Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Gaba daya duk sun zazzauna saman kujerun yayin da table din ke shaqe da kayan ciye ciye iri²,Abusufyan tare da Abban nasu sae junaid suna a zaune wuri daya,Ayaan da jahan da kuma fawan suna zaune suma a wuri daya suna cin abincinsu,Irfan da jabeer sae khaleed suma suna zaune a table daya,
Kanal yousouf ne ya buɗe masu taron da addu'o'i,kafin su fara kulu washarabu hani'an,sunyi haje haje da naman kaji,farfesu iri iri da sauran kayan maƙwalashe,
,kowa ya mayar da hankalinshi akan abincin dake gabanshi,
 "Wai ni ina Rafayet da Omar ne?naga kowa amma bandasu,"Abusufyan ne yayi ma Abba maganar a yayin da yake ɗaukar cup na lemu,yakai bakinshi yana kur6a,
 "Ina tunanin suna ciki suna shiryawa,kasan su fa manya ne nasu wankan ba irin namu bane,nasan shiyasa suka jima aciki basu fito ba,"a cewar abbansu,
"Naga alama,amma ni ko ina so na tambayeka yaya,wai har yanzu Sgr da Omar basu fara soyayya bane "?yayi tambayar yana kallonshi,
 Murmushi Abba ya ɗanyi kafin yace"Omar dae ya sanar dani cewa akwai yarinyar da yake so,kuma ashirye yake daya aureta,amma shi rafayet har yanzu fa babu wani sauyi yana nan yadda kasan shi,amma kwanan nan na fuskanci kamar akwai wani abu atsakaninshi da yarinyar gidan nan,wadda na faɗa maka cewa tana taya Azmee aiki,kamar akwai soyayya atsakaninsu,duk da dae bani da tabbacin hakan,"
 tunda suka soma magana junaid baisan me suke tattaunawa ba,saboda hankalinshi na can wurin tunanin abu biyu,rishi ɗinsa da kuma zuwan mommynsu a takure yake,gaba ɗaya ya gaza samun natsuwa saboda ya kwallafa rae akan zuwan nata,
Abusufyan yace"yanzu me ka yanke shawara agame dasu ne?zaka tunkari Sgr da maganar yarinyar ne ko kuwa"?
"A'a,bana tunanin cewa zai amince cewa yana sonta harma ya yarda ayi auren kasan halin shi,yanzu dai akwai wani shiri da nakeyi dama zuwanka kawai nake jira,nan da sati mai zuwa zan sanar dakai insha Allah,"
Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"Allah ya kaimu lafiya,"
Abba ya amsa mashi da Ameeen,
Juyawa abbansu yayi tare da kallon junaid ya ambaci sunanshi,
 Firgit junaid yayi tare da aza idanunshi kan abban nasu yace"Abbana,"
..murmushi sukayi gaba É—ayansu,Uncle abusufyan yace"junaid kodae ka fara soyayya ne?tun É—azu muke magana amma hankalinka na'a wani wuri,"
 Murmushi ya ɗanyi tare da sunnar da kanshi ƙasa yana kallon plate dake ajiye gabanshi shaƙe da Chips,tun da Azmee ta zuba mashi bai ko ta6a shi ba,
 "Junaid naji kayi shiru kodae dagaske ne abunda Uncle ɗinku yace ka fara soyayya"?Abbansu ne yayi maganar cike da zolaya yana kallonshi,
 Duk kunya tabi ta kama junaid,ba wai abban nasu yake ji ma kunya ba,uncle ɗinsu yake ji ma kunya,don ta Abbansu har zancen aure suna yi dashi in wasan nasu ya motsa,
 yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,wayar shi ta shiga ringing,jikinshi na rawa ya zura hannunshi a aljihu ya curo wayar yana duba sunan mai kiran nashi,private number ya gani wato anyi hidden ɗin numbar,kallon abbansu yayi tare da cewa"Abba zan amsa waya,"
amsa amshi yayi da cewa"okey,amma kada ka jima,muna jiranka,don bamu gama hotunan ba,"
 Murmushi ya saki tare da miƙewa yabar wurin,sae da yayi nesa dasu sannan ya ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanshi yana jiran jin wanene ke kiran nashi,
 Wata sanyayyar murya yaji ta karaɗe kunnan shi da cewa"babyn abbanshi kana ina ne"?
 Tunani ya shiga yi kodae mommynshi ce don haka yace"ina a gida ne,"
 Matar tace"Idan ba damuwa kazo Airport kadauke ni,na ƙaraso Nigeria amma banaso kowa yasan da maganar,kai kadae kawai nakeso kazo ɗaukana,Kada ka bari kowa ya biyo ka"
 da ƙarfi junaid ya ambaci sunan mommy fuskar nan tashi cike da farin ciki yace"mommy am coming right away"
 Matar tace"okey,idan ka fito daga cikin gidan ka sanar mun,"
 Cike da zumuɗi ya amsa mata da toh,sannan jiki na rawa ya katse kiran tare da zura wayar a aljihun shi,
 Gaba ɗaya ya gaza rufe bakinshi saboda tsabar farin ciki,juyawa yayi yana kallon ƴan uwanshi dake zazzaune kowannansu fuskarshi ɗauke da farin ciki,aranshi yace"kodai na sanar masu cewa mommy ta ƙaraso?kuma dae tace kar na faɗama kowa,gaskiya bazan faɗa masu ba,zan basu mamaki ne nasan in suka ga mommy zasu yi murna sosai,amma kuma inason na sanya rishi a idanuna kafin nabar gidan nan,bari nayi sauri naje naga wankanta na yau,
 Yayi maganar tare da nufar corridorn ɗakinsu sehrish da sauri da sauri ya ƙarasa kopar bedroom ɗin nata,
 A lokacin tana acikin bedroom din nata sae faman zagaye takeyi,tarasa ya zatayi ta fita,kunya take ji su ganta da kwalliyar jikinta,
Jin kwankwasa ƙopar ɗakin nata yasa ta cewa"wanene,"
daga waje junaid ya amsa mata da cewa"Mijinki ne insha Allah,"
 Murmushi ta saki tare da cewa"ka samu iznin shigowa ciki,daga matarka insha Allah,"
 tura ƙopar yayi tare da sanya ƙafa ya shiga cikin ɗakin,koda yayi arba da sehrish nan take yaji gabanshi ya faɗi,kokwonto ya shiga yi yana tambayar kanshi Anya wannan sehrish ce kuwa?
 matsawa kusa dashi tayi tace"meya faru junaid naga ka toge anan?
 "Reesh,kinyi kyau Over,"cikin sanyin murya yayi maganar,don ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,
 Ƙayataccen murmushi ta sakar mashi tare da cewa"saboda kai nayi wannan kwalliyar,launin lips dinka red colour ne,shiyasa nima na sanya jan lace don inyi anko da kai,to ya kaga wankan"?
tayi maganar tare da jujjuya mashi bayanta don ya kalla da kyau,aikuwa ba ƙaramin ruɗashi tayi ba,gaba daya yabi ya susuce,
Kamar yakai mata runguma haka yaje ji,amma ba halin yin hakan jikin shi sae faman kerma ya keyi,
juyawa tayi tare da nufar bedside drawer dinta,ta É—auko wayarta tare da dawowa saitinshi ta É—aga wayar tare da cewa"ka shirya in É—auka?'tayi maganar tana jiran jin amsarshi,
Jin hannunshi ta gefen waist dinta yasa ta ɗan razana kaɗan,sosai ya ruƙo qugunta tare da kwantar da kanshi saman kafaɗarta yace"ki ɗauka,"
Zuba mashi ido tayi ta cikin camera É—in tana kallon fuskarshi,hakanan ta dinga jin zuciyarta nayi mata wani irin bugu,muryarta akasalance tace"junaid ka buÉ—e idanunka,taya zan É—auka dakai ido a rufe"?
Murmushi yayi tare da buɗe idanunshi yana cewa"Reesh,ƙamshin turaran nan naki,kashe mun jiki na yake yi,ba kiji yarda nake ji ba,don Allah reesh,kada ki guje ni kinji"?
Martanin murmushin ta mayar mashi sannan tace"junaid banda hankaline da zan guje ka?angaya maka kai irin mazan da ake gudu ne?kai fa na musamman ne junaid,tun farkon ranar dana fara zuwa aiki gidan nan,dakai nafara cin karo,a lokacin da nayi arba da wannan kyakkyawar fuskar taka mai ɗauke da wannan tsadadden murmushin,lokaci guda na rasa samun natsuwa,kasan Allah junaid da ace siyar da wannan murmushin naka kakeyi da ba ƙaramin ciniki zakayi ba Allah,"
Fashewa da dariya junaid yayi saboda jin kalaman sehrish akanshi,ba ƙaramin hura mashi kai tayi ba,kuma ta samar da farin ciki acikin zuciyarshi,
É—aukar hoton sehrish ta shiga yi,style iri iri suka shiga yi ita da junaid,hada wanda ya manna mata kiss a gefen fuskarta,da kuma wanda ta lotsa yatsanta acikin dimple dinshi,hotunan sunyi kyau sosai,
Sae da suka kammala hoton sannan ta lura da zoben diamond ɗin dake hannunshi,sae faman ƙyalli yake yi,
Waro ido waje tayi alamar mamaki tace"wow junaid wannan fa,waya siya maka shi!"
"Mommy azeema ce ta bani shi,dama É—azu na sanar dake cewa zan nuna maki gift din da takawo mun,to itace wannan,'
Ya ƙarasa maganar yana nuna mata zoben da Wrist watch din,
"Junaid sunyi kyau wlh,musamman daya kasance kaine ka sanyasu,"
"Thank u reesh,sunyi mun kyau amman idan ke kika sanyasu sae sun fi yi maki kyau,bari na ciro maki su ki sanya,nafison su kasance a hannunki,"
cikin sauri tace mashi"no junaid that's impossible,Auntynku azeema ce ta baka shi,muddin ta neme shi a hannunka bata ganshi ba zata nemi jin ba'asin inda ka kai su,kuma ma in banda abun ka junaid wannan ae irin naku ne!kamar diamond ne fa,nida ko zoben azurfa ban ta6a sanyawa a hannu ba,balle diamond!
Kafin ya buɗe baki ya bata amsa wayarshi ta shiga ruri,nan take ya tuna da abunda mommynshi ta sanar mashi na cewa ta ƙaraso nigeria tana a Airport yaje ya ɗaukota,
Jiki na rawa yayi ma sehrish sallama tare da fucewa daga cikin bedroom É—in,
Junaid bai sanar ma kowa ba,ya shige motarshi tare da janta yabar gidan gaba ɗaya,ya miƙi hanyar zuwa airport din cike da zumuɗin son ganin Mommyn tashi.
💋Boss Bature💋
A hankali sehrish ta sanya kafarta tare da fitowa daga cikin bedroom ɗin nata,a natse take tafiya yayin da takalman kafarta ke bada sauti kwas,kwas duk in ta takasu ƙasa,cike da fargaba ta tunkari babban falon gidan,
Jin takun takalmanta ne yasa matasan dake zaune acikin falon dawo da hankalinsu akanta,koda su kayi arba da sehrish,lokaci guda sukayi tsit yarda kasan mutuwa ta gifta,babu mai magana acikinsu ba don komai ba,sae don kallon da suka bita dashi,
Abbansu ne yayi ƙoƙarin cewa"Masha Allah my daughter,irin wannan kyau haka kamar sarauniyar kyawun duniya"?yayi maganar fuskarshi ɗauke da murmushi,
Ita ma murmushin ta shiga sakar mashi tare da ƙarasawa wurin table dinsu don ta gaishe dashi,a lokacin Abusufyan yabar wurin saboda kiran wayar da akayi mashi,yaje ya amsa kiran ne,
"Ina yini Abba,"
Lafiya lou daughter,tun É—azu nake jiran fitowarki amma ban ganki ba,har azmee na tambaya ta sanar dani cewa kina nan zuwa,
Ya ƙarasa maganar tare da cewa"kinyi kyau sosai,da ace ƴa'ƴana zasu bari dana yi ta biyu dake......'yayi maganar cike da zolaya yana satar kallonsu fawan da suka ƙure ta da ido suna kallonta,koda suka ji abunda Abban nasu yace nan take suka ɗaure mashi fuska alamar basu son zancen,hakan ba ƙaramin dariya ya bashi ba,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.