Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Sehrish bata bar bedroom É—in sgr ba,har sai da aka kira sallar magrib suka fita tare da abbansu domin zuwa yin sallar magrib sannan ta samu cikin sauri ta É—age curtains É—in,da hanzarin gaske ta sungumi mayafinta sannan da sauri hadda gudu ta haÉ—a wurin barin part É—insa,
Saukowa downstairs tayi a lokacin duk sun tafi salla masallaci,kai tsaye kitchen ta nufa tunkan ta ƙarasa ta hangi Azmee da hayaam suna ta haramar kammala dinner ɗin ranar,duk sai taji babu daɗi taso ace tare da ita suka fara,jiki asanyaye ta shiga kitchen ɗin da sallama a bakinta,
Juyowa sukayi suna kallonta atare,da alama ma sun kammala aikin nasu,Azmee ce ke haÉ—awa Hayaam warmers acikin tray tana kaiwa dining,
"Kin kammala gyara mashi part É—in nasa ne?azmee ce ta jefa mata tambaya,
"Eh,nagama,"
"Ya akai kika daÉ—e acan ne"?
Sunnar da kai tayi tana wasa da yatsun hannunta saboda ta rasa amsar da zata bata,
Hayaam kuwa sai faman wurga mata harara take yi kamar kwayar idonta zata faɗo ƙasa,
Murmushi azmee tayi tare da cewa"ki wuce kije kiyi sallah,kada ki samu damuwa,nasan cewa wani abunne ya tsayar dake,"
Ajiyar zuciya sehrish ta sauke kafin ta juya tasa kai tabar cikin kitchen É—in,bedroom É—inta ta nufa domin tayi sallah,
A 6angaren su hossana kuwa,tun bayan da suka dawo daga school suke ta faman saran zuwan Omar amma baizo ba,burin jahad ta sanar dashi cewa taga ƙaninshi a school ɗinsu,gaba ɗaya yinin ranar sunyi shi ne cike da kewar Ya omar ɗinsu musamman hossana ko lunch bata ci ba tunda suka dawo gashi ko'a school ma bataci komai ba,saboda tayi alƙawarin cewa tare da ya omar zasu ci abinci zai bata abaki,hakan yasa taƙi cin komai,duk yarda jahad taso ta fahimtar da hossana akan ta zauna taci abinci sam taƙi,har dai tagaji ta ƙyaleta,
sai faman zagaye takeyi acikin bedroom ɗinsu,fuskar nan ɗauke da murmushi ae tunda tayi arba da Romeo sam tagaza samun natsuwa wani irin tsantsar son shi da ƙaunarshi takeji kamar kamar me,fiye da yarda take jin ya omar ma lokacin da taso shi,saboda shi son da tayi mashi hada ƙarin don ta kyautata mashi ne akan irin ɗawainiyar da yake yi dasu,shi kuma kalar son da take yi ma junaid kallo ɗaya tayi ma kyakkyawar fuskarshi tabi ta rikice,kuma tunda Omar ya furta cewa ƙaninshi ne nan take taji ya kwanta mata aranta,sai dai abunda jahad bata sani ba shine,junaid ba babba bane kamar yarda take tunani,
**********haroon
Gaba ɗaya ya rikita ɗakin nashi wurin neman kuɗin da su Twins suka bashi,sam hankalin shi ya gaza kwanciya yama rasa inda zaisa kanshi,wata irin zufa ce ke gangaro mashi a fuskarshi saboda tsabar 6acin rai,yafi ƙarfin awa 2 yana neman jakar kuɗin amma babu ita ƙasa ko sama,an ɗauke ta daga ɗakinshi babu ita babu alamarta,yayi ma bedroom ɗin nashi kaca kaca wurin binciken inda jakar kuɗin take,kamar zaiyi hauka saboda yarda ya zauce,sun rigada sun gama tsara plan ɗinsu,
shirin tafiya kawai ya rage mashi daga zuwa ya É—auki jakar kuÉ—in an É—auketa daga É—akinshi,gashi ya rasa wanda ya shigo har cikin bedroom É—inshi ya É—aukar mashi ita,komawa yayi gefen gadonshi ya zauna yana faman huci kamar wani zaki,tunani ya shiga yi wanene zai iya shigowa É—akinshi ya É—aukar mashi jakar kuÉ—in shi?kodai su twins ne suka yi mashi wayau,don sunsan cewa ya goge videon shine suka É—auke jakar kuÉ—in,tabbas kuwa sune saboda su kaÉ—ai ne suka san da kuÉ—in acikin bedroom É—inshi,
Jinjina kanshi yayi yana huci yace"yara kenan harni zakuyiwa wayau,ƙananun ƴan iska kawai masu kwana da wando,saboda sun mayar dani shashasha shine suka zagayo ta bayan idona suka ɗauki jakar kuɗin,wlh sai kunyi danasani saina illata rayuwarku gaba ɗaya muddin baku maido mun da kuɗina ba,"ya faɗi a lokacin da ya miƙe tsaye zumbur yana faman naushin tafin hannunshi na dama da hannunshi na hagu,tashin hankali da ba'a sama shi date,
**********************Amani
Zaune take saman 3 seater,yayin da Amal ke zaune kusa da ita,ta fito fess abunta tayi wanka ta bata kaya ta canza duk da rigar tayi mata yawa saboda kayanta ne taba ma amal ɗin ta sanya kafin zuwa gobe zata je da ita shopping mall ta zabi abunda take so,ta kuma yi mata siyayyar kayan sawa da sauran abubuwa na rayuwa wanda zata buƙata,
Hannunta na ruƙe da wayarta,shiga contact ɗinta tayi tare da nemo numbar Aunty babba ta buga mata call,nan take wayar tashiga ringing,
Hafsat na faman zarya acikin parlourn nasu taji shigowar kira a wayar mommynta dake ajiye saman hannun kujera,cikin sauri takai hannu tare da ɗaukar wayar,ganin sunan Amani ya bayyana ne yasa ta juya tare da tunkarar kitchen ɗin,tunkan taƙarasa aunty babba tafito daga kitchen din jin ringing ɗin wayarta,miƙa mata wayarta tayi tare da cewa"Amani ce ke kira,"
Yatsina fuska tayi tare dasa hannu ta kar6i wayar bayan tayi picking ta kara wayar a kunnanta tana cewa"Sai yau kika tuna dani"?_
on the other hand Amani tace"Am really sorry auntyna takaina,kullum kina araina,kawai abubuwane sunyi mun yawa,"
tsoki aunty babba taja tare da cewa"Abubuwa su kayi maki yawa,ciki gare ki ko goyo"?_
Amani tace"ko ɗaya daga cikinsu babu,pls mubar zancen ae nabaki haƙuri,yanzu akwai maganar da nakeso nayi maki pls,"
Aunty babba tace"kunne ke ji,"
"dama maganar Amal ne!wai har yanzu ba labarinta?ba'asan inda take ba?nagaza samun kwanciyar hankaline saboda mafarkin da nayi jiya agame da ita,"
Shu'umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa"Yawwa dama inaso nayi maki magana game da Zancen neman Amal,munyi waya da mammy ta sanar dani cewa an samu wasu malaman da zasuyi mata sauka,manyan malamai ne na addini kuma da zarar sunyi saukar nan ake cin sa'a buƙata ta biya,"
Ƙiriss ya rage Amani ta saki dariya,don tsabar takaici da ban haushi,aranta tace wai sai yaushe matar nan,zata daina ƙarya ne?
Juyawa tayi ta É—an kalli Amal dake zaune hankalinta kwance idonta na kallon plasma tv É—in dake facing dinsu,tana kallon tashar mbc 3,
gyara murya Amani tayi tare da cewa"Masha Allah,gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba auntyna takaina,ashe ansamu wasu malaman ae ni indai akan Amal ne ko nawa ne zan iya badawa,ko bani dasu zan nemo ne,'_
Jin haka yasa aunty babba,janye wayar daga kunnanta tana faman 6a66aka dariyar mugunta,duk hafsat na tsaye tana kallonta baki asake saboda tasan da zancen neman Amal ɗin,kuma a gabanta Jiya abra ta kira mommyn nata tana sanar da ita cewa Amal ta gudu,sarai tasan cewa yarinyar ta gudu shine kuma takeson ƙara cutar da Amani saboda tsabar son abun duniya?
"Yanzu nawa zan tura kenan"?acewar Amani,
Aunty babba tace"ba wasu kuɗine masu yawa ba,dubu ɗari takwas ne,ae ni nayi mamakin ma yarda suka faɗi kuɗin da sauƙi har haka,"
murmushin takaici amani ta saki kafin tace"okey,zanyi maki magana indae na samu kuÉ—in,yanzu dae mu koma zancen Hayaam,shin har yanzu tana maid ne ko tazo Abujan nan"?
"Tun jiya fa ta ƙaraso,yanzu ae ta jima da zama ƴar gida,"ta ƙarasa maganar tana washe baki,anzo inda tafi auki,
É—an ta6e baki amani tayi tace"Okey yayi kyau,yanzu komai zai fara tafiya dai dai,akwai wani albishir da zanyi maki,"
Natsuwa Aunty babba tayi tare da cewa"ina sauraronki ƙanwata,faɗamun albishir ɗin,"
Shu'umin murmushi Amani tasaki tare da miƙewa daga saman sofa ɗin tabar Amal zaune tana kallo,takawa tayi nesa da falon,sannan tace"Nasan inna faɗa maki albishirin nan ko bacci ba zaki iya yi ba saboda tsabar farin ciki,"
A ƙagare Aunty babba tace"dan Allah shaƙamun mana kanwata wane irin albishir ne wannan,
Murmushi Amani ta kuma yi sannan tace"nasamo ma Hayaam maganin mallaka a wurin wani hamshaƙin boka,aikin shi tamkar yankan wuƙa yake,saboda Ni shaidace akan idona aka ta6a amfani da maganin kuma yaci,"
Cike da farin ciki Aunty babba tace"Wai dagaske"?
dariya amani tayi tare da cewa"dagaske mana!,wata neigbour ɗinace keson ƙanwarta ta auri ƙanin mijinta,sun rasa yarda zasu jawo hankalinshi acikin gidannan saboda mutunne mai matuƙar ji dakai,kamar dai sgr,ina baki labari kwatsam sai ga wata ƙawarmu ta bamu labari akan wani shu'umin boka,agabana aka shirya zuwa wurin bokan suka amso maganin,a yanzu dai labarin da nake baki,yarinyar na nan ta aure shi hada ciki ma sai faman shan soyayya suke abun gwanin burgewa,"_
Saboda tsabar Murna Aunty babba ta gaza rufe bakinta dakyar ta iya cewa"Yanzu ya za'ae kenan asama ma Hayaam maganin?nawa zamu nema"?
"Ko sisi basai kin bada ba Auntyna,fisabilillah na amso ma hayaam maganin da kuÉ—ina ai nima kanwata ce ko,nidae burina shine inga ta auri sgr Abra kuma ta auri marshal Omar,"
washe baki Aunty babba tashiga yi tana cewa"Allah sarki Amani,ashe haka kika damu da ƙannen namu?gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba,yanzu kenan Hayaam zatazo ta kar6i maganin gidanki kenan"?
Amani tace"eh,in ma batasamu zuwa ba ni zanje nakai mata shi,babu damuwa,"_
Sun jima suna waya kafin daga bisani firar tasu ta ƙare anan,
Tuntsirewa da dariya Aunty babba tayi tana tafa hannu tashiga cewa"ban ta6a ganin Æ´ar wahala ba irin Amani,duk irin abunda nakeyi mata amma ita burinta ta taimakamun wurin ganin na cimma burina,gaskiya na tausaya mata,abun tausayi,
girgiza kai kawai hafsat tayi tare da wucewa ciki tabar mommyn nata tana ta faman sambatu,
A can 6angaren kuwa fashewa da dariya Amani tayi tare da cewa"Aunty laila kenan!ke atunaninki kinyi mun wayau bakisan cewa Amanin da kika sani ada ba ita bace ayanzu ba,ashirye nake dana kwance dukkan wasu notikan kanki,zan mayar dake kamar wata zararra,ita kuma hayaam zanyi amfani da wannan damar wurin ganin na canza mata halittar jikinta,kamar yarda kuka canzawa Amal kamanni ta tsotse ta rame ta ƙanjame haka itama nakeson ta koma,dama ance ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,that's my plan!
Tana faɗin hakan ta juya tare da komawa wurin Amal ta zauna,kallonta Amal tayi tare da cewa"Aunty amani,dan Allah kiyi haƙuri da abunda zan faɗa maki,bansan ko zai 6ata maki rai ba,nasan cewa su mammy sun cutar damu sosai,amma kada kice zaki ɗauki fansa,mubarsu da Allah kawai shi zai saka mana,sannan in zamu iya mu taimaki mahaifinmu don yana cikin mawuyacin hali"
Shuru kawai amani tayi batace mata komai ba,amma fa har yanzu tana akan bakanta,maganar mahaifinsu kuwa tasan matukar mammy na numfashi bazata barshi ya sarara ba,don ba karamar shedaniyar mata bace,ita kanta yanzu tana shakkun in don Allah aka hadata da Abbas.
_💋Boss Bature💋_
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.