Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
 Saukowa down tayi cikin sauri adai dai lokacin ta ji saukar motoci cikin gidan alamar sunyi baƙi, kitchen ta wuce anan tasamu junaid zaune saman dinner table harya kammala cin breakfast ɗin shi, yana ganinta yace "dama yanzu nake shirin biyo ki, bansan meya tsayar dake ba gashi har time ya ƙure ma,da ace ana bugu a school ɗin wlh da kinsha bulala yau," dariya sehrish tayi jin abunda yace
 "Bari na ɗauko school bag dita," ta faɗi tare da juyawa cikin sauri ta koma bedroom ɗinta,
 Sallama junaid yayi wa aunty azmee sannan yabaro kitchen din, jin sallamar Cg Abbas yasa shi É—agowa cikin tsananin farin ciki yace "Yaya Abbas kaine tare da Aunty Amani !!!"Â
murmushi suka saki gaba ɗayansu da yake tare suka zo shi da AMANI yana sanye cikin shigar shadda maroon color ita kuma tana sanye da Arab gown white colour mai kwalliya ajikinta na duwatsu tayi rolling veil a kanta, ba ƙaramin kyau tayi ba,
 sam junaid ya gaza rufe bakinsa don murna, buɗe mashi hannu abbas yayi cikin sauri junaid ya ƙarasa tare da faɗawa ya rungume shi sosai ajikinsa yana cewa "i really missed u our last born, duk da ina fushi dakai saboda baka son zuwa kawo min ziyara,' yayi maganar a lokacin da ya raba jikin shi dana junaid,
 ɗan turo mouth dinsa yayi cikin shagawa6a yace "Yaya Abbas saboda me zaka ce kana fushi dani dan Allah, bakasan yarda na damu dakai ba koda yaushe inason zuwa amma shaiɗan ya hanani zuwa,' dariya sukayi gaba ɗayansu jin abunda junaid yace,
 ɗan gyaran murya amani tayi masa tare da cewa"Junaid ni baka ganni bane"?
 matsawa yayi tare da kai hannu zai rungumeta ajikin shi, ae kuwa a razane Abbas ya finciko rigarshi tare da janyo shi baya baya yana cewa "Sannu mati na mata,!matar tawa zaka rungume agabana? salon mu koma gida ta juya mun baya ko?"
 Fashewa da dariya Amani tayi shima junaid ɗin dariyar yake yi cikin jin kunya ya sunnar dakai, shi aganin shi ba wani abu bane don ya rungume matar yayan shi, duk cikin waye wa ne,
 Abbas ya kuma cewa "Oh ni junaid? Yanzu fa in na Æ™yale ka sai ka rungume ta ko"?Â
 ɗaga mashi kai yayi alamar Eh, hannu abbas yasa tare da É—an jan kunnan shi har yayi Æ´ar Æ™ara yana faÉ—in "wayyo yaya Abbas karka cire mun kunne na in rasa na jin magana,"Â
 "Hanzarta ka cire masa kunnan, hukuma ce zata raba ni dakai," acewar Abbansu wanda bai jima da fitowa ba ganin su yasa shi tunkaro su,
  Murmushi suka saki gaba ɗayansu, adai dai lokacin Sehrish tafito daga ɗakinta, harta sanya Sandals ɗinta taruƙo school bag ɗinta, ƙarasawa tayi inda suke,
 tunkan taƙaraso Amani ke kallonta cikin jin bugun zuciya, shi kanshi Abbas kallon matashiyar yarinyar yake yi cike da mamakin ina aka samu yarinya mace acikin gidan,
Ganin duk hankalinsu yadawo kanta yasa jikinta ya soma yin kerma, dakatawa tayi da tafiya sannan cikin en ina tace "umm....ina kwananan ku,"
 atare abbas da abbansu suka amsa mata banda Amani dake tsaye Æ™iÆ™am tana kallonta cikin tashin hankali, ita kanta sehrish atsorace take da kallon da Amani ke yi mata,Â
 "Zonan My daughter nayi missing ɗin ganinki, gashi bakya zuwa kina gaishe da Abbanki ko"? Yayi maganar yana kallonta,
 Ƙarasawa sehrish tayi gab da Abban nasu ta tsaya tana faman ƙaƙume hannun jakarta da ta sargafo a kafaɗarta,
Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta yace"yaushe kika fara zuwa school ne ba'a sanar mun ba"?
....daker sehrish ta iya cewa "jiya ne nafara zuwa,"
Jinjina kansa yayi tare da cewa "okey,ki maida hankali sosai akaratun ki kinji ko? Banda biye ma Æ™awayeÂ
 "Insha Allah Abba," ta amsa mashi,
Baki asake Abbas yace "yakamata a wayar mun dakaina mana, ina aka samu yarinya kyakkyawa kodai daga cikin danginmu ne na damaturu ko zariyya"?
 Ya tambaya aÉ—an ruÉ—e yana kallon Abban nasu, tunkafin Abban nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa "Æ™anwata ce yaya Abbas, sunanta Sehrish kuma abbane yayi mun Æ™anwa da ita, itama Æ´ar Abban mu ce, ba'a jima da haihuwarta ba, nasan zakayi mamakin yarda tayi saurin girma har haka, ka tambayi Abba zaiyi maka bayanin komai,'Â
 yana faɗin haka yaja hannun sehrish suka bi ta gefensu suka fuce,
 Dariya kawai Abbansu ke saki hada shi Abbas ɗin,
 "Ji wata shiririta irinta junaid,hakanan kawai ya zabga mun Æ™arya, ina na ajiye matar bare harna haifi Æ´a kamar wannan,'Â
Ya fadi tare da yi masu alamar su shiga daga ciki, bin shi su kayi tare da samun wurin saman royal sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna, Amani na kusa da Abbas yayin da Abban ke fuskantar su yace "sannun ku da zuwa,nayi mamakin ganinku da wuri haka,"
Abbas yace "tun jiya muka so muzo,amma dare yayi sosai lokacin, wlh sam nagaza samun natsuwa ne game da halin da naga fawan a asibiti, shine nace mata tashirya muzo har gida mu duba shi,"Â
 yayi maganar fuskarshi dauke da damuwa, Amani ma tace "Abba ya mai jiki? sai jiya da daddare yake faɗamun abunda ya faru dasu fawan hankali na ya tashi sosai, tun jiya nima naso ko wayane nakira na tambayi jikin shi amma duk layin dana kira ba'a ɗagawa,"
Abba yace "ae ba zaki same su ba, saboda duk muna cikin damuwa ne,bakowa ma yasan inda ya jefa wayarshi ba,abun ne ya tayar mana da hankali sosai,
Cikin sanyin murya tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya,ya tashi kafaÉ—un shi, su kuma waÉ—anda sukayi mashi wannan aika aikan Allah ya toni asirin su,"
 "Ameen Ameen," suka amsa mataÂ
Daga bisani Abbas yace "bari mu shiga ciki mu dubo shi,"
 Miƙewa su kayi hada Abban yayi masu jagowa izuwa ɗakin da aka kwantar da fawan,
 Da sallama suka shiga ciki, har lokacin fawan na kwance sai faman sharar bacci yake yi, Abbas yace "masha Allah jikin nasa yafara sauƙi, tun da harya samu bacci,"
 "Ae tunjiya dana shigo ɗakin na same shi yana ta faman fisge-fisge yana cewa sun biyo shi zasu kashe shi,saina zauna wurin shi anan zaune muka kwana ni dashi da asuba ne nabar ɗakin," Abban nasu ne yayi maganar ayayin da yake samun wuri gefen gadon tare da zama yana kallon fawan ɗin dake kwance magashiyyan yana kwasar bacci,
 matsawa Abbas yayi shima tare da samun wurin kusa da Abban nasu ya zauna sannan yakai hannun shi ya dafa forehead din fawan yana cewa "Baƙaramin jiki yaji ba gaskiya,sun azabtar dashi sosai bawan Allah, amma asannu zai warware insha Allah,
 Kafin Abban nasu ya kuma cewa wani abu wayar Amani dake acikin handbag ɗinta tashiga yin ringing da ƙarfin gaske,
 Kallonta Abbas yayi tare da cewa "ki fita waje ki amsa wayar," cikin sauri ta amsa mashi da toh sannan ta fuce,
 dama so take ta fita daga ɗakin saboda gulmar data ciyota kunsan mu mata abun ajinin mu yake,da zarar abun gulma ya samu nan take zaka ga jikin mutun har rawa yake yi don ya faɗama ɗan uwansa, (Amma fa ni bana gulma) 😒
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.