cewa "naji na amince zan kirata, Amma ba yanzu ba,"
ajiyar zuciya suka sauke gaba É—ayansu nan take suka ji wani irin sanyin ya ratsa zuciyoyinsu,
Ayaan yace "yaushe zaka kirata"? Junaid yace "an jima kaÉ—an," ya faÉ—i a shagwa6e
Murmushi suka saki gaba ɗayansu har haɗa hannu suke yi wurin goge masa hawayansa da suka wanke masa fuska, har lokacin suna a zuƙunne su duka ukun suna fuskantar juna,
Jahan yace "Am Sorry junaid, ka yafe mun marin da nayi maka, nayi dana sani sosai," ya faÉ—i cikin sanyin murya,
Junaid yace "gsky bazan yafe ba yaya Jahan har sai kunci abinci sannan nagani da idona tukunnan,
Ayaan yace "shikenan junaid komai kake so zamu yi,"
Murmushi ya saki sannan ya ruƙo hannayen su suka miƙe tsaye atare, bayan sunyi wiping tears ɗinsu, Sannan suka fito daga ɗakin nasu,
Ajere suka jera suna tafiya sun sanya shi tsakiyarsu a lokacin Sehrish da azmee suna a cikin kitchen suna aikace-aikacen girkin dinner É—in gidan,
Sai da junaid ya tabbatar Ayaan da jahan sun zauna saman dining chairs É—in sannan yace "ku jira ni, yanzun nan zan kawo maku abinci ku ci," ya faÉ—i da murmushi a fuskarsa sannan ya wuce kitchen É—in,
har lokacin jahan dana sani yake yi akan marin da yayiwa junaid,ya gaza yarda cewa shi da kansa ya ɗaga tafin hannunsa ya zabga ma romeo ɗinsu mari, yana ganin abun tamkar a mafarki,😥Kitchen ya wuce yana ganin sehrish ya soma sakin murmushi, sallama yayi masu sannan ya shiga, amsa mashi su kayi gaba ɗayansu, sannan ya matsa wurin sehrish dake agaban chopping board tana yayyanka kayan lambu,
 "Reesh idan akwai abun da kuka kammala inaso ki shiryamun a tray zan kai ma yaya Ayaan da Yaya jahan ne, yunwa suke ji ssae," ya faɗi yana yamutsa fuska tamkar shike jin yunwar, zuba mashi ido sehrish tayi tare da cewa "junaid ! meya faru dakaine? waya mare ka har haka"?
  Cikin sauri junaid yasa tafin hannunsa ya rufe gefen fuskarsa yane cewa"ki daina É—aga murya sehrish kada wani yaji, banaso wani yaji kiyi shiru kawai da bakin ki,"Â
Jikinta ne yayi wani irin sanyi aranta tana mamakin yarda akai har wani ya aza tafin hannunsa a fuskar junaid ga sahun yatsu nan sun bayyana raÉ—au a fatar fuskarsa yayi jawur wurin,
Jinjina kanta kawai tayi tare da cewa "Shikenan bari na shirya maka abincin ka kai masu," ta faÉ—i tana kallonsa cikin jin tausayinsa,
Ajiyar wuÆ™ar hannunta tayi sannan ta wuce ciki donta haÉ—a masa, hannu yasa ya É—auki knife É—in da ta ajiye yaci gaba da yanka mata lettus É—in data bari,Â
Azmee ce ta taya ta zuba masu acikin warmers duk tana jin magananun da suka yi ita da junaid, aranta tana mamakin marin da taji sehrish ta ambata anyiwa junaid, har satar kallonsa tayi taga yarda fuskarsa tayi jawur gefen da aka maresa ga alama nan tabbas in wani yaji acikin gidan sai an tada husuma,
  Ruƙo tray ɗin tayi a hannunta zata wuce takai masu cikin sauri junaid ya ajiye wuƙar ya tare ta da cewa "kawo na kai masu,"miƙa mashi tayi yasa hannu ya kar6a yana kallon fuskarta da murmushi yace "thank u," itama murmushin ta sakar mashi duk tashiga damuwa akan yanayin fuskarshi,
 Yana karba ya fuce yakai masu, yadda yabarsu haka ya same su, sunyi zugudun suna kallon junansu, Jahan na ganinsa ya saki fara'a tare da cewa "Yawwa heart beat mun gode sosai da irin kulawar daka ba mu, duk ka damu akan mu," murmushi junaid ya saki a lokacin ya ajiye masu tray ɗin kayan abincin asaman table ɗin,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.