Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Yana cikin shan coffeen nan wani abu ya sarƙe mashi adaidai saitin throat ɗinshi,a hanzarce ya ajiye cup ɗin tare da zura fingers ɗinshi guda biyu cikin bakin cikin sa'a ya ruƙo siririn abun,
Lokacin daya fiddo da abun daga bakin nashi yayi arba da dogon gashi,ware idanunshi yayi, hankali a matukar tashe yana kallon gashin yace"in my coffee...!
Jin wannan maganar tashi yasa sehrish saurin juyawa don taga menene,a lokacin har tasa ƙafa zata fita daga ɗakin,
Gabanta ne taji yayi wani irin mugun buga ganin siririn gashin da Sgr ya ruƙo a hannunshi,
Yunkurin amai yashiga yi,nan take ya miƙe da saurin gaske ya faɗa toilet,kai tsaye ya ƙarasa gaban basin yana kwarara aman,tamkar ƴan hanjin cikinshi zasu fito,kasancewar shi mutum mai tsaftar gaske ga ƙyanƙyami ya tsani ƙazanta a rayuwarshi duk mun ƙankanta,ranshi ba ƙaramin 6aci yayi ba,gashi a abun shansa kuma har ya shiga bakinsa!!,a wannan lokacin komai zai iya aikatawa he can't even control him self, cos he has a very bad temper,kuma ta motsa.
Tap ya kunna,ruwa yashiga zubowa yana kora vomitting É—in da yayi,sannan ya tarba tafin hannayenshi biyu tare da É—ebo ruwan ya watsa su a fuskarshi yana faman sakin huci,
Sehrish dake atsaye abakin kopan bedroom ɗin nashi,jikinta sai faman kerma yake yi,gaba daya tabi ta rikice kan ta ya gama ɗaurewa,taya akai aka samu gashi acikin abun shan Sgr?ita dae tasan cewa ba gashin kanta bane,saboda ta sanya hijab ajikinta,hasalima ba ita bace ta shirya mashi kayan breakfast ɗin nashi ba,tunkan taga hukuncin da zaiyi mata har tafara matsar kwalla,don tasan bazai ƙyale ta ba,dole ya hukunta ta,
A fusace ya fito daga cikin toilet ɗin,sai faman huci yake yi,ɗagowa yayi da idanunshi yana kallon inda sehrish take atsaye jikinta sai kerma ya keyi,tunda taga zufa na gangarowa a gefen fuskarshi, ta ƙara tsorata sosai,
tamkar wani zaki haka ya tunkaro ta,a tsananin tsorace sehrish ta shiga ja da baya tana girgiza kai cikin shessheƙar kuka take cewa"wlh bani da masaniya akan gashin nan,banawa bane bansan ya akai ya shiga cikin abun shanka ba,'
wata irin tsawa da Sgr ya daka mata nan take sehrish ta firgita agigice take zazzare ido tana kallon fuskarshi,
biting lips É—inshi ya shiga yi,yama rasa wane irin punishment zaiyi mata,
Nuna ta da dogon yatsan sa yayi tare da cewa"as from today!bana son na ƙara ganinki a part ɗina!'
Cikin shessheƙar kuka sehrish tace"Am really sorry babban yaya........ba laifi na bane bada sani na gashin ya faɗa aciki ba..........'tun kafin ta ƙarasa maganar ya ɗaga hannunshi da nufin ya sharara mata mari,runtse ido sehrish tayi tana jiran jin saukar marin nashi a kuncinta,
ji yayi bazai iya ba saboda tunda yake arayuwarshi bai ta6a gigin ta6a jikin wata Æ´a mace ba da sunan bugu,tun suna yara Abbansu ya hane su da yin wannan,kullum yana tunasar dasu akan su dinga daraja Æ´a mace,
Dunkule hannunshi yayi tare da yarfar dashi gefe guda,sannan yace"Get out from my bedroom!since before I show u my true colour!,
ya ƙarasa maganar tare da juyawa yabarta tsaye anan tana faman shessheƙar kuka,
Ji tayi bazata iya jure hukuncin da Sgr yayi mata ba, na hanata aiki a ƙarkashin shi ba,
gaba É—aya jikinta ya gama yin sanyi, a wani irin yanayi ta zube asaman guiwowinta,cikin sanyin murya,muryarta na rawa tace"nasan na 6ata maka rai sosai,na cancanci kowane irin hukunci daga gare ka,amma ina neman alfarma a wurin ka........'dakatawa tayi da maganar tana kallon bayan shi daya juya mata,
ganin ya tsaya da yin tafiyar yasa ta gane cewa ita yake sauraro,
anatse taci gaba da magana"ka yanke mun kowane irin hukuncin daya dace da laifin dana aikata,amma kada ka hanani yin aiki a ƙarkashinka,wannan horon yayi mun tsauri sosai,bazan iya jurewa ba,tun da nake maka aiki banta6a yin irin wannan gangancin ba,ina kiyaye wa sosai wurin ganin na tsaftace duk wani abu da zan kawo maka kaci ko ka sha,ba zanso wani abu da zai cutar dakai ba,wannan ma bansan ya akai hakan ta faru ba,don Allah kayi haƙuri ka yafe mun............'ƙarasa maganar tayi cikin shashsheka yayin da hawaye ke cigaba da zuba a idanunta,
shiru Sgr ya É—anyi na wani lokaci batare da ya motsa ba,hakan yasa ta fidda rai da cewar zai yafe mata,
Hannu tasa tana sharar hawayenta tana kallon bayanshi,cigaba da tafiya sgr yayi kai tsaye ya tunkari wurin dressing mirror É—inshi,hannu yasa tare da janyo drawer chest din dake ajikinshi,sabon scissors ya É—auko cikin ledarshi, ya fiddo dashi yana kallonshi,
lokacin daya juyo hannunshi ɗauke da almakashin nan,hankali atashe sehrish ta zaro ido tare da miƙewa tsaye daga kneel down ɗin da tayi tana ja da baya tana girgiza mashi kai,alamar karyayi mata haka,
Gadan gadan Sgr ya tunkare ta,hannunshi ɗauke da almakashin nan sai faman salƙi yake yi,hannu sehrish ta aza asaman kanta tana cewa"Nashiga uku!innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..........dan Allah kada ka datse mun gashin kaina ......'tana magana tana ja da baya yayin da shi kuma yake tunkararta,abu kamar wasa haka suka shiga zagaye ɗakin yana binta tana ja da baya,a ƙarshe daya fusata a zafafe ya damƙo hijabin dake jikinta tare da tun6uke ta daga jikinta yayi wurgi da ita gefe guda,yarda ya fusge hijabin daga jikinta gaba ɗaya ta tafi zata faɗi kasa,yakai hannu tare da janyo ta ta faɗo saman wide chest ɗinshi,kuka take kamar ranta zai fita saboda ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nan nata ba,ta kwallafa rai akanshi shiyasa kullum take ƙokari wurin gyara shi,har tasamu tatara shi da yawa bayan yanke shin da akai da zata fara aiki gidan,gashi yau akan kuskuren da ba ita ta aikata ba,za'ayi mata aski tana ji tana gani ba yarda zata yi,
tunda sehrish ta faɗa jikinshi gaba ɗaya ya rasa duk wani kuzari na jikinshi,ƙamshin turaren jikinta ba ƙaramin kashe mashi jiki yayi ba,abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,a hankali yakai hannunshi tare da Cire ribbom ɗin da ta ɗaure gashin kanta dashi,ya warwaro shi duka tare da yin wurgi dashi gefe guda ya fadi kasa saman hijab ɗinta,
Nan take lallausar suman kan nata mai laushin gaske ya tarwatse abayanta yayi mata tamkar hijabi,
Ai ina baku labari tunda boss man É—in nan ya zura hannunshi acikin sumar kanta nan fa yashiga murza gashin acikin hannunshi,laushin gashin kan nata ne yake fisgarshi har yayi hakan batare da saninshi ba,
A hankali ya russinar da kanshi tare da kai tsinin hancinshi saman sumar kanta yana shaƙar daddaɗan kamshin dake fitowa daga cikin sumar kan nata,wani irin bugu zuciyarshi tashiga yi da sauri sauri take harbawa,
ƙankame shi sosai sehrish tayi ta hanyar zagayo da hannayenta abayan waist ɗinshi ta ruƙo shi sosai kamar wani zai kwace mata shi,ba ƙaramin yanayi ta jefa Sgr ba ta kara sanya mashi kasala ajikinshi,kamar yarda itama ta shiga yanayin,tunda ta lafe mashi ajikinshi tayi lamo,wata irin natsuwa ta ji
da bata ta6a ji ba atattare da ita,shessheƙar kukan nan da takeyi gaba daya ta neme ta ta rasa,tsit tayi tana sauraron heart beat ɗinshi,
Suna cikin wannan yanayin na shauƙi sai ga Abbansu ya faɗo cikin part ɗin nasa yana neman shi,ganin baya acikin falon yasa ya wuce izuwa bedroom ɗin shi,tunkan ya ƙarasa ya hange su manne da juna kamar tip da tyre, adaidai ƙopar shiga bedroom din nashi,abban nasu ya tsaya cike da mamaki yana kallon wannan abun al'ajabin,ko motsi basa yi,bakomai yafi ɗaure mashi kai ba,face yarda sgr yake cakuɗa sumar kan yarinyar acikin hannunshi sai faman murzar gashin kan nata yake,ga kuma hancinshi daya cusa asaman kan nata yana shaƙar kamshin da sumar kan nata ke badawa mai daɗin gaske,
Ita kuma ta ƙankame mashi qugunshi da hannunta,ta kwantar da kanta asaman chest ɗinshi,
baki asake Abbansu ke kallon wannan tashin hankali,jinjina kai ya shiga yi cikin ranshi yana cewa"Oh ni hussein!tun yaushe wannan al'amarin ya soma faruwa acikin gidan nan batare da sani na ba!Hmmmm yanzu haka zare mata ido yakeyi yana tsoratar da ita don ya samu abunda yake so,nasan maganinka Rafayet,"ya faɗi hakan tare da kama hanya yabar part ɗin nashi fuskarshi ɗauke da murmushi,don shi wannan abun farin ciki ne awurinshi,ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don tsabar farin cikin ganin rafayet tare da mace,baida burin daya wuce wannan arayuwarshi,shi dae yaga Sgr yafara kula mace da sunan soyayya,yau dae gashi Allah ya nuna mashi,
Janye hancinshi yayi daga cikin sumar kan nata,sannan ya tattaro gashin nata tare da sanya almakashin ya datse mata shi,sosai ya yanke gashin,yabar mata guntu wanda ko kafaÉ—arta bai sauko ba,'
hankali a matuƙar tashe sehrish ta raba jikinta da nashi, da sauri takai idonta akan hannunshi dake ruƙe da dogon gashin daya yanke mata,kamar a mafarki take kallon gashin nata daya yanke mata,
A hanzarce takai hannu tare da shafo kan nata don taji sauran daya rage mata,
Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita,dakyar takai hannu tare da É—aukar hijab É—inta, sannan ta juya tare da watsawa aguje tana kuka ta fuce daga cikin É—akin nashi,
ajiyar zuciya ya sauke tare da takawa izuwa gaban dressing mirror É—in nashi ya mayar da scissors É—in aciki tare da gashin kan sehrish daya datse,duka ya tura shi aciki ya ajiye,sannan ya maida drawer chest É—in ya rufe,
Komawa yayi tare da haye wa saman gadonshi ya kwanta,yanayin da bai ta6a ji ba atattare dashi ba yake ji,tsananin tausayinta ne ya kama shi,har ya dinga jin tamkar baiyi mata adalci ba daya datse mata gashin kanta,ya lura ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nata ba,lumshe idanunshi yayi a hankali yana tariyo abunda ya faru tsakaninta dashi,especially lokacin da ta watsa da gudu tana kuka,duk baiji daɗi ba saboda shi baiyi mata hakan da nufin ya 6ata mata rai ba.
 Â
  Â
  *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة ØØ¨ رومانسية بين Ø³ØØ±ÙŠØ´ ÙˆØ§Ù„Ø¬Ø±Ø§Ø Ø§Ù„Ø¹Ø§Ù… Ø±ÙØ§ÙŠØªðŸ’‹ðŸ’˜â¤ðŸ¤â¤ðŸ’•💖
Saboda masu complain, nacewa nace zan tura da safe ban turo ba,Allah ne bai nufa zan tura da safen ba,
Ga half page nan,later zan tura sauran
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.