Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Zaune take acikin class ɗin gaba daya ta shiga damuwar rashin ganin Sehrish kwana biyu ko layinta ta kira bata samu,hatta wayar junaid ta jaraba kira shima ba'a ɗagawa,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tagumi tayi idonta cike tab da hawaye saboda damuwar da take ciki,taso ace sehrish na nan atlease zata ɗebe mata kewa,tana cikin wannan tunanin har malam ya shigo cikin class ɗin nasu bata sani ba,bayan ya kammala amsar gaisuwa daga wurin student din,kai tsaye ya ƙarasa seat ɗin da Amrish take,hannun shi yakai wanda ke ruƙe da maker ya ɗan bubbugi desk ɗinta,a firgice takai idanunta akanshi,Yunƙurawa tayi tare da miƙewa ganin Ya mu'allim,wanda tun ranar daya ba sehrish Ruwan addu'ar nan bai ƙara zuwa makarantar ba,duk da sun samu labarin cewar Ya tafi Umra ne,shiyasa aka musanya masu shi,
Murmushi ya É—an saki afuskarshi yana kallonta yace"tunanin me kike yi ne?har na shigo cikin class É—in baki sani ba?
Muryarta na rawa tace"Ayimun afwa ya mu'allim,Bana jin daÉ—i ne bansan ka shigo ba,
Jinjina kanshi yayi tare da É—an kai idanunshi kan Seat É—in sehrish yace"Ina yarinyar nan take?Æ´ar family É—in Salahuddeeen hussein naga kamar bata a class É—in"?
fuskarta É—auke da damuwa tace"Batazo ba,yau kusan kwana huÉ—u kenan bata zo school ba,kuma nayi trying kiran layinta amma bana samu,har brother É—inta na kira,shima layinsa ba'a samu,'
Jin hakan yasa shi fargabar to kodai wani abu ya faru da yarinyar?Yaso yaji ya tayi da ruwan addu'ar daya bata,shin tasha ko bata sha ba?
Jinjina kanshi yayi tare da juyawa yace"Allah yasa dae lafiya,in har batazo ba,zuwa sati mai zuwa zan je gidansu don na binciki dalilin rashin zuwan nata,'
Jiki asanyaye Amrish ta koma ta zauna,saman seat É—in nata,jikinta har ya fara kerma saboda tsoran kar ace wani abune ya faru da Sehrish,
A ƙarshe dae ta yanke shawarar neman gidansu don taje ta ganta da kanta.
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
Sai faman safa da marwa takeyi acikin bedroom ɗinta,gaba ɗaya ta rasa samun natsuwa,hakanan ta dinga jin fargabar zuwa abuja,ga zumuɗin zuwan da takeyi amma kuma tana zullumin abunda zai biyo baya,hakanan ta dinga jin kamar wani abu mara daɗi zai faru,ƙafafunta har sun fara ciwo saboda zaryar da take ta faman yi,tun bayan da ta kammala sallar asuba bata koma bacci ba,Jikinta na sanye da Zumbuleliyar riga doguwa brown,sae guntun hijabin da ta kammala sallah dashi,hannunta na ruƙe da wayarta,wani tunani ne ya fado mata aranta,cikin sauri ta shiga danna wayar dake hannunta,Hayaam ta buga ma waya,nan take kiran ya shiga,batare da 6ata lokaci ba hayaam ta ɗaga kiran,daƙyar take magana saboda ta katse mata baccinta,rai a6ace tace"Lafiya kika kira Ni?bayan kin gama kwashe mun albarka"!
 Cikin lallami Aunty babba tace"Dan Allah hayaam komai ya wuce kinji ƙanwata?nasan ban kyauta ba,amma kiyi haƙuri,"
 Tsoki hayaam taja tare da cewa"hmmm,halan yanzu kin gasgata maganata ne?shiyasa kika kira don jin ƙarin bayani?
 Aunty babba tace"EH,hakane,na yadda da abunda kika faɗamun,tuntuni shiyasa ma na kira ki,"
 Hayaam tace"Yanzu ya kenan?ya zamuyi?don gaskiya akwai matsala aunty laila,burin mu bazai ta6a cika ba,muddin yaran nan suna nan!"
 Jinjina kai Aunty babba tayi tana cewa"babban takaicina yaran da suka kasance mata ne!har ƴan uku,gaskiya abusufyan bai kyauta mana ba tsakani da Allah,haka ake?kawai sai yaje yayi aure a 6oye batare da sanin kowa ba?wai kuma da sanin ammi kuwa"?
 Hayamm tace"Anya,gaskiya ina tunanin Ammi bata sani ba,'
 Jin haka yasa Aunty babba cewa"Allah yasa in tazo tace bata amince da yaran ba,kinsanta Jarababbiyace,musamman ma da yayi auren bada saninta ba,Wai shin su yaran ina mahaifiyarsu take ne?tana da asali kuwa"?tayi tambayar cike da son jin ƙarin bayani,
 Hayamm tace"Ina fa,ae rannan na tambayi azmee game da mahaifiyarsu,shine take sanar dani cewa mahaifiyar yaran Ƴar fa mai gadin gidan gwaggon katsina ne!basu da wani asali,buzaye ne ƴan niger,"
 Aunty babba tace"tabɗijancan aikuwa Ammi bazata ta6a yarda dasu ba,kinsanta ta tsani mutun mara asali,gata ita kaifi ɗaya ce muddin tace bata yarda dasu ba amatsayin ƴa'ƴan Abusufyan to fa korasu zatayi daga gidan,yakamata muyi wani abu akai,tun kafin takai ga zuwa,"
 Hayaam tace"meke nan zamuyi?kinsan fa gobene walimar kuma gobe zata zo,"
 "Abunda zamuyi shine,Ae ina da numbar Ammin a wayata,zanyi amfani da sabon sim ɗina,wanda ban fara amfani dashi ba,zan kirata na sanar da ita game dasu tunkan taji a wurin wani,"acewar Aunty babba
 dariya hayaam tayi tare da cewa"Gaskiya aunty laila kin iya haɗa tuggu,ni sam banyi tunanin hakan ba,wannan ce hanyar da zamu bi wurin tarwatsasu,idan kika kirata awayar ki tunzurata sosai,ki ɗaurata akan network har sai ta amince da kalamanki,ki sanar da ita cewa yaran shaggu ne,abusufyan yayi ma mahaifiyarsu ciki a 6oye,shine suka so su 6oye mata,don karta sani,"
 Murmushi Aunty babba ta saki tana cewa"hakan yayi sosai,zan tsara komai yanzu........."tana cikin maganar taji alamar dirar motar ishaq,
 Cikin sauri tace"Hayaam inaso ki ɗauko min hoton yaran kafin muzo gobe,zan kashe wayar yanzu ishaq ya dawo,
 "Toh aunty laila,zanyi ƙoƙarin ɗauko maki hoton nasu,"
Daga haka sukayi sallama da juna,
Ajiyar zuciya aunty babba ta sauke,har taji wani sanyi a ranta saboda ta samu mafita,
Bayan sun kammala wayar hayaam ta buɗe ƙopar ɗakinta tare da fitowa,cikin sanɗa hayam take tafiya don kar wani ya ganta,a haka har ta ƙarasa bedroom ɗinsu sehrish,tura ƙopar tayi cikin sa'a ta samu ƙopar ɗakin a buɗe,leƙa kanta ta fara yi anan ta same su,suna ta sharar bacci wanda tun bayan sallar Asuba da suka tashi suka koma suna yin baccin,
Murmushi ta saki tare da sa kai ta shige ciki,adai dai bakin gadon nasu ta tsaya tare da É—ago da wayarta dama already a cikin camera take,Saita fuskarsu tayi dama kuma duk suna facing É—in ceilling,kyakkyawan hoton fuskokinsu ta É—auka,bayan ta kammala É—aukar hoton,ta lalla6a batare da kowa ya ganta ba,ta koma bedroom É—inta,cikin sauri ta tura ma Aunty babba hoton ta whatsapp É—inta,
â¤ðŸ¤â¤
Wuraren karfe takwas,suka farka daga bacci,sehrish ce ta fara shiga toilet tayi wanka,bayan ta fito daga wankan jahad ta shiga ciki,gaban dressing mirror ta zauna ta gama shafe jikinta,ta feshe shi da turare,sannan ta koma ta ɗauko Jallabiya fara ta zura ajikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,musamman adon dake jikin rigar na stones,shiya ƙara ƙawata rigar,bayan tayi rolling kanta da mayafin rigar,ta fito daga cikin bedroom ɗin nasu ta wuce kitchen,cike da zumuɗin kaima babban yaya breakfast ɗinshi gaba ɗaya ta manta da abunda Uncle abusufyan ya faɗa mata,
A kitchen ta samu azmee,har ta kusa kammala girkin,ganin yadda take ta aiki ita kaÉ—ae yasa sehrish taji duk ba daÉ—i,muryarta a sanyaye tace"Ina kwana Aunty azmee,"
Juyowa tayi daga tsayen da take gaban gas cooker,fuskar nan É—auke da murmushi tace"Lafiya lou Æ´an matan abusufyan,fatan kun tashi lafiya"
 "Lafiya lou,amma aunty azmee gaskiya banajin daɗi in naga kina aiki ke kaɗae,meyasa baki tashe mu ba,munzo mun tayaki aikin"?tayi maganar yayin da take ƙarasa shiga cikin kitchen ɗin,
 Azmee tace"kada ki damu,na riga na saba da aiki,wannan ba wani abu bane,Abba ma ya nemi daya ƙaro masu aiki amma nace mashi ya barshi kawai,saboda na saba da yin aiki ni kadae,"
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"that's impossible,gaskiya in har ba zaki amince a ƙaro masu aiki ba,to daga yau Ni dasu jahad zamu dinga tayaki aiki,don bazaiyiwu ba kiyi ta wahala ke kaɗai,"
 murmushi kawai azmee tayi batare da tace Komai ba,
  "Aunty azmee idan akwai abunda kika kammala inaso zan fara kaiwa dining in jera,kinga na rage maki wani aikin,"
 "Ban kaiga shiryasu ba,amma sai dai idan zaki kaima Sgr nashi,sae na haɗa maki,ki kai mashi,"
 Murmushi ta saki tare da cewa"Toh,"
Shirya mata breakfast azmee tayi acikin ƙayataccen tray,bayan ta kammala,sehrish ta ɗauki tray ɗin tare da fucewa daga kitchen ɗin,
tana cikin tafiya harta kusa hayewa upstairs taji anyi mata gyaran murya abayanta,cikin sauri ta juya don taga Wanene,ganin Uncle abusufyan yasa gabanta faÉ—uwa,saboda tana kallonshi ta tunano da abunda ya faÉ—a mata a daren jiya,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.