Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
ï¿?
 Murmushi azmee tayi tare da kai hannu taja kumatunta tace"bani zaki godemawa ba, ko kin manta waÉ—anda suka bada kuÉ—i akayi maki siyayyar ne"?Â
 girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"a'a ban manta ba,amma ina jin kunyar zuwa inyi masu godiya,"
  "Gaskiya yakamata kije kam,zasu ji daÉ—i sosai su son cewa kinji daÉ—in abunda sukayi maki,ki same su kiyi masu godiya,"Â
 "Insha Allah zanje," ta amsa mata, sakin kumatun nata tayi sannan ta juya zata futa, har ta ruÆ™e Æ™opar zata buÉ—e ta jinkirta kamar mai tunanin wani abu, sake juyowa tayi tare da kallon Sehrish dake a tsaye tace"wai nikam akwai abunda nake taso in tambayeki tuntuni sai in ta mantawa,"Â
 cike da kulawa sehrish take kallonta don jin me zata ce,
 Cigaba da cewa tayi "a kwanakin baya kinyimun magana akan cewa kinason zuwa garinku domin ki duba ƴan uwanki da basa lafiya ko"? ta tambaya tana kallonta,
  A ruÉ—e sehrish tace"Æ´an uwana kuma aunty azmee? Su wa kenan ? ni ba muyi wannan maganar ba kodai kin manta ne"?Â
 hararar wasa azmee tayi mata tare da cewa"banason wasa fa, kinsan me nake magana akai mana, nan kwanaki kikazomin kina kuka kina cewa in taimaka maki kije kiga Æ´an uwanki shine kuma yanzu zaki ce mun har kin manta?Â
 Hankali tashe sehrish tace"aunty azmee ni bani da wasu Æ´an uwa, bani da kowa wlh, bansan akan me kike magana ba,"Â
  mamaki ne ya kama azmee ganin yarda sehrish ta haƙiƙance akan cewa bata da wasu ƴan uwa kuma fuskarta babu alamun zolaya,bayan ita da kanta ta sanar da ita game dasu,
  ɗaure mata fuska tayi tare da cewa"banason rainin hankali sehrish!kina nufin dama baki da wasu Æ´an uwa!Æ™arya ce kawai kika shirga mun?tun farkon zuwanki gidan nan aiki, kika sanar dani cewa Æ´an uwanki ne basu da lafiya shiyasa kikazo neman kuÉ—in da za'ayi masu aiki, har na ranta maki kuÉ—i dubu É—ari tara domin ayi masu aiki a amatsayin kuÉ—in aikin ki na shekara É—aya da rabi, shima wannan duk plan ne kika tsara mun !!!!? Rai a6ace azmee ke magana hakan ba Æ™aramin É—aga mata hankali yayi ba, tuni idonta suka soma zubar da hawaye saboda tagaza gane kan me azmeen ke magana akai,.Â
ï¿?
  "Aunty azmee wlh ni duk bansan anyi wannan ba! Bamu ta6a magana dake akan cewa ina da wasu Æ´an uwa ba,kuma ni ban amshi wasu kuÉ—i ba saboda ayi ma wasu aiki ba.....'Â
 tunkan ta ƙarasa maganar azmee ta kwatsa mata tsawa tare da cewa"Ya isa haka Sehrish!!ashe dama ke maƙaryaciya ce!! kin cuce ni kinyi mun karyar cewa kina da ƴan uwa,ashe duk tsara ni kikayi saboda ki samu kuɗi,danasan haka kike da tunfarko ban yarda dake ba, wlh sehrish kinban mamaki kuma na gama yarda dake.......' tana kai ƙarshen maganarta, a fusace ta juya zata bar ɗakin cikin sauri sehrish ta ruƙo jallabiyar jikinta,muryarta na rawa cikin kuka tashiga cewa"wlh aunty azmee bansan komai game da abunda kike faɗa ba,na rantse maki da Allah wlh bani da wasu ƴan uwa aduniyar......'
Karanta>>> Taswirar Ƙaddara Complete Novel Document
 girgiza kai azmee tashi ga yi tana cewa"wlh kin ban mamaki sehrish,bansan haka kike ba ae da tun farko ban bari kin fara aiki agidan nan ba!!kin cuce ni kin rushe duk wata yarda da nayi maki,sai faman rantse rantse kikeyi mun ko tsoran Allah bakiji," rai a6ace azmee tayi maganar tare da fusge rigarta daga riƙon da sehrish tayi mata, cikin sauri tasa kai ta fuce daga ɗakin,
 A wani irin yanayi sehrish ta zube saman guiwowinta tana faman sharara kuka,mutun É—aya da ta yarda da ita aduniyar nan ayau ta juya mata baya akan abunda batasan dashi ba,har ga Allah ita gaskiyarta take faÉ—i amma azmee taÆ™i fahimtarta,tuni zazza6i ya fara hawa jikinta,sam tagaza tashi daga kneel down din da tayi ðŸ˜
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
  Â
Tun da azmee ta fuce daga É—akin sehrish, kai tsaye ta wuce nata bedroom É—in, shiga ciki tayi tana faman safa da marwa,ranta ba Æ™aramin sosuwa yayi ba,gaba É—aya taji sehrish tafara fitar mata arai,saboda Æ™aryar da ta shirga mata,cikin Æ™unar rai take cewa"kin cuce ni sehrish,banta6a tunanin zakiyi mun haka ba,natsani makaryaci arayuwata, me yasa tunfarko bata fito fili ta faÉ—amun cewa kuÉ—i takeso ba,don me za tayi mun Æ™arya?Â
 tuni idon azmee sun cicciko da kwalla saboda ƙululun baƙin cikin daya tsaya mata arai,daƙyar ta iya samun wuri ta zauna daga gefen gadonta tana cigaba da tunani acikin ranta,
 "ɗan adam kenan!yanzu duk yardkyautatama yarinyar can sai da ta butulce mun,saboda farin cikinta nakeyin wasu abubuwan don na faranta mata,amma hakan bai hana tayi mun ƙarya ba!!idan har dagaske ne sehrish ba ta da wasu ƴan uwa ƙarya ne tayimun,TO WAYE TASA NA TURA MA KUƊIN!!!!!!? miƙewa azmee tayi lokaci guda gabanta yashiga faɗuwa tuni taji zufa tasoma tsattsafo mata,hankali tashe tace"nashiga uku!! tabbas na tafka kuskuren yarda da yarinyar can!! meyasa tunfarko najata ajikina?kada fa ace da wata manufa tazo cikin gidan nan!!!
 abubuwa iri iri suka dinga zuwa mata acikin ranta game da SEHRISH,😥
Lamarin dae ba daÉ—in ji
💋BOSS BATURE💋
A 6angaren su hossana kuwa tun bayan da suka yi faɗan nan atsakaninsu,su kayi fushi da junansu,saman gado hossana ta haye tana baccin wahala bayan ta gama shan kukan nata,Jahad kuwa bayan sun gama faɗan toilet tashiga tayi wankanta,bayan ta fito ta shirya cikin riga fara off shoulder tare da dogon wando baƙi,ba ƙaramin kyau tayi ba,musamman gyaran gashin kanta wanda akayi masu a wurin saloon ya ƙara ƙawata ta sosai,
 komawa tayi ta zauna daga gefen gadon kusa da hossana, bin ta da kallo tayi sai faman sharar bacci takeyi tana jan minshari,haryanzu kayan baccin nan ne ajikinta tun na daren jiya,
ï¿?
  Hannu tasa tare da bubbuga bayanta a hankali tana cewa"hossana ki tashi!ko baki jin yunwa ne?Â
  tsoki taja tare da juya mata Æ™eya don karta takura mata, sake bugun bayanta jahad tayi tace"wai ba zaki tashi bane!?Â
  buge hannunta hossana tayi tare da cewa"ki rabu dani, babu ruwanki dani,idan banyi wankan ba jikinki ne ko nawa?ko kin ta6a ganin zararre mara hankali yayi wanka ne? ni mahaukaciya ce kibarni inyi rayuwata.......'cikin kuka hossana ta ƙarasa maganar,da alama abun ya ta6a mata zuciya dama ta tsani akirata da zararriya,
 Cike da lallashi jahad tace"am really sorry hossana nasan ban kyauta ba,raina ne ya 6aci shiyasa har na gaya maki hakan,bazan Æ™ara ba insha Allah,"Â
  tayi maganar tare da ruko hannun hossana donta tashi,fisge hannunta tayi daga cikin nata tace"pls jahad leave me alone,zuciyata ba ta mun daɗi,yaya Omar kawai nake jira yazo,"
  Murmushi jahad tayi tare da janyo gashin kan hossana tana wasa dashi a hannunta tace"faÉ—a mun gsky hossana kodae son yaya omar kike ne"?Â
  juyowa hossana tayi tare da kallonta fuskarnan É—auke da murmushi tace"eh ina son yaya omar sosai ke fa"?Â
  jiki asanyaye jahad tace"Wani kalar so kike nufi? Na soyayya da aure? ta tambaya tana kallonta,
 hossana tace"shi nake nufi,jahad inason ya omar sosai,"
 shiru jahad tayi gabanta na faÉ—uwa tuni yanayin fuskarta ya canza izuwa matsananciyar damuwa,ganin hakan yasa hossana tashi zaune tana kallonta tace"jahad naga kamar fuskarki ta canza meya faru ne"?Â
 cikin sauri ta basar tare da ƙaƙaro murmushi tace"bakomai hossana,ni zan wuce kitchen na shirya mana lunch," tana faɗin hakan ta miƙe da hanzari tabar bedroom ɗin nasu,saukowa daga saman gadon hossana tayi tare da wuce wa cikin toilet don tayi bath,
  sam jahad tagaza jurewa tana fitowa daga bedroom ɗin ta wuce cikin falon tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna jiki amace,
 "dagaske ne hossana ya Omar take so?amma hossana ba ta da cikakken hankali bana tunanin tasan menene *SO* ya Allah kasa hakane saboda bazan iya jurewa ba......' ta furta tare da kai hannunta saman goshinta,bakomai bane ya faɗo mata aranta ba face farkon haɗuwarsu dashi a asibiti,lokacin ba ƙaramin tafiya yayi da zuciyarta ba saboda yarda yake acting dinsa,kyawawan ɗabi'unsa da halayansa sune suka sa jahad faɗawa tarkon shi, ita kanta bata tashi tabbatar da hakan ba sai ranar daya sanya handkerchief dinsa yana goge mata hawayenta..........."
  tayi nisa cikin tunanin nata muryar hossana ta katse ta da cewa"jahad nayi tunanin zanzo na sameki a kitchen ne ashe kina nan zaune," firgit jahad tayi tana kallonta sai da ta dai²ta natsuwarta sannan tace"har kinyi wankan kenan," ta faÉ—i tana kallon hossana dake nufota jikinta na sanye da gown black colour, ta saki curly hairs É—inta ya barbazo mata abayanta,Â
  Amsa mata tayi da cewa"Eh baki ga har na canza kaya ba," ta faɗi tare da jujjuya mata donta gani,
 Murmushi jahad tayi tare da cewa"kinyi kyau sosai," ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye tace"kizo muje kitchen ɗin atare saiki tayani aiki, muyi sauri mu kammala,"
 Amsa mata tayi da toh, sannan suka wuce atare kitchen ɗin atare,
 ***************
Zaune yake acikin motarsu Ƙirar mercedes S450,ash colour,jikin shi na sanye da kakin sojoji,sai faman duba wrist watch É—in dake hannun shi yake lokaci zuwa lokaci,gajiyar da yayi da jira ne yasa shi É—auko wayarshi daga cikin trouser pocket dinsa ya buga ma Jahan kira nan take kiran ya shiga bada jimawa ba Ya É—aga kiran, tsoki ayaan yaja tare da cewa"Wai kuÉ—in sunÆ™i fidduwa ne? Nifa nagaji da jira wlh," fuskarshi a yamutse yayi maganar,. Â
 on the other hand jahan yace"Am sorry yanzu haka ma na fitowa daga bankin gani nan zuwa,"
ï¿?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.