Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
 ****************
A 6angaren su hossana kuwa saboda damuwar da suka shiga na jin cewa ya Omar É—insu na da aure gaba É—ayansu ba wanda yayi breakfast saboda damuwa, su kansu sun rasa gane dalilin dayasa suke jin kishin matar shi data kirasu a waya, abincin da jahad ta shirya masu har yayi sanyi saboda tun safe yake ajiye saman dining table babu wanda ya ta6a shi, gashi har Æ™arfe É—aya yanzu yayi na rana,Â
  A tare suke kabbara sallah bayan sun kammala suka zauna suna addu'o'i, shiru jahad tayi tana sauraron addu'ar hossana da take yi,
  "Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba na cewa ya Omar yana da mata, in ma dagaske ne ya Allah kasa ya sake ta su rabu, zuciya ta tafarfasa takeyi mun bazan iya jurewa ba........'Â
  katse ta Jahad tayi da cewa"hossana kina a hayyacinki kuwa? ya sake ta fa kika ce? Idan yana son matar shi fa?Â
 harara hossana ta jefa mata tare da cewa"waya faÉ—a maki yana sonta? Auren dole ne akayi masu, da ace yana sonta ae da bai 6oye mana cewa yana da mata ba har da ciki...'Â
   Itama jahad ɗin harar ta mayar mata tare da cewa"baki da hankali wlh,dagaske ɗin ke zararriya ce, yaya omar yana son matarshi, ke bakiji muryarta ba yarda take magana daga gani tana cikin kwanciyar hankali, kuma tana samun soyayyar mijinta tunda gashi har tana da ciki zata haifa mashi baby..........' jahad bata ƙarasa maganar ba, hossana takai ma wuyan hijabinta cakuma tana cewa"Ni ce zararriya? ɗaga kai jahad tayi alamar e,
  Bugu hossana tashiga kai mata, ganin bazata iya jurewa ba yasa suka kacame da faɗa, abu kamar wasa sai da dukkansu suka sha kuka, dama ransu a6ace yake, duk don saboda matar Omar,
  (Sehrish tayi tsiya)
tsaf ta kammala gyara mashi bedroom dinshi da toilet dinshi da falonsa duka ko'ina a kimtse tabar mashi shi, fitowa tayi ta sauko down stairs a lokacin duk sun kammala yin breakfast ɗin nasu babu kowa a falon, kai tsaye ta wuce bedroom ɗin Haroon gabanta na faduwa rass rass, ƙopar a rufe take don haka saita sanya hannu tare da yin knocking ɗinta, daga cikin ɗakin tajiyo muryarshi yana cewa"Wanene"?
  "Ni ce," ta bashi amsa cike da ƙarfin guiwa,
  buÉ—e mata Æ™opar yayi fuskar nan É—auke da murmushi, jikinshi na sanye da singlet fara tare da shorts baÆ™i,Â
 "shigo daga ciki mana," ya faɗi yana nuna mata hanya, kallon shi kawai takeyi , sa kai tayi ta shiga ciki daga tsaye ta tsaya tana kallon shi, rufe ƙopar yayi sannan ya juyo ya kalle ta yace "wlh har naji sanyi araina dana ganki cikin ƙoshin lafiya,ae nayi tunanin e warhaka kina asibitin kwance magashiyyan rai hannun Allah.....' bai ƙarasa maganar tashi ba tace"me nayi maka? Meyasa kake son kashe ni? saboda me ka bani wannan allurar?
  tafi yayi da hannunshi yana dariya, wuce ta yayi tare da samun wuri daga gefen gadonshi ya zauna yana facing É—inta yace"Ko da ace zan iya kashe kowa a duniyar nan, ni bazan iya kashe abunda raina ke so ba!!! nasan cewa ba zaki mutu ba, akwai wanda zaizo ya taimake ki shiyasa nayi hakan ! kinfiye taurin kai shiyasa na gwada maki kaÉ—an daga cikin shaiÉ—ancina, kin manta maganar da kika faÉ—a mun nacewa NAMIJI kike kallo? Shiyasa na haÉ—aki da namijin...........' Æ™arasa maganar yayi yana faman tiÆ™ar dariya, sakin baki sehrish tayi tana kallon shi. Da Æ™yar ya tsagaita da maganar tashi yana kashe mata ido yace"Yarinya taji maza,baki ban labari ba ya kuka Æ™are jiya?Â
  shiru tayi tana kallon shi kawai saboda abun yafi Æ™arfinta haroon ba Æ™aramin shaiÉ—ani bane,Â
  ta6e bakin shi yayi yana kallonta sannan yaci gaba da cewa"wannan allurar da na baki, miyagu irina suke amfani da ita, aduk lokacin da mutun yayiwa kanshi allurar nan, imanin shi gaba É—aya take cire wa, zai iya yi ma mata sama da goma sha biyar raping a lokaci guda batare da ya gaji ba tamkar engine zai dinga aiki, sannan koda ace mahaifiyarshi ce akusa dashi itama hakan ce zata faru da ita ba zai iya tantance fari ba balle baÆ™i, saboda gaba É—aya take tayarwa mutun da wata irin jarababbiyar shawa'a da kuma Æ™arfi na ban mamaki, kuma muddin a lokacin bai samu ya kawar da sha'awarnan ba, to fa zuciyarshi zata iya bugawa nan take,.......'Â
 tunda ya soma bayani sehrish ke kallon shi cikin tsananin tashin hankali har sai da yakai Æ™arshe sannan cikin sanyin murya tace"me yasa ka fita daban acikinsu ne? Saboda me kake son cutar da shi ne? idan ni nayi maka laifi saboda me laifin zai shafe shi?Â
   shu'umin murmushi haroon ya saki kafin yace"tun ina yaro nake da son yin mugunta, ni ko dariya ban cika yi ba sai in anyi abun mugunta sannan take zuwa mun, burina kawai naga kowa cikin masifa da tashin hankali,natsani inga ana ta rayuwar farin ciki mai É—aurewa, wannan ne dalilin dayasa nakeson in kawo canji acikin gidan nan,". Hankali kwance haroon ke kora mata bayani batare da nuna alamun wasa ba,Â
  tuni taji idonta sun ciko da kwalla cike da takaici tace "tausayinka nake ji ! kana bani tausayi saboda kai abun tausayi ne, ban ta6a tunanin cewa a jinin abba za'a samu mai irin waÉ—annan mugayen É—abi'un da halayen irin naka ba, saboda me yasa kai ba zaka yi koyi da sauran ba? ka zama mutumin kirki tamkar sauran"?Â
  tasowa haroon yayi daga zaunen da yake ya ƙarasa dab da inda take a wannan karan fuskarshi babu wasa acikinta yace"kina so in shiryu ne? In zama mutumin kirki?
  ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
 Murmushi haroon yayi kafin yace"kece mutun ta biyu, da kikayi mun fatan shiriya arayuwata, sai dae kash hakan bazai ta6a yiyuwa ba sehrish ni ba cikakken mutun bane kamar yarda kike tunanin....................' a wani irin firgice sehrish ta É—ago tana kallon cikin idanunshi fuskarta cike da tsoro tace"kana nufin kai ba mutun bane"?Â
  dariya ya ɗanyi kafin yace"kona faɗa maki ba zaki yarda ba, amma bari na sanar dake wani abu da baki sani ba, ni da kaina na turo marshal Omar ɗakin sgr domin ya taimake ki ! kuma ni ne nan na hana ki furta sunana agaban Omar, na shaƙe maki maƙoshinki na hana sautin fita daga bakin ki, shin bakiyi mamakin taya akai duk nasan da wannan ba !!!!!!!!!!!
  Zazzare ido sehrish tayi gabanta na faɗuwa, tuni zufa ta soma tsattsafo mata, ja da baya da baya tadinga yi tana kallon shi.....
 dariya sosai haroon yayi kafin yace"Shiyasa nace ki nemi tsari daga sharrina wlh ni shaiÉ—anin aljani ne ba mutun ba..........'Â
 tunkan ya ƙarasa maganar tashi Da gudun gaske sehrish ta juya tare da buɗe ƙopar ɗakin nashi ta fuce ji kake garam !!!! Ƙopar ta datse,
  Fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikin shi, daga bisani kuma ya ɗan tsagaita da dariya tare da cewa "Yarinyar tana da kyau, shiyasa na tsoratar da ita saboda inga kyawawan idanuwan nan nata masu kashe mun zuciya," ya furta tare da kai hannun shi saitin zuciyarshi yana faman sakin murmushi...............😳 tashin hankali anya kuwa haroon 👹😈
 Â
 Ko kallon gabanta ba tayi saboda gudun da take yi gaba É—aya ta gama firgita da haroon, bata yi wani aune ba ta faÉ—ama junaid wanda ya nufo part din nasu, aikuwa gaba É—aya suka faÉ—a Æ™asa a manne da juna, atare zuciyoyinsu ke bugawa, musamman sehrish yana jin yarda zuciyarta ke faman bugawa da Æ™arfi da Æ™arfi, sun jima a haka kusan 8 mins sannan junaid ya ambaci sunanta "Sehrish,"Â
  lamo tayi a jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya sai da ta samu natsuwa sosai sannan ta É—ago daga jikinshi,tayi gefe guda zaune dirshan tana kallon shi, tasowa yayi daga kwancen da yake yana faman sakar mata murmushi, tun safe yakeson ganin ta amma basu haÉ—u ba sai yanzu, shima zama yayi suna fuskantar juna da ita, wankan jeans da t shirt red colour ne ajikinshi, sai faman Æ™amshi yake yi,Â
   "Me ya faru ne naga kina ta tiÆ™ar gudu kodai motsa jiki kike yi ne? ae muna da wurin gym acikin gidan nan,'Â
 Ya faɗi yana kallonta, tayi mashi zuru da ido,
  Ganin bata da niyar yin magana yasa shi cewa "Labari mai daɗi "! cike da zumuɗi tace "dagaske ? Wani irin labari ne wannan,
 "Mafarki nayi jiya,"Â
"Me ya faru acikin mafarkin"? ta tambaye shi cike da son ji,
  gyara murya yayi tare da cewa" mafarki nayi da wani narkeken zaki acikin wani Æ™urmin daji ya biyo ki da gudun gaske, kamar zaki tashi sama haka kika dinga gudu kina ihu, kinsan waye ya cece ki a wannan lokacin"? Ya jefa mata tambaya, hankali tashe tace "A'a," Æ´ar hararar ta yayi tare da cewa"Ni ne nan, nazo da suffar jemage na É—auke ki da fika fiki na mukayi sama can cikin gajimare...........' ganin yarda sehrish ta fashe da dariya yasa shi dakatawa da labarin yana kallonta, nuna shi tayi ta yatsa tana cewa"junaid kaji tsoran Allah, jemage fa kace? taya jemage zai iya É—aukar mutun ? sannu malam fesal ka feso mun Æ™arya,Â
 gaba ɗaya suka sanya dariya, ba ƙaramin nishaɗi junaid ya sanyata ba duk da fargabar da take ciki, sun jima a zaune ƙasa suna fira, kafin daga bisa ni suka tashi, shi ya wuce mosque ita kuma ta wuce bedroom ɗinta saboda tayi sallar itama,``The father Of Soldiers```
Â
Story &Â Â WrittenÂ
    ByÂ
   Hafsat Bature
**********
zaune take agaban mirror ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar material blue colour mai kyan gaske, rigar tabi shape ɗin jikinta daga can ƙasa yayi ƴar baza tamkar mermaid haka shape ɗin ya bada,hoda ta ɗauka tana shafa ma fuskarta, bayan tagama ta ɗauki jan baki red colour ta murza, ba ƙaramin kyau tayi ba, set na brushes ɗinta ta ɗauko ta gyara eye brows ɗinta,bayan ta kammala gyara gashin giran, ta ɗauki ribbom ɗinta data ajiye saman mirror ɗin, tattara sumar kanta tayi tana kiciniyar ɗaure gashin amma sam tagaza saboda yawan da yayi,ita kanta tayi mamamkin yarda gashinta yake toho,ba ƙaramin tsayi yayi ba ga yawan gaske dami guda dashi,bakomai ya jawo hakan ba face mayukan da take amfani dasu na gyaran gashi sun amshi kanta sosai,
  Sakin gashin tayi ya tarwatse a bayanta,saboda gajiyar da tayi da ruÆ™on shi,hannu takai cikin jerin perfumes dinta ta dauki kwalbar turaren flower bomb wanda junaid ya É—aukar mata a lokacin da suka je siyayya saboda shima yana da irin shi, shiyasa ya haÉ—a mata dashi don suyi anko, feshe jikinta tayi da turaren ko'ina ya ji, nan take daddaÉ—an Æ™amshinsa ya gaure ko'ina na É—akin gaba É—aya,mayar da kawalbar turaren tayi bayan ta kammala fesa wa, sannan ta zuba ma madubin ido tana kallon fuskarta,fuskar sgr ta dinga gani acikin mirror É—in,nan take ta tuna lokacin da ta watsa a guje zata bar É—akin ya biyota da gudun gaske tare da ruÆ™ota a jikinshi,tafin hannunta tasa tare da rufe fuskarta tana faman sakin murmushi,sake tunawa tayi da lokacin da ya yage rigar jikinta kai tsaye ya afka mata,nan take taji wani irin sanyi da kasala sun rufar mata,gaba É—aya fa sehrish ta shiga yanayi cike da shauÆ™i take tariyo duk wani abu da ya faru da ita a daren jiyan ta shagala sosai, taji knocking daga waje, muryarta cike da kasala tace"Wanene"?Â
.muryar Azmee tajiyo tana cewa"Auntynki ce," jin hakan yasa sehrish tashi tare da ƙarasawa ta buɗe mata ƙopar,tana a tsaye jikinta sanye da jallabiya ta mata maroon colour, ta yafa mayafi akanta ba ƙaramin kyau tayi ba,
 sakin baki tayi tana kallon Sehrish kafin tace"Masha Allah, irin wannan kyau haka? sai kace sabuwar amarya,kinyi kyau sosai,"murmushi kawai sehrish ke saki,
  matsa mata hanya tayi tare da cewa"Aunty azmee ki shigo daga ciki mana,"Â
 "A'a basai nashigo ba, dama nazo naji ya kuka Æ™are da Omar?ina fata kin sanar dashi gaskiya?Â
  shiru sehrish tayi tana tunanin amsar da zata bata,ranta ne ya bata cewa kawai ta amsa mata da eh,saboda tana da tabbacin cewa muddin ta faÉ—a mata cewa takasa furta sunan haroon agaban Omar to tabbas azmeen zata iya cewa zata sanar dashi ita da kanta,idan kuma hakan ya faru to tabbas itama azmeen zata fuskanci irin abunda sehrish ta fuskanta wurin Furta sunan Haroon,kuma bazata so hakan ya faru ba don ba Æ™aramin raÉ—aÉ—i taji ba,.Â
 Sam ta tafi duniyar tunani taji muryar azmee ta katsa ta da cewa"Lafiya kuwa naji kinyi shiru baki ban amsa ba"?.Â
  cikin sauri sehrish tace"aunty azmee na sanar dashi gaskiya kuma yace zaiyi bincike akan haroon É—in,"Â
 "Kin tabbata"? ɗaga kai sehrish tari alamar eh,
 Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"kayan sunyi maki kyau sosai Allah," murmushi sehrish tayi tana sunnar dakai,
  Azmee ta kuma cewa"Munyi magana da junaid akan kayan nan naki da aka kai É—inki,yace mun tailor din ya kammala É—inki shi zaije ya amso maki kayan," cike da farin ciki sehrish tace"ngde sosoe aunty azmee na,"Â
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.