Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Haka su sehrish suka ci gaba da shan wahalar rayuwa a hannun mutumin nan,wani tashin hankalinma sayyadi ya fara kwaɗaita dasu,ya dinga nemansu a 6oye abu bata sani ba,duk in tayi kuskuren fita ta barsu acikin gidan yazo ya same su haka zai ƙumshe su aɗakin yana tsoratar dasu akan susha mashi gabanshi,duk abu bata ankare ba,sae wata rana da ta ta6a dawowa ta same su suna ta kwarara amai wani irin abu mai yauƙi yauƙi yana fitowa abakinsu,tsare su tayi da tambaya akan me suka sha ne ya 6ata masu ciki,ƙin faɗa mata sukayi saboda tsoran kada Abbansu ya kasheta kamar yadda yayi masu barazana in suka faɗa mata,ganin sunƙi faɗa mata yasa ta ɗauko wuƙa a kitchen ta nuna su da ita tana cewa"Ko ku faɗa mun ko in kashe ku a wurin nan,"gaba daya suka tsorata,sehrish ce ta buɗe baki ta sanar da ita abunda mahaifinsu ke sanyasu suna yi mashi,saboda tashin hankali nan take ta yanke jiki ta faɗi asume,
Kukan da suka fashe dashi ne yasa makwabciyarsu shigowa gidan don taga meke faruwa ne,anan ta samu abu a sume ruwa ta ɗebo ta yayyafa mata ta farka,miƙewa tayi zaune tare da sanya hannu ta dafe saitin zuciyarta tana ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!ya Allah ka ɗauki raina tun kafin baƙin cikin mutumin nan ya kashe ni,Sayyadi ka cuci rayuwata ka gama dani nashiga uku! Wayyo Allah na!
 Tasha kuka kamar ta zauce,daƙyar maman sadeeq ta lallashe ta bayan ta tsagaita da yin kukan take tambayarta meya faru,bata 6oye mata komai ba ta kwashe ta sanar mata,a lokacin maman sadeeq har hawaye sai da ta zubar masu saboda tsabar tausayin yaran,ranar yini sukayi suna jimamin abunda ya faru atare kuma suka duba yaran don su tabbatar in bai lalata su ba,duk da sun tambayesu ko ya masu wani abu a wurin sunce a'a,bayan tafiyar maman sadeeq ta koma gida mijinta ta samu tayi mashi magana akan Yayi ma sayyadi magana akan abunda yake aikatawa saboda abun yayi yawa,yana cutar da rayuwar yaran, nan gaba zai iya lalata masu rayuwarsu gaba ɗaya har ma yayi silar Rasa ransu,
 Jinjina kai Malam yayi tare da cewa"Hmmmm taya zan tunkari mutumin nan?me zan iya yi mashi?Mutumin da kana ja mashi aya yana fassarata!taya zai fahimci cewa badai dai yake aikatawa ba?bayan yasani kuma yake take sanin!Tabbas na tausaya ma rayuwarsu amma babu ta yadda zan iya taimakon rayuwarsu sae dae na bisu da addu'a kawai,Allah shine zaiyi maganinshi"shi kanshi Abban sadeeq sae da ya zubar masu da kwalla,ya tausaya ma rayuwar yaran,tabbas suna cikin masifa,
Bari in taƙaice maku labarin,sayyadi shine yayi sanadiyar ta6in hankalin hosana,a tsakar dare suna bacci ya ɗauketa batare da sanin kowa ba,ya kaita gidan wani Babban ɗan siyasa kamar yadda suka tsara dashi akan cewa zai kai mashi ita yayi amfani da ita don cin nasarar za6en shi,sam batasan ya ɗaukota ba sae dae kawai ta ganta asaman gadon mutumin,fasa ihu tayi da sauri ta diro daga saman gadon tana ƙanƙame jikinta,mutumin nan babu kunya babu tsoran Allah ya shiga tu6e kayan jikinshi agabanta,a tsorace tace mashi fitsari take ji,ya nuna mata hanyar toilet taje tayi fitsarin yana jiranta,
Jiki na rawa ta shige cikin toilet ɗin ta rufo ƙopar,Kunna fanfo tayi don kar yaji ƙarar abunda zatayi,zagaye tashiga yi acikin toilet din tana neman abunda zata fasa window ɗin kewayen,annan ƙasa ta samu wasu ƙarafuna masu ɗan tsayi kamar an ta6ayin gyaran wani abu a toilet ɗin aka ajesu nan,
 Hannu tasa ta ɗauka jiki na rawa ta haye saman toilet seat ɗin dake a rufe,ta faffasa windown da sauri da sauri duk mutumin nan baijiyota ba,sai da ta fasa glass din ya tarwatse sannan ta biyo ta windown duk batayi tunanin cewa bayan yana da tsayi ba,kawai ta afka,gaba ɗaya ta bugi floor ɗin da ƙarfi kanta ya fashe,hancinta da bakinta duk suka bugu ga sauran kananun glass da suka yayyanketa ta,gigitacciyar ƙara ta saki saboda azabar da tasha,amma hakan bai hanata yunƙurawa ta miƙe da gudun gaske ta nufi hanyar fita daga gidan,mai gadin gidan na sallar dare ta samu ta fice da gudu ta karamar kopa tana kuka ta miƙi hanya gashi dare ne,
Acan kuwa tsakar dare Oummansu na bacci ta jiyo muryar jahad tana cewa"oumma ki tashi,hosana bata a gida fa,banganta ba,har kewaye na duba amma babu ita bansan ina taje ba,hankali atashe abu ta farka,a lokacin itama sehrish ta tashi,gaba daya suka shiga nemanta,duk sayyadi na ɗakinshi yana jiyo hayaniyarsu bai tanka masu ba,da suka duba ko ina basu ganta ba,anan fa hankalinsu ya ƙara tashi,fitowa sukayi suna bi gidaje suna tambayarta wasu a amsa masu da bata nan,wasu gidajenma ba mai zuwa balle ya basu amsa,kai tsaye suka miƙi hanya suna duddubawa ko wani mummunan abu ya faru da ita ne,lokacin da suka hau gefen titi suna tafiya........
  Adai dai time ɗin Hosana ta shigo kan hanyar da gudu tana kuka hannunta dafe da kanta dake ta zubar da jini,tana ambaton oumma, oumma,
  a gigice suka kai idanunsu wurinta,da gudun gaske suka tunkareta,abu na ƙoƙarin dakatar da ita akan ta kauce daga saman titin amma sam bata a cikin hayyacinta,wata mota ce ta bugeta da ƙarfin gaske gaba ɗaya ta kife ƙasa,mai motar na bugeta yaja motar da gudu yabar wurin alamar cewa da gangan ya bugeta,ashe ɗan siyasan nan ne yabiyo ta,bayan ya jima yana jiranta ta fito daga toilet bata fito ba,kawai ya afka ciki anan ya samu ta fasa glass ta gudu,yana huci ya fito ya mayar da kayanshi,ya bi bayanta cikin motarshi,don karta tona mashi asiri yasa yayi mata haka don ta mutu,
 Zubewa sukayi agabanta suna ta kuka suna ta faman jijjigata a ƙarshe Abu ta sanya hannu ta ɗauketa,a ƙafa suka taka da sauri da sauri saboda babu abun hawa,gashi sae bleeding takeyi,suna cikin tafiyar nan sai ga Mijin maman sadeeq cikin napep,ashe tun lokacin da suka je gidan neman Hosana,bayan tafiyarsu ya gaza samun natsuwa shine ya biyo bayansu,napep ɗin ma bata shi bace arota yayi,saboda mashin ɗinshi babu mai,
 Adai dai inda suke ya tsayar da abun hawan nashi,tunda yaga halin da hosana ke ciki bai tsaya tambayar ba'asi ba yace su shiga ciki,
 A daren ranar suka kaita asibiti,likitoci suka shiga duba ta,tun nan aka sanar dasu cewa Sai anyi mata aiki,ana buƙatar kuɗi miliyan ɗaya da rabi,nan fa hankalinsu ya tashi,saboda ko sisi basu da ita,
Har washe garin ranar ana kan abu ɗaya,andai samu an fara treating ɗin raunukan jikin nata,aikin dai ne ya gagara,sun jima a asibitin nan ana neman taimakon kuɗin da za'ayi mata aiki amma ba'a samu ba,sayyadi ko leƙo asibitin baiyi ba,bayan shine silar komai don ubanshi,
Sanadin haukacewar mahaifiyarsu kuwa,lokacin anata neman yarda za'a harhaÉ—a kuÉ—in aikin hosanan,duk wani abu mai dan amfani tasa an sayar dama ba wasu abun kirki suka rage mata ba,don duk ta siyar da kayayyakinta wurin kula dasu Sehrish,a lokacin abu duk ta gama fita hayyacinta ta kode ta rame,duk da dae kyawunta na nan,amman inka ganta zaka yi tunanin ta girmi shekarunta saboda wahalar rayuwa,
ta yanke shawarar zuwa gidan ta duba taga idan sayyadi yana nan jin shiru bai neme su ba,ko labarin kwanciyar hosana asibiti baije mashi bane,
 Tana sa ƙafarta tsakar gidan nanfa ta dinga jin wannan gurnanin abunda sukeyi mara daɗin ji,ranta yayi mugun 6aci,kitchen ta nufa ta ɗauko tukunya ta zubo ruwa a fanfo kusan rabin tukunyar mai fadi,bayan ta ɗaura ruwan sai da ta jira ruwan ya tafasa sosai yana huci sannan ta sauke shi,tsumma ta ɗauko ta ruƙo tukunyar dashi,ta nufi ɗakin nashi,cikin sa'a sun bar ƙopar a buɗe dama da yawan lokutta basa rufe ƙopa turo ta kawai sukeyi,
 Faɗawa cikin ɗakin abu tayi,mutun shida ta samu kamar wasu mayu manne da juna,aikuwa tana ƙarasawa wurin gadon,ta ɗaga tukunyar gaba ɗaya ta maka masu ruwan zafin ajikinsu,wa'iyazubillah,agigice suka rabe da junasu,wata irin gigitacciyar ƙara suka shiga saki ta azabar radaɗin tafasasshen ruwan zafin nan da abu ta watsa musu,ihu suka dinga yi suna birgima,fatar jikinsu duk ta ɗame ta lalace,
 Duk atunaninta hada sayyadi acikinsu ashe yana acikin toilet,razananniyar ƙarar daya jiyo daga cikin bedroom ɗinshi ne yasa shi fitowa daga cikin toilet din,Waro ido waje Sayyadi yayi tare da aza hannunshi akai yana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Abu baki da hankali ne!!kinsan ko me kika aikata?
 Idanunta jawur ta kalleshi rai amatuƙar 6ace tace"Na sani,kuma ina cikin hayyacina,wlh naso ace hada kai acikinsu na haɗa na ƙona,uban kowa ya huta da wannan masifar.....'
Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya kifa mata mari zazzafan gaske har sae da gefen bakinta ya fashe,
 Ɗagowa tayi da idanunta dake zubar da hawaye tace"Banji zafin marin da kayi mun ba!ada inajin shakkarka amma yanzu bana jin tsoranka acikin zuciyata,Wlh saina tona maku asiri duniya tasan me kuke aikatawa,daga nan in na fita gidan radio zanje in yaɗa duk wani mugun abunda kuke aikatawa,'
 Wani irin huci ya shiga yi zufa na gangarowa daga jikinshi sae tsuma yake yi,hannu yakai tare da shaƙo wuyanta ya bugata jikin wardrobe ɗin dakin,
 Sannan ya soma magana da wata irin murya mara daɗin ji yace"Ke daƙiƙiyace har yanzu bakisan ciwon kanki ba!kina tunanin cewa zan bari ki tona mun asiri ne!!kafin na juya maki tunaninki,inaso nasanar dake cewa Hosana jahad da sehrish ba ƴa'ƴa na bane!Da cikin abusufyan na aure ki!kuma nine na kashe mahaifinki baba buzu,saboda yana ƙoƙarin hanani auranki!'
Wasu irin hawaye ne masu zafin gaske suka shiga gangarowa a fuskarta,tsabar baƙin ciki da takaici yasa ta gaza magana,saboda wani irin ƙululun baƙin ciki daya tokare mata maƙoshinta,
  ƴa'ƴan naki ma bazan barsu ba!ɗaya bayan ɗaya saina kashe su!'
 Yana faɗin hakan ya saki wuyanta,da gudun gaske abu ta fito daga cikin ɗakin nashi tana kuka,a ƙopar gidan ta tsaya tana faman ambaton sunan baba buzu tana cewa babana ka kashe mun ka raba shi da ranshi,ka kashe mun babana ko,kuma zaka rabani da ƴa'ƴana suma ka kashe su ko......'haka ta dinga sambatu ita kaɗae,
 Tun daga wannan lokacin abu ta haukace ta miƙi santa tana faman sambatu,
Wannan shine silar rabuwarsu da mahaifiyarsu basu ƙara sanin inda take ba,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.