Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
 daker sehrish ta tsagaita da dariyar tace"Abba zan tafi kitchen nabarsu suna aiki,"Â
 Murmushi yayi tare da cewa"hakan nada kyau,kwara tun ynx ki koyi girkin shima yana daya daga cikin jarabawar da zan maki don bazan aura ma ƴa'ƴana macen da bata iya girki ba,then idan nasamu free time zan wa junaid magana ya kira mun ke don mu ƙara tattaunawa,"
 Amsa mashi tayi fuskarta cike da annashuwa tabi ta gefenshi tana faman sakin murmushi ba don komai ba sai don maganar Abban nasu dayace idan marking ta F9 ne zai aura mata haroon hakan na nufin shi kanshi yasan cewa haroon cikon bencin gidan ne 🤣😂😅
 Har juyawa abban nasu yayi yana kallonta a lokacin tayi nisa wurin sauka daga stairs ɗin,ajiyar zuciya ya saki saboda ganin farin ciki a fuskar yarinyar, dama yayi hakan ne don ya mantar da ita damuwar da ta shiga har ta la6e tana kuka,kama hanya yayi ya wuce,dama bedroom ɗin junaid ya nufa,
***************************
Tun ɗazu da suka kammala lunch ɗinsu after Azhar hossana da Camila suka koma bedroom din saman katafaren gadon suka baje suna bacci abun ba'a magana,ita kuwa jahad sam tagaza yin bacci tun da tayi sallar la'asar tafito daga ɗakin ta tsaya a falon tana zagaye, bakomai take burin gani ba face Ya Omar dinsu ko zafin ciwon ƙafarta yanzu tadaina ji,har wurin ƙarfe biyar da wani abu tana wannan safa da marwar in betwn seater's ɗin dake a palourn,tana cikin wannan zagayen MARSHAL OMAR ya shigo falon da sallamar shi, sam bata ji shi ba saboda ta juya masa baya tamiƙi hanya tana tafiya,
 Murmushi ya saki ya tsaya yana tunanin wacece acikinsu jahad ko hossana,koma dae wacece ba ƙaramin kyau tayi masa ba acikin kayan,yaji daɗin hakan saboda dama burinshi ya gansu cikin jin daɗi da walwala,ganin bata da alamar juyowa yasa shi yin gyaran murya da ɗan ƙarfi, cikin sauri jahad ta juyo tana faman zare ido don batayi tsammanin ganin mutun ba,nan da nan wani irin farin ciki ya mamaye fuskarta da karfi ta furta"Ya Omar," lumshe idonshi yayi tare da buɗe su yana murmushi,
 Watsa wa tayi da gudu tamkar zata rungume shi,sai da taje dab dashi sannan taci burki tana dariya,yana ganin hakan ya gane cewa Jahad ce,don da ace hossana ce sai tayi hugging dinshi,
 "Fatan na same ku lafiya"? Ya furta yana kallonta,fuskarta awashe tace"Alhmdllh ya omar,dama tun ɗazu nake jiran zuwan ka, ashe zaka zo da har na fidda rai,
  Omar yace"naso nazo ɗazu to bansamu hali ba,shiyasa na aiko maku da major don ya ɗauko ku,ina fata gidan yayi maku?
 "ya omar ni nama rasa da wasu kalmomi zanyi amfani dasu wurin yi maka godiya Allah.........."tuni idanunta sun cicciko da kwalla sun soma gangarowa daga cikin idanunta,
 Cikin sauri yace"Why jahad?me yasa zakiyi mun kuka bayan kinsan bana son ganin hawayen ku,sannan bana son godiya kada na sake ji,duk wani abu da nayi maku nayi shi ne don Allah,kuma haƙƙin ku ne dake akaina har yanzu ma ni ji nake kamar akwai sauran abubuwan da banyi maku ba,
..kallon shi kawai take yi yana bayani har yanzu tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Marshal omar,
Cikin shessheƙar kuka tace"ya omar kai wane irin mutun ne?narasa dame zan fasalta ka,kyawawan ɗabi'unka da halayenka da kyakkyawar zuciya irin taka bana tunanin a doran duniyar nan za'a samu mai irinsu,koda za'a samu sai anci baƙar wahala kuma cikin kashi 100 bai wuci asamu kashi biyu ba,kai na musamman Ne ya omar,ina taya iyayenka farin ciki sosai da samun ɗa kamarka,saboda kai abun alfahari ne........ni bansan da me zamu saka maka ba ya omar,ka bamu kyakkyawar rayuwa ka cire mu daga ƙangin rayuwar da muke ci,a lokacin da muke tunanin cewa kowa ya tsanemu bai son mu mutuwa ma kawai muke jira,sai gashi Allah ya haɗamu dakai,tun a lokacin nasan cewa kai kyauta ne daga Allah...........
 tun da jahad ta soma kora jawabi ya goya hanneyen shi a faffaɗan kirjinshi ya natsuwa yana sauraronta fuskarshi ɗauke da murmushi,saboda kalamanta ba ƙaramin shigarshi su kayi ba yadda take magana a natse ga wata irin murya dake gareta mai sanyin gaske irin muryar da duk 6acin ran da kake ciki in. Ka ji ta sai ka manta dashi,ae jahad akwai natsuwa ga tawakkali nima na shaida hakan 😘
"Ya omar ka faÉ—amun dame zamu saka maka?nasan ma babu Ba mu da abunda zamu iya saka maka aduniyar nan face addu'a itace kawai ke gare mu,i will keep pryaing 4 u ya omar hada family É—inka duka zan saku a addu'ata till the end of my life bazan manta ba aduk lokacin da nayi sallah ko nayi karatun alkur'ani har night prayers ma zan dinga tashi inayi just because u ya omar and ur family,
 ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya har lokacin hawayen fuskarta basu tsaya da kwarara ba,
 Hannu omar yasa tare da zaro handkerchief ɗinsa dake front pocket dinsa dake a t shirt din jikinshi,
 Da hannun shi yasa yana wiping tears dinta a hankali,runtse idonta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa a tattare da ita,
 Muryarshi ce ta tsinkaye ta da cewa"jahad ngde ssae kalamanki kawai da kikayi mun a yanzu ma sun wadatar dani,sannan idan kuna so ku saka mun abunda nakeso shine koda nan gaba kada ku juyamun baya bana son ku canzamin inaso ku tsaya a yarda nasan ku,ina tsananin ƙaunarku sosai bana son abunda zai raba ni daku,inason zumunci ya ɗaure a tsakanina daku daganan har can......
katse shi tayi da cewa"har ina kenan ya omar,"
 Cikin zolaya yace"gidan Aljanna mana," dariya tayi sosai kafin ta tsagaita da dariyar tace"insha Allah ya omar ba zamu ta6a baka kunya ba,zamu kasance kamar yarda kakeso,"
 Jinjina kansa yayi sannan yace"where's my hossana banganta ba,ko tana ciki ne? Ya yi nuni da hannun shi,
 Jahad tace"hossana suna ciki tare da wannan nurse camila din sai sharar bacci suke yi tun ɗazu,"
 Murmushi yayi tare da cewa"naso na ganta,"
 Cikin sauri tace"ya omar ka shigo daga ciki mana ka zauna na kira maka ita don itama hossana a ƙagare take data ganka,"
 Omar yace"sauri nake na koma gida yanxu,ki gaishe mun da ita dae,ko kuma zan kira wayane ae akwai telephone sai mu gaisa," jinjina kai tayi tare da cewa"shikenan zan sanar mata,amma nasan zatayi kuka in taji cewa kazo kuma ka tafi bata ganka ba,
  juyawa yayi yana faman sakin murmushi har ya kusa fita daga falon tace "ya omar," juyowa ya kuma yi yana kallonta,Â
 "Tun jiya inata so in kazo inyi maka ya mai jiki,abun yana araina ɗan uwanka daka sanar mun cewa bai lpy,"
  Omar yace"oh fawan da sauƙi jikin shi sosai,kada ki damu zan bashi waya inyaji sauki ssae sai kiyi mashi ya jiki,"
 Jinjina kanta tayi alamar toh daga nan sukayi sallama ya fuce daga falon,
 Ajiyar zuciya ta saki tare da wuce wa ciki fuskarta asake 😇
****AUNTY BABBA******
💋Boss Bature💋_
********AUNTY BABBA************
Zaune take agaban dressing mirror ranta a matuƙar 6ace fuskar nan tayi jawur saboda kukan da taci,ta zabga uban tagumi zuciyarta sai faman tafarfasa take yi,bakomai bane ya haddasa mata wannan 6acin ran ba face General ishaq daya hanata zuwa abuja,duk yarda ta kwallafa rai akan zuwa abujan ya hanata,sai da ya bari tasha wankanta ta kimtsa cikin leshi ta yafa mayafi ta ruƙo jakarta, tana fitowa ta same shi zaune a falo jikin shi sanye da gajeran wando baki,wani irin kallo yabi ta dashi tare da cewa"Ina zuwa,"
washe masa baki tayi tare da cewa"Abuja mana,kai fa kace zamuje duba jikin fawan,"
kai tsaye yace"ae nafasa wannan,ni kaÉ—ai zanje inyaso ko a waya ne kun kira Abba kuyi masu Allah kyauta,"
Tur6une fuska tayi tare da cewa"dan Allah idan wasa kake mun ka daina,"
ï¿?
 Shima ya tamke fuskarshi yace"ba wasa nake ba,ni kaɗai zanje inyaso saina wakilce ku,"
 Hankali tashe tace"Haba Abban hafsat sai da na kammala shirina, tafiya kawai ta rage zaka ce wai an fasa gaskiya ni sai naje," ta faɗi tare da ruƙe qugunta tamkar zata buge shi,
 MiÆ™ewa ishaq yayi fuskarshi ba wasa yace"to ki sani muddin kikasa Æ™afarki kika bar gidan nan without my permission hmmmmmm ke kinsan mai zai biyo baya,Â
 Yana faɗin hakan ya fuce ma daga falon yabarta,
 da gudu ta koma bedroom ɗinta a ƙasa ma tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado ta faɗa tadinga shan kukan baƙin ciki har bacci ya kwashe ta,
Ta jima tana baccin kafin ta tashi cike da kunci ta koma gaban mirror ta zabga tagumi rai a6ace,
Download>>>Â Dangin Rabi Complete Document
Ta jima tana tunanin meyasa general ishaq ya hanata zuwa gidansu don ta duba jikin fawan,abun ya É—aure mata kai saboda shi da kansa yace zasu je dubiya atare amma ya canza ra'ayinsa yanzu,
  tsoki ta buga tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake agaban mirror ɗin,contact ɗinta ta shiga ta lalubo numbar wayar HAYAAM ta danna mata kira,ringing ta shiga yi kusan sau uku ba'a ɗaga ba,
tana a cikin toilet kiran ya shigo a lokacin wayar na hannun wani matashin saurayi dake zaune saman wani haÉ—aÉ—É—en gado, daga shi sai shorts ajikin shi ya baje abun shi, ganin sunan Aunty Layla ya bayyana akan screen É—in wayar yasa shi É—aga murya tare da cewa"babe!babe!ur phone is ringing,
 Daga cikin toilet ɗin tace"wanene ke kirana?in dae mommy ce ko Abi ka kashe wayar gaba ɗaya bana son takura,
 "No basu bane,wannan auntyn naki ne Layla,"
Jin sunan Aunty laila yasa ta yin wuff ta fito daga cikin toilet ɗin, doguwa ce sosai fara sol babu ko tabo ajikinta kai kana ganin fatar nan zakasan cewa ba ƙaramin kuɗi take kashe mata ba saboda yarda take ɗaukar ido,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.