Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Bayan sun kammala Sallar magrib,atare suka dawo a nan babban falon suka Hallara gaba ɗayansu banda Azmee da Hayaam da kuma su Sehrish,a lokacin Shima C.g Abbas ya ƙaraso gidan,kowa ya samu wuri ya zauna,Su fawan jabeer da kuma Irfan suna zaune a 3 seater,Abbansu tare da Uncle abusufyan suna zaune asaman 2 seater,Omar kuma tare da Sgr da Kanal yousouf suna xaune ne aɗayar 3 seater ɗin,Abbas da khaleed suma suna zaune asaman 2 seater,sai Aunty azeema dasu jahan kowanne na akan one seater,
Gyaran murya Abba yayi tare da kallon Abusufyan dake zaune zugudum agefenshi yace"kamar yarda ka buƙaci mu hallara gaba ɗayanmu a falo,gashi nan duk mun haɗu a wuri ɗaya kai muke sauraro,"
Nannauyar Ajiyar zuciya Abusufyan ya sauke kafin ya soma magana calmy yace"abunda yasa nace ku haÉ—u ku dukan ku wuri É—aya,saboda inaso in bayyana maku cewa ina da Æ´a'Æ´a,kuma Æ´a'Æ´an nan na same su ne ta hanyar daya dace,Banaso wani ya zargeni ne da laifin aikata zina,wlh ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar zina ba,ban ta6a kasancewa tare da matar da ba muharramata ba ina nufin ba matata ba.......'
 Shiru yayi na ɗan wani lokaci alamar yana nazarin wani abu,duk suka kasa kunne suna sauraron shi,kowa burinshi yaji taya akai Abusufyan ɗinsu ya samu ƴa'ƴa,kuma suwaye ƴa'ƴan nashi!?
"Shekara ashirin da ƴan kai da suka gabata,mun samu sa6ani da Ammi saboda rashin jin maganata,babu jituwa atsakanina da ita,bakomai yake haɗani da ita ba,face irin rayuwar dana taso inayi,abota da mata,na maidasu tamkar maza awurina yarda nake friendship da mata ko maza bana kulawa haka,wannan abunne ke 6ata mata rai,saboda ta tsani ta ganni tare da ƴan mata,ko in aka bata labarin cewa anganni tare da mace acikin mota,nan fa hankalinta zai tashi,a ƙarshe data rasa yarda za tayi dani shine,ta tattara mun kayana gaba ɗaya tace in koma Kano wurin ƙanwarta Hajiya Ameena inci gaba da zama acan,saboda nafi ƙarfinta ba zata iya dani ba don ta lura kaina rawa yakeyi,amma tana da tabbacin cewa in na koma wurin ƙanwarta zan shiryu in dawo dai dai,
Wannan ne farkon abunda ya rabani da gidanmu na koma wurin goggon mu da zama gaba daya,don ta gyaramun tarbiyyata kamar yadda ku su yaya hossein kuka sani,maimakon hakan sai ta sangarta ni saboda tsananin son da takeyi mun wanda ko ɗanta a wannan lokacin bata nuna mashi irin son da takeyi mun,komai nakeso shi takeyi mun,wankane kawai ba tayi mun,idan nayi laifi kuwa ko na janyo faɗa awaje rufe ido takeyi taita zazzaga masifa kuma tana sane cewa ni ne mai laifin,in mun shiga gida tayi ta lallashina tana bani haƙuri,
TUSHEN LABARIN,
Alhaji nuraddeen mai dala,hamshaƙin mai kuɗi ne kuma attajirin gaske,na bugawa a jarida,babban ɗan kasuwa ne wanda yayi kaurin suna a harkar kasuwancin saye da siyarwa atsakanin ƙasashe daban daban,haifaffen garin zariya ne,kuma yana ɗaya daga cikin Aminnan Salahuddeen,aiki ne ya kawo shi katsina kafin daga baya lokacin daya fara kasuwanci ya yanke shawarar komawa garin kano da zama saboda kasuwancinshi yafi ƙarfi acan,wannan dalilin ne yasa shi tattarawa ya dawo gaba ɗaya da zama anan kano tare da iyalanshi a katafaren gidanshi dake a unguwar Nasarawa g.r.a anan jihar kano,farkon haɗuwarshi da hajiya Amina kanwar Ammi wato goggon katsina,tun lokacin da suka je ɗaurin auren Salahuddeen da Ammi a jihar yobe damaturu,acan ya ganota ya ƙyasa,basu baro wurin ɗaurin auren ba sae da aka shafa fatiharsu su duka biyun a lokaci guda,
Yaronsu É—aya wanda sai da sukayi aure da jimawa kafin Allah ya albarkace su dashi,ba kowa bane wannan face Dr haris babban likita,shine É—a É—aya tilo da suke dashi,kafin Ammi ta mallaka mata Abusufyan don tagyara mata tarbiyarshi,sae suka kasance su biyu ne Æ´a'Æ´an dake a wurinta,É—anta da kuma É—an yayarta abusufyan,tom da kuma jerry,don gaba É—ayansu basa jin magana a wannan lokacin,Æ´an abi yarima asha kiÉ—ane,atare suke fita yawon dare,sun iya zuwa club a haÉ—u da Æ´an mata ayita rawa,zuwa wurin party kuwa koba a gayyace su ba sai sunje,wannan shine rashin jin da ammi ta tsana na abusufyan,shi dae haka rayuwarshi take baida burin daya wuce afita yawo tare da Æ´an mata akashe masu kuÉ—i,kullum yana manne dasu,shi dai kawai yaji mace akusa dashi ba namiji ba,kuma bawai don yayi wani abu da ita ba,sam shi wannan bai agabansa,
Ana haka su Abusufyan suka samu hutun makaranta,atare da dr haris suka je kai ziyara zariya wurin danginsu,
Bayan tafiyarsu ne,Hajiya Amina da Mijinta alhaji nuraddeen suka tafi umra,dama tun kafin su tafi alhaji ya sallami mai gadin gidansu baba buzu don yaje ƙasarsu niger ya gano danginshi kafin su dawo,
Ba ƙaramin daɗi yaji ba,saboda dama atakure yake na rashin ganin ƴar shi tilo da yake da ita,kullum yana cikin damuwar rashin yarinyar a kusa dashi,saboda halin da ya barota acan,basu da kowa danginsu duk sun tarwatse ba haɗin kai,ga talauci dake damun kowannansu,ita kanta yarinyar ya barta ne a hannun matar babanshi,tunda baida kowa iyayenshi duk sun rasu,matar nan ta tsani yarinyar ta takurama rayuwarta gata irin tsoffin nan ne masu mitar tsiya,duk wani aiki yarinyar take ɗauramawa,girki,sharar gida,wanki,ɗebo ruwa,kuma ƙarama ce alokacin bazata wuce 16 years ba,
Koda baba buzu yazo niger ganin gida,zuwan bazata yayi masu bai sanar ma kowa da maganar zuwan nashi ba,saboda yana so yaba Abu mamaki kuma yaga irin farin cikin da zatayi idan ta ganshi,kwatsam yana shiga gidan ya samu matar baban nan tashi zaune saman abu ta danneta a tsakar gida,yarinyar sai ihu takeyi tana wutsil wutsil da ƙafafunta,ita kuma matar sae sambatu takeyi tana cewa"Babu abunda zai hana inƙi kasheki acikin gidan nan Abu,dan ubanki ni zakiyi ma asarar tsintsiya?kin barta a ƙasa har ruwan sama ya jiƙata baki ɗauketa ba!ko don kina taƙamar ubanki ne ke turo mana da kuɗi muna siyan kayan abinci....'
Hankalin baba buzu ba ƙaramin tashi yayi ba a wannan lokacin,ganin zai rasa ƴarshi ɗaya tilo akan tsintsiyar shara da bata wuce naira hamsin ba,ba ƙaramin fusata yayi ba,a ranar ko zama gidan baiyi ba ya ɗauki ƴarshi ya tafi da ita gidan wani amininshi,tamkar ya zubar mata da hawaye haka yaji a wannan lokacin,yarinyar duk ta rame ta fige ta ƙanjame kamar ba mutun ba,yarinyar da duk garinsu babu wanda ya kama ƙafarta a wurin kyau,tun lokacin da mahaifiyarta ta haifa mashi ita,Allah yayi mata rasuwa tabar mashi ita ƴar jinjira da ita,shi yaci gaba da kula da yarinyar,mutane sunsha zuwa suna nuna mashi kuɗi don ya bar musu yarinyar su ruƙe awurinsu amma yaƙi amincewa da hakan,saboda son da yake yi mata,
Bayan hajiya Amina sun dawo nigeria ita da mijinta,Baba buzu ya shirya tafiya tare da ƴarsa abu,babu yarda abokinshi baiyi dashi ba akan ya bar mashi Abu suci gaba da kular mashi da yarinyar a hannunsu,amma ina yace ae ƙafarshi kafar abu,bazai ƙara gangancin barinta a wurin wani ba,kwara ta kasance atare dashi,yana jin motsinta a kusa dashi,zaifi samun kwanciyar hankali,
Da daddare suka ƙaraso nigeria bayan uwar tafiyar da suka sha agalabaice suka iso cikin gidan,ruƙe da hannun Abu ya shigo cikin falon gidan,lokacin hajiya ameena na zaune saman kujera mai mazaunin mutun uku tana kallo a tv,tun da sukayi sallama ta dago ta kellesu ganin baba buzu yasa ta saki fara'a tana cewa"marhabun lale ƙaraso ciki mutumina,ashe kana kan hanya banyi tsammanin zuwan.....'bata ƙarasa maganar ba,saboda ganin yarinyar dake ruke da hannunshi,
.mikewa tayi tare da zame farin glass É—in dake a fuskarta tace"baba buzu wannan yarinyar fa?yar waye kazo da ita,"
 bai bata amsa ba,sae da suka ƙarasa wurin kujerar da take tsaye,suka zauna kasa saman carpet,sannan ya soma magana"hajiya shannunku da dawowa,ya gajiyar tafiya,'
"Lafiyalou Alhmdulillah,"
Taƙarasa maganar har lokacin idanunta na akan abu,komawa tayi tare da zama saman kujerar sannan tace"bakayi mun bayani game da yarinyar nan ba,"Tayi maganar tana nuna Abu dake ƙankame jikin abbanta
 Fargabarsa kada ya sanar dasu cewa ƴarshi ce,suƙi kar6arta baisan inda zai kai yarinyar ba,ya kwaso yarinya ya kawo masu batare da ya sanar dasu ba,
dakyar ya iya buÉ—e baki muryarshi kamar zaiyi kuka yace"yarinyar wurina ce hajiya sunanta Abu,ina neman alfarmar ku taimaka mun ta zauna awurina,saboda bata da kowa acan niger,dama a hannun kishiyar babata take zaune,matar bata da imani naje na shame ta tana gallazama yarinyar nan,ban ta6a sanin abunda ke faruwa ba,sai da nayi masu zuwan bazatan nan.......'komai ya kawashe ya sanar ma hajiya ameena,
 Kamar jira takeyi ya kai ƙarshen maganar tashi,nan ta rufe shi da faɗa tana cewa"Amma baba buzu ka bani mamaki wlh,yanzu duk irin shaƙuwar dake tsakaninmu dakai,duk irin yarda muka ɗaukeka tamkar ɗanuwanmu,hakan baisa ka sanar damu cewa kana da ƴa ba,meyasa tun lokacin daka fara aiki agidan nan baka ɗauko yarinyar ka kawota gidan nan ba!....'ta inda take shiga bata nan take fita ba,
Jin waÉ—annan kalaman na Hajiya ameena yasa baba buzu fashewa da kuka yana cewa"na cuci kaina da ban sanar maku ba,ban ta6a tunanin cewa zaku kar6i yarinyar nan hannu bibbiyu ba hajia,da tuni na jima da kawo maku ita,kullum ina cikin takaicin rashinta a kusa dani,saboda itace kaÉ—ai nake gani inji dadi aduniyar nan......'sosai baba buzu ke zubda hawayenshi,
 Abu kuwa ganin mahaifinta na kuka yasa itama ta fashe da kukan,jikin hajiya ameena ne yayi sanyi,tausayinsu duk ya kamata,
tausasa muryarta tayi tace"baba buzu kukan ya isa hakanan,naji daÉ—in dawowarka musamman daka kawo mana wannan Æ´ar kyakkyawar yarinyar taka,kuma insha Allahu zamu bata kyakkyawar kulawa,zata zama tamkar Æ´ar cikina,dama kuma banda Æ´a' mace,gashi inason Æ´a mace,Ashe da rabon zan samu......'
 Share hawayen shi ya shiga yi yana yi mata godiya,
 "Yanzu abunda nakeso dakai,ka wuce ɗakinka kayi wanka zansa akawo maka abinci,nasan kun kwaso gajiya sosai kuna bukatar hutu,ita abu kabarta awurina,zan gyara maka ita sosai da anjima zata zo ta gaishe ka,"
 Cikin shesshekar kuka baba buzu yace"hajiya bansan da wani irin kalamai zan gode maku ba,kunyi mun abinda bazan iya saka maku ba,kun jima kuna ɗawainiya dani kuma yanzu gashi zaku ɗauki ɗawainiyar yarinyata,Allah yasa ka maku da mafifincin alkhairinsa.....'sosai baba buzu ya shiga yi masu addu'o'i hakan ba ƙaramin dadi yayi ma Hajiya ameena ba,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.