Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Sosai junaid ya shiga romancing ɗinta kamar zai zauce,duk yarda jahad taso ta kwace kanta a hannunshi amma yaƙi barinta,sai da yayi mai isarshi sannan ya zame jikinshi daga nata,cikin sauri jahad ta kifa kanta asaman laps dinta,tana faman sauke ajiyar zuciya,sam tagaza yarda cewa itace da kanta ta ba wani namiji damar kissing lips ɗinta abunda bata 6ata yi ba,to dama dae duk inda mace da namiji suka ke6e irin haka na ukkun su shaidan ne,Allah ya kyauta.
   jikinshi ne yayi sanyi,shi kanshi baisan cewa abun zai kaisu ga haka ba,daƙyar ya iya tashin motar da wata irin kasala ajikinshi yake driving din,ya hau saman titi sosae tare da wucewa dasu gida,
 Â
_💋Boss Bature💋_
tashin hankali!Lokacin da Hosana ta fito a nan ta samu osman yana jiransu tsaye a bakin motarshi,
  ƙarasawa tayi wurinshi tana cewa"ya Osman Ina jahad ɗin?ina ta nemanta banganta ba,nayi tunanin ta rigani fitowa ne,"
  "Wai kina nufin jahad bata acikin school ɗin naku"?ya tambaya hankali a tashe yana kallonta,.
daga mashi kai tayi alamar eh tace"babu kowa acikin makarantar ya Osman,na duba ko'ina ban ganta ba,"
 Gabansa ne ya faɗi rass,saboda kullum jahad ita ke riga hosana fitowa,yau kuma hosana ta rigata fitowa,tabbas akwai matsala,
 cikin sauri yace"shiga ki zauna bari nashiga cikin classes din na duba ko zan same ta acan,Allah dae yasa ba wani mummunan abune ya faru da ita ba,'
 Ya ƙarasa maganar tare da yin saurin shigewa cikin makarantar,buɗe motar hosana tayi tare da shigewa ciki ta zauna tana jiranshi,
 lokacin da Osman ya shiga cikin classes din yana neman jahad,duk ajin daya duba babu kowa wayam duk sun tafi gida,ko'ina ya dinga bi na makarantar saƙo da lungu yana dubawa amma babu jahad babu alamarta,tun yana sa ran ganinta har ya fidda rae,yafi ƙarfin awa ɗaya da rabi acikin makarantar yana neman jahad amma bai ganta ba,
 Cikin sauri ya fito jiki na rawa ya koma cikin motar,ya zauna a mazaunin driver,
 Ganin ya dawo shi kadae yasa hosana cewa"Ya osman ina jahad din?baka ganta ba"?
  "Na duba ko'ina banganta ba,bansan ina jahad taje ba,bari na fara kaiki gida nasan kin gaji sosai,"
  jan motar yayi tare da fucewa daga cikin gate ɗin makarantar,duk yabi ya ruɗe saboda fargabar kada ace wani abune ya faru da jahad,yana jiyo hosana tana shessheƙar kuka tana cewa"Nashiga uku,Allah yasa jahad bata 6ace ba,bansan ya zanyi ba in na rasata ba,kamar yarda na rasa sehrish,"
   "Kada ki damu jahad tana cikin ƙoshin lafiya,zan nemo maki ita,in ma ban sameta ba,zan kira major na sanar dashi halin da ake ciki,nasan zaiyi ma marshal Magana,"ya ƙarasa maganar a lokacin da yake shiga kwanar gidan Abusufyan,
Yana shiga ciki ya sauke hosana,sannan ya fisgi motar da gudun gaske ya fuce daga gidan,
Abunda ya faru bayan fitar motar osman daga cikin school din,Sai ga sehrish hannunta ɗauke da school bag ɗinta,daƙyar take iya tafiya saboda ciwon da tasha,ta jima acikin toilet din tana juyi kafin Allah ya kawo mata sauƙi harta samu ta fito,
ganin babu kowa acikin makarantar yasa taji gabanta ya fadi,nan tashiga fargabar Allah yasa junaid bai tafi ba,tasan dole ya gaji da jiranta,
Lokacin da taƙarasa wurin gate din taga babu kowa sai security guard din dake tsaron makarantar,tamkar ta aza hannu akai ta fashe da ihu haka taji,
Ganin yarinya tsaye cikin damuwa yasa mai gadin ya ƙaraso wurinta yana tambayar ko lafiya,
muryarta tamkar za tayi kuka tace"Mai É—aukata nake nema,kuma naga babu kowa acikin makarantar,bansan ya zanyi ba,"
mai gadin yace"meyasa baki fito kin tsaya anan waje ba?me kikeyi acikin makarantar ne"?
cikin shessheƙar kuka tace"bani da lafiya ne,bacci ne ya ɗauke ni kuma babu wanda ya tashe ni,shiyasa bansamu na fito ba akan lokaci,"
"Kuma baki da waya a hannunki"?acewar mai gadin,
É—aga mashi kai tayi alamar eh,
"Ko numbar wani baki ruƙe a cikin kanki ba,"
"Bani da numbar kowa,ban ruke akaina ba,"
Cike da takaici mai gadin yace"kaji matsalar,ni yanzu bansan ya zanyi dake ba,amma me zai hana ki ɗan fita daga wajen gate ɗin,wata'ƙil shi drivern naki ya dawo daukarki,nasan ma zai dawo ne,da zarar sunji shiru baki ƙarasa ba",
Amsa mashi tayi da toh,sannan ta fice daga cikin makarantar ta tsaya a bakin gate din,tana ta Æ´an waige waige ko zata hango motar junaid,
_💋Boss bature💋_
A hankali motar junaid ta ƙetare babban gate din gidan nasu,a lokacin jahad ta ɗago da kanta,ta cikin glass ɗin take hangen katafaren gidan,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,yau gata acikin gidansu ya Omar dinsu,koba komai zata hadu dashi harma ta sanar dashi halin da suke ciki na rashin ganin shi,addu'a tashiga yi acikin ranta Allah yasa Ya Omar na nan,
tsayar da motar junaid yayi tare da buɗewa ya fito sannan ya zagaya ya buɗe ma Jahad motar,cikin sanyin murya yace"Reesh,am really sorry game da abunda ya faru a tsakanin mu,na fita hayyacina ne shiyasa,kinsan cewa ba halina bane.....kuma bazan ƙara ba insha Allah,
Murmushi jahad ta sakar mashi ayayin da take fitowa daga cikin motar tace"just forget about it,komai ya wuce,na yarda dakai sosai nasan cewa bada son ranka hakan ta faru ba,
ba ƙaramin daɗi junaid yaji ba,ya jima yana mamakin nasarar daya samu akan reeshi ɗinsa,farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,
Bayan ya rufe motar ya ruƙo hannunta suka shige cikin gidan atare,a ruɗe jahad ke kallon katafaren gidan,jinjina kai kawai takeyi acikin ranta tana cewa"wai dama a wannan daular ya Omar ke rayuwa!gidan yayi mun kyau ya haɗu sosai,Allah yasa yana ciki,inaso na cika ma hosana alƙawarinta na ganin na haɗata da ya Omar dinta,
Babu kowa acikin main palour É—in,sakin hannunta junaid yayi tare da cewa"bari na shiga ciki na huta,da anjima zan shigo muyi magana,"
amsa mashi tayi da toh,cikin sauri junaid ya wuce bedroom din Abbansu,
tashin hankali,jahad fa batasan ina zata dosa ba,gata dae acikin gidansu Omar,batasan a ina zata ganshi ba,
Tsayawa tayi ƙiƙam batare da ta motsa ba,
Gyaran muryar da taji ne yasa ta yin saurin juyawa don taga wanene,
Azmee ce ta fito sai faman sakar mata murmushi takeyi,jikinta sanye da jallabiya,ta É—aure kanta da mayafi,ta fito fess abunta,
Gaban jahad ne ya shiga faduwa aranta tashiga tunanin cewa kodae wannan ce mahaifiyarsu?Amma meyasa naga tana sakar mun murmushi kamar tasanni itama...?
Bata ƙarasa zancen zucin nata ba,azmee ta ƙaraso tare da janyota jikinta ta rungumeta tana cewa"Sannu da dawowa kyakkyawata,ya school din?
Tayi maganar tare da raba jikinta daga na Jahad,
Zuru jahad tayi duk tabi ta dabarbarce ta rasa ganema wannan abun al'ajabin,tamkar a mafarki haka take ganin wannan ikon Allah,
"Rishi lafiya naga kina bina da kallo?kodae bakya jin daÉ—i ne?nayi magana baki amsa mun ba"
Cikin en ina jahad tace"am...um...lafiya lou,makaranta Alhamdulillah,'
Azmee tace"ko ke fa,shigo daga ciki na hada maki lunch ki ci,ko kya dawo daedae don na lura yau ba ƙaramar yunwa kika kwaso ba,"
Tayi maganar tare da ruƙo hannun jahad taja ta suka nufi dakin sehrish,da kanta ta buɗe mata kopa tare da shigar da ita ciki tace"ki zauna ki huta,yanzu zan haɗo maki lunch,"tana faɗin hakan ta rufe mata dakin,
Abun ya gama ɗaure mata kai,juyawa tayi tana ƙarema bedroom ɗin kallo ba ƙaramin kyau yayi mata ba,daga bisani kuma ta shiga damuwa akan wane hali hosana ke ciki,tasan cewa zasu nemeta sosai,kuma in basu ganta ba hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba,
komawa tayi daga gefen gadon sehrish ta É—an zauna,ya zama dole in koma gida,kada hosana tayi ta kukan rashina akusa da ita,bansani ba ko zan samu ya omar acikin gidan nan ba,ni ba komai yafi É—auremun kai ba face yarda suke nuna kamar sun sanni,bayan bamu ta6a haduwa da kowannansu ba,to kodae dukkansu suna da mental illness ne?ta jefa ma kanta tambaya,
Turo kopar azmee tayi tare da shigowa hannunta ɗauke da tray wanda ta shirya mata lunch,ƙarasawa tayi tare da ajiye mata tray din asaman bedside drawer dinta tace"Wannan farfesun da kike gani,hajiya azeema na shirya mashi,ƙanwar abbanku da nake gaya maki,tana nan ta iso,nasan bakisanta ba,amma kin ta6a ganinta lokacin da Sgr da Omar suka dawo daga U.S kin tuna"? Fuskarta ɗauke da murmushi takeyi mata maganar,
Jin ta ambaci sunan Omar yasa jahad cewa"Ya Omar na nan"?
Azmee tace"eh,yana acikin part dinshi,amma meyasa kika tambaye shi?maimakon ki tambayeni mutumin ki Sgr"?
"Babu komai,kawai inason ganin shi ne,"ta bata amsa,
Azmee tace"ki bari idan kin kammala shan farfesun sae kije ki same shi adakin shi,'
gyaÉ—a kai jahad tayi tare da cewa toh,nagode sosai,bari na fara sha,
Juyawa azmee tayi tare dayi mata sallama ta fuce daga dakin,a ranta tana tunanin ko wani abu ke damun rishin ne taga duk tayi sukuku.
Zama jahad tayi tare da dauko plate ɗin dake ɗauke da farfesun,sae uban ƙamshi ke tashi,duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hanata shan farfesun nan ba,sae da taci ta ƙoshi, sannan ta miƙe tare da shiga toilet ta wanko hannayenta,
Bayan ta fito komawa tayi saman gadon ta zauna cike da zullumin mai zai biyo baya,
_💋Boss Bature💋_
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.