Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
 Omar yace"abun ya ɗaure mun kai major,kaji wani iko na Allah nan,gaba ɗaya yaran su ukun suna a ƙarƙashin kulawar family dinmu,duka Allah ya haɗasu awurinmu batare da saninsu ba,kuma batare da sanin mu ba,ita ɗayar ƙaddarar aiki ce ta kawota gidan mu,yayin da su kuma su hosana da jahad,ƙaddarar zaman asibiti ce ta haɗani dasu a lokacin da hosana ke hauka hannunta ruƙe da bindiga,Major abun akwai wata sarƙaƙiya acikinshi,tabbas akwai abunda Allah yake nufi da waɗannan yaran!akwai wani abu da Allah ke son bayyana mana shiyasa ya haɗasu duka awurin mu!"
 Zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi ita kanta abun ya ɗaure mata kai,
 Shi kanshi major ya shiga kokonton cewa Anya yaran basu da alaƙa dasu Marshal Omar?juyawa yayi ya dan kalli fuskar marshal sannan ya mayar da idonshi akan hosana,sae lokacin ya dinga ganin wata irin kamanceceniya atsakaninsu sosae,tabbas akwai wata alaƙa ta jini a tsakaninsu,shiru kawai yayi baice komai ba,
 Kowa ya tafi duniyar tunani hafsat bature ma,ta ɗan ajiye typing tana tunanin wannan abun daya ɗaure mata kai tamau...,
 "Ya Omar,"gaba dayansu sukayi firgit suna kallon Hosana dake kwance tafarka tana faman mutsistsike idanunta,jin muryar Omar yasa ta ambaci sunan shi,
 Murmushi ya dan saki tare da ambaton sunanta "Hosana",
 miƙewa tayi zaune tana ƙare masu kallo gaba ɗayansu,tashi Omar yayi ya koma gefenta ya zauna yana kallonta,
  lokacin da ta tabbatar cewa shine saita fashe mashi da kuka tana cewa"Ya omar fushi nake dakai,meyasa ka tafi kabarmu kadaina zuwa wurin mu?laifin me mukayi maka da har kayi mana wannan horon"?
Lallashinta ya shiga yi yana cewa"Am really sorry hosana..pls stop crying and wipe ur tears,komai ya wuce yanzu muna tattaunawa ne game da Æ´ar uwarku Sehrish...... '
 Tunda ya ambaci sunan sehrish hosana tayi tsit ta nemi kukan da takeyi ta rasa la66anta har rawa sukeyi wurin cewa"Anganta ne ya omar?"
 Murmushi Omar ya saki tare da cewa"An ganta hosana!ƴar uwarku da ku ka jima kuna nema,ashe itace yarinyar dake yi mana aiki agidan......"bai ƙarasa maganar ba hosana ta fashe da kukan murna tana cewa"Ya omar tana ina?ina rishi ɗinmu take?inaso naganta!tana ina,wayyo Allah na....'
 Yarfa hannunta tashiga yi saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa hawaye na zuba fuskar kuma ɗauke da dariyar farin ciki,
 Itama jahad farin cikin ne tsantsa afuskarta yau takasance babbar rana agaresu rana mafi girma arayuwarsu ranar da Allah yasa suka gano inda Æ´ar uwarsu sehrish take,dole suyi farin ciki,bama su kaÉ—ai ba,hatta masu karanta labarin rayuwarsu da kuma marubuciyar data zauna ta tsara labarin ita da kanta tana taya su farinciki,Ya Allah ka Æ™ara danÆ™on Æ™auna atsakaninmu da Æ´an uwanmu masu son mu,Allah ka bamu ikon faranta ma juna da kuma taimakon junanmu,a gudu tare kuma atsira tareâ?
Omar ya jima a wurinsu hosana kamar karya tafi ya barsu haka yaji,abunda yasa bai tafi dasu yau ba saboda Yarinyar gidan tasu da ba'a gani ba,yafi son sai sun É—auko yarinyar sannan ya kaisu gidan nasu don suga Æ´ar uwarsu ido da ido,zai so yaga wannan farin cikin a fuskokinsu,
Bayan tafiyar su Marshal Omar,jahad da hosana duk sun bi sun ruɗe saboda tsabar murna ko abincin rana basu ci ba,sai faman sintiri sukeyi acikin babban falon nasu,aƙagare suke dasu ga sehrish,zuciyarsu sae faman azalzalarsu take akan son ganinta kamar suyi hauka.
💋BOSS BATURE💋
Ga wani tashin hankalin kuma,duk yadda sojojin nan suka so su kama sehrish abun yaci tura domin kuwa sehrish ta kubce masu,babu irin neman da basuyi mata ba,amma babu ita 6at ta 6ace kamar al'jana,abu kamar wasa har bayan sallar La'asar basu ganta ba,
Niko sehrish ina kika shiga ne!kai jama'a daga antaro nan sae kuma nan ya ruguje,
tunda Abbansu ya sanar mashi game da zuwan Aunty azeema,jiki na rawa junaid ya fito daga dakin Abbansu da gudun gaske ya nufi ɗakin da aka saukar da ita,faɗawa cikin ɗakin yayi ko sallama babu saboda tsabar ɗoki,a lokacin tana daga zaune saman gadonta tana daddana wayarta,sam bata lura dashi ba,bata ji shigowarshi ba,sae dae kwatsam taji faɗowarshi jikinta,gaba ɗaya ya ƙanƙameta sosai,yana yi mata kukan shagwa6a wai yayi missing ɗinta sosai,
Dariya sosai hajiya Azeema tashiga yi tana cewa"Oh ni junaid,tun ɗazu nake ta tambayar ina babynmu yake ina babyn mu yake,duk na ƙosa naganka naso ace ina shigowa cikin gidan nan kaine mutun na farko da zaka fara tarbata da wannan sumbatar taka,"
 ta ƙarasa maganar tare da ɗago shi daga jikinta tana bin shi da kallo tace"Masha Allah,junaid kaine ka koma haka?ka ƙara girma sosai kyakkyawan yarona,nayi missing ɗinka sosai,"
 murmushi junaid ya sakar mata tare da cewa"mommy azeema ina tsarabata?me kika kawo mun"?
 Dariya tayi tana girgiza kai tace"Tsarabarka na nan junaid,wannan karan nazo maka da abun ban mamaki,inaso inga farin cikin da zakayi idan nabaka tsarabar nan,"
 cike da zumudi junaid yace"tana ina,"
 Harara ta ɗan watsa mashi tare da cewa"Shine damuwarka?ka manta baka bani kiss dina ba,"
 matsawa junaid yayi tare da kai bakinshi gefen fuskarta ya manna mata kiss sannan ya ɗago yana kallonta yace"yanzu sai aban tsarabata ko"?
 Dariya tayi tace"ɗaukomin trolley ɗin kayana,"tayi maganar tana yi mashi nuni da trolleyn da Kanal yousouf ya jingine mata ajikin wardrobe,
 jiki na rawa junaid ya saukko daga saman gadon ya taka izuwa wurin wardrobe din ya ruƙo trolleyn tare da janyoshi har wurin gadon ya miƙa mata shi,sannan ya zauna daga gefe ya zuba ido yana jiran ganin tsabar da tayi mashi,
  hannu tasa ta buɗe trolley din ta curo wani ɗan kit ƙarami sai faman ƙyalƙyali yake yi yadda kasan da gold akayi jikinshi,tunkan ta buɗe shi junaid ke ta faman haɗiye yawu yarda kasan yaga abunci,
   Murmushi ta danyi tare da kallon fuskarshi tace"close ur eyes,"
 Rufe ido junaid yayi kamar yarda ta umarta,
  Murmushi ta kuma yi tare da buɗe akwatin tace"Now Open ur eyes,"
  A hankali junaid ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka akan danƙareran Zoben diamond ɗin da ta siya mashi tare da agogonshi,sae faman ƙyalli suke suna ɗaukar ido,diamond bana wasa ba,wanda aƙalla price ɗinsu yayi miliyan ɗari uku,
 Waro ido waje junaid yayi yana bin su da kallo saboda tsabar farin ciki ya gaza rufe bakinshi,hannunshi na kerma ya kar6i akwatin yana ƙare masu kallo,
Cikin tsantsar farin ciki yace"aun...aunty..wannan duk nawa ne"?
  dariya Azeema tayi ganin yarda yabi ya rikice ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba,saboda bata da wani burin daya wuce taga ta faranta mashi,tana son ganin farin cikin junaid sosai,yaron tun yana ƙarami take tsananin son shi,
 "Junaid duk naka ne wannan,Na musamman ne nasa akayi maka shi,duk duniya babu mai irin shi sae kai kaɗae,ni da kaine na bada sample ɗin yadda za'a haɗa maka shi,ka duba a jikin zoben ka gani,Harafin J ne ajiki wato farin sunanka,"
Wani irin farin ciki ne,ya cika junaid,a ƙarshe daya rasa abun cewa kawai sae ya fashe mata da kuka Yana cewa"mommy azeema,narasa da wasu kalmomi zan iya gode maki,babu su abakina,kin sanyani farin ciki sosai da wannan kyautar da kika bani.
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.