Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Acan kuwa,bayan Azmee tayi ma sgr jagora har izuwa É—akin sehrish,ita tafara shiga sannan ya bi bayanta har izuwa wurin gadonta,karo na farko kenan da Sgr yafara shiga É—akin Sehrish,lokacin ne yama san inda dakin yake,tsayawa yayi daga tsaye yana kallonta,sae faman juyi takeyi atsakiyar gadon gaba É—aya tagama fita hayyacinta saboda raÉ—aÉ—in ciwon cikinta,
 Hannu azmee tasa tare da janyo bargo ta lullu6e mata jikinta,ganin yarda surar jikinta ta fito sosai,
  "Wane kalar ciwon ciki ne takeyi"?yayi maganar ba tare daya kalli azmee ba,yana da tabbacin cewa menstruation ne,amma yafiso yaji daga bakinta,
 "Na al'ada ne,"azmee ta bashi amsa,
 "Okey,"ya ambaci hakan tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,
 Komawa azmee tayi tare da zama daga gefen sehrish tana kallonta gwanin ban tausayi,Ba ƙaramar wahala tasha ba,ta jigata sosai,ta wani 6angaren kuma taji daɗi da Sgr ne zai dubata,don tasan cewa zata samu kyakkyawar kulawa awurinshi,zaiyi mata abunda ya dace ne,"
 15mins da fitar shi,sae gashi ya dawo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da Allura har ya ɗura ruwan allurar acikin sirinjin,
  Ganin shi yasa azmee mikewa daga zaunen da take gefen gadon ta bashi wuri don ya samu damar yi mata allurar,
 Zama yayi daga gefen gadon tare da ruƙo hannun sehrish da ta fito dashi daga cikin bargon da azmee ta rufa mata ajikinta sae faman hargowa take tana ambaton cikinta,
  Yana ƙokarin tsira mata allurar,ta ware idanunta sosai kai tsaye suka sauka akan Syringe ɗin dake hannunshi,duk da bata acikin hayyacinta amma ta gane cewa Allura ce fa za'ayi mata,
 a firgice sehrish ta fusge hannunta tare da yin wurgi da bargon da azmee ta yafa mata,gefe guda ta jefar dashi,matse kanta tayi ajikin headboard na gadon tana faman shesshekar kuka tana cewa"banaso!dan Allah ku kyaleni kada kuyi mun allura,"gaba daya duk tabi ta firgice dama ta tsani allura arayuwarta mugun tsoranta take ji,
   sanin cewa Sgr yana da bad temper bazai iya jure koke-koken da sehrish keyi mashi ba,muddin taƙi tsayawa zai iya kwashe ta da mari,don ta dawo dai dai,
 Cikin sauri azmee tace"Zan iya ruƙe maka ita?
 "E" ya bata amsa ataƙaice,
Wucewa saman gadon azmee tayi tare da rurruke sehrish,aikuwa a gigice sehrish ta shiga kokawar kwace kwanta hada gartsa mata cizo a hannunta,
   Cire hannunta tayi daga ruƙon da tayi ma sehrish,saboda taji zafin cizon da tayi mata,
 Ganin haka yasa sgr bata Umarnin ta fita daga ɗakin,
  Saukowa azmee tayi daga saman gadon,tare da kama hanya ta fuce daga cikin dakin,
 A waje ta samu junaid atsaye sae faman zagaye yake yi a wurin ɗakunan nasu,bawan Allah duk ya rasa natsuwarshi tunda yaji cewar Sehrish bata da lafiya,
 "Junaid," jin an ambaci sunanshi yasa shi yin firgit ya juya yana kallon azmee dake tsaye a kopar dakin,
 Ƙarasawa yayi wurinta fuskarshi ɗauke da damuwa yace"Aunty azmee wai meya faru da sehrish ne?ina taje ne?duk nabi na ruɗe wlh,bansan ta yadda akai ta sanya ƙafa tabar gidan nan ba,nifa dakaina na ɗaukota daga school na kawota gida,"
 ruƙo hannunshi azmee tayi taja shi daga dan gefe suna fuskantar juna tace"Junaid ka kwantar da hankalinka,ba abunda ya faru da sehrish,stomach pain ne kawai kuma insha Allah zata ji sauƙi ne,sannan maganar fitar sehrish daga cikin gidan nan,kada kayi confusing kanka,ka manta da wannan kawai,komai ya wuce,"
 ajiyar zuciya ya shiga saukewa,har cikin ranshi yaji daɗin bayanin da azmee tayi mashi,
 "Yanzu kaje ka kwanta mana,zuwa da safe in yaso sae kazo ka dubata ko"?
 cike da shagwa6a yace"Aunty azmee kona koma ɗaki bazan iya bacci ba,in har ban sanyata acikin idanuna ba,'
 Murmushi azmee tayi tace"ummm romeo kenan shugaban ƴan soyayya,dama tunda na ganka nan tsaye nasan cewa abunne ya motsa,"
 Sunnar da kai ƙasa junaid yayi yana faman sakin murmushi,
   A nan suka tsaya suna cigaba da yin fira atsakaninsu,janye mashi hankali azmee ta dinga yi saboda ta lura da yadda yake firgita duk in yaji sautin kukan sehrish,daƙyar tasamu junaid ya wuce bedroom dinshi itama ta wuce nata ɗakin,
 suna barin wurin hayaam ta fito daga ɗakinta,cikin sanɗa take tafiya harta ƙaraso wurin kopar ɗakin sehrish,anan ta tsaya tare da jingina kanta ajikin ƙopar ta kasa kunnanta tana sauraran kukan da sehrish keyi,duk atunaninta ita kaɗaice acikin ɗakin take kuka,hakan yasa taji daɗi acikin ranta har tana cewa"Shegiyar Allah yasa ta mutu kowa ya huta,wlh bazan shiga in taimaketa ba,koda ciwon zai kashe ta,
acan cikin ɗakin kuwa duk yadda sgr yaso sehrish ta tsaya yayi mata allurar abun ya faskara,taƙi bashi haɗin kai,sae faman yawo take mashi da hankali,wannan ne yasa shi fusata har ya daka mata tsawa,wannan tsawar da sgr ya daka ma sehrish yasa ta dawo cikin hayyacinta sosai,waro ido waje tayi hankalinta a matuƙar tashe take kallon sgr,abun kamar a mafarki take kallonshi,wai dama shine!taya akai ya shigo ɗakinta?
a tsananin tsorace take binshi da kallo,jallabiya ce fara ajikinshi mai gajeran hannu,hakan ya bayyana damtsen hannun nan nashi,
  zazzare ido tashiga yi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,
 Matsawa sgr yayi kusa da ita,suna facing din juna face to face,a hankali yake bin fuskarta da kallo yayin da itama take ƙare ma tashi kallo,har lokacin kokwanto takeyi anya shine da kanshi ya shigo ɗakinta,Sgr sukutum da guda yau a bedroom ɗinta zaune gefen gadonta,a kusa da ita?
 Hmmmmm ina labarin Hayaam dake la6e ajikin ƙopar ɗakin tana sauraron kukan Sehrish,ae tun lokacin da taji muryar sgr ya daka ma sehrish tsawa,jinjina kai ta shiga yi tana faman sakin huci kamar wata zakanya saboda tsabar 6acin rai da takaici,acikin ranta tashiga cewa"lallaima yarinyar nan,wato harta samu matsayin da sgr zai dinga takawa da ƙafafunshi yana shiga ɗakinta,'
 ɗagowa tayi tare da aza hannunta asaman kanta tana cewa"nashiga uku ni yau hayaam bansan ya zanyi da yarinyar can ba,tana shigar min gonata!tabbas dole nayi wani abu akanta,bazan ƙyaleta ba tayi nasara akaina ba,
 Tana cikin wannan zancen zucin nata ta jiyo muryar sgr yana magana daga cikin ɗakin,cikin sauri ta kasa kunne tana sauraron me yake ce ma sehrish ɗin,
  "Bana son wannan koke koken da kikeyi mun,kamar zan rabaki da ranki ne,"!.Â
 tsit Sehrish tayi tana sauraranshi,yayin da take bin pink lips ɗinshi da kallo,
 Cigaba da magana yayi anatse yace"idan kika natsu,ba da zafi zan maki ba,a hankali zanyi maki,batare da kowa ya ji mu ba,"
  tashin hankali tunda hayaam taji wannan zancen da Sgr yakeyi ma sehrish nan take taji gabanta ya faɗi rass,zullumi ta shiga yi gabanta na faduwa,duk atunaninta wani mummunan abunne sgr da sehrish ke aikatawa,gaba daya ta rasa natsuwarta,kamar ta fada cikin ɗakin taga me suke aikatawa haka take ji aranta,zuciyarta sae faman azalzalarta takeyi tana tunzurata akan ta shiga taga me sukeyi,
 Yanayin yarda sgr keyi mata magana cikin sanyin murya,yasa taji wani irin yanayi atare da ita,da kanta ta miƙa mashi hannunta don yayi mata allurar,
 Hannunshi yasa tare da ruƙo wrist din hannunta,sannu a hankali ya zura allurar a cikin jijiyar hannun nata,lokacin da tsinin allurar ya ratsa cikin jijiyar,a ɗan razane sehrish ta saki ƴar ƙara tare da runtse idanunta tana faman cizon la66anta,
 a hankali sgr ya ɗago da blue eyes ɗinshi yana kallon fuskar sehrish,zuba mata ido yayi yana kallon eye lashes ɗin idanunta masu tsayin gaske,kafin ya mayar da idanun nashi akan la66anta dake ta faman kerma,tana ɗan cizon gefensu da Teeth ɗinta,
 gaba daya ya gaza control ɗin kanshi,har ya gaza janye idanunshi daga kallon la66anta da yake yi,ba ƙaramin yanayi ta jefa shi ba,cos she looks so sexy a wannan lokacin komai tayi bashi sha'awa yake yi,
 siraran hawaye ne suka shiga gangarowa daga cikin idanunta,batare da saninshi ba yakai hannu zai share mata hawayen,buɗe idanuwan da tayi ne yasa shi dakatawa tare da janye hannunshi,
ya kawar da kanshi gefe guda a lokacin ya kammala yi mata allurar,
  tayi danasanin buɗe idanuwanta da tayi,taso ace ya sanya hannayen shi ya share mata hawayen,ko ba komai zata ajiye wannan ranar a matsayin ɗaya daga cikin ranakun da suka kafa tarihi a rayuwarta,
  Ganin ya miƙe tsaye tare da kama hanyar fita daga cikin bedroom ɗin nata yasa tayi saurin cewa"ngd da taimakon da kayi mun,"
 Batare da ya juyo ya kalleta ba yace"get well soon"
Yana ƙarasa maganar tashi yasa hannu ya ruƙe handle ɗin ƙopar zai buɗe door ɗin ɗakin,jin motsin shi yasa jiki na rawa hayaam ta watsa da gudu izuwa cikin bedroom ɗinta,
Upstairs ya nufa ya wuce part É—inshi a wani irin yanayi ya faÉ—a saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke kallon saman ceiling É—in É—akin nashi,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.