Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Atare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da suka shaida cewa junaid ne,sai faman murza idanunshi yake yi da hannunshi,da alama magagin bacci ne ya shigo dashi,hakan ya basu tabbacin ba lallai in ya fahimci komae ba,
  cikin sauri Jahan yace"junaid tun yaushe kake anan?me kake yi har yanzu baka yi bacci ba"?Â
 Cikin shagwa6a yace"nima bansan ya akai na shigo ba,dan Allah kutaimaka mun ku kaini ɗakin abbanmu in kwanta,wurin shi nake son zuwa,"
 Shu'umin Murmushi haroon yasaki yana kallon shi,
 ganin yarda yake binshi da kallo yasa su twins saurin ruƙe hannun junaid suka fuce dashi daga ɗakin,
  "Ayaan kaje kawai ka kwanta,ni bari nakai shi ɗakin Abban namu,"
Amsa mashi yayi da toh,sannan ya wuce bedroom É—insu,
 Shi kuma jahan zuƙunnawa yayi tare da ce mashi"ka hau na goya ka karka faɗi,"
  daddagewa junaid yayi ya haye bayanshi tare da ƙanƙame shi,sannan jahan ya miƙe ɗauke dashi abayansa ya wuce bedroom ɗin Abban nasu,
  A hankali ya tura ƙopar bedroom ɗin Abban nasu,yana kwance sai faman sharar bacci yake yi asaman royal bed ɗinshi,shiga da junaid ciki yayi a hankali ya sauke junaid saman gadon daga gefen abban nasu,
   gyara kwanciya junaid yayi tare da rungumo Abban nasu da hannunshi sannan yace ma Jahan"thank u,"
 murmushi jahan yayi ba ƙaramin burge shi yayi ba,sam junaid bashi da wata damuwa,sai yaji dama shine ke irin rayuwar shi,
  "Sleep well," ya furta tare da juyawa ya fuce daga bedroom ɗin yana sauke ajiyar zuciya,ɗakinsu ya koma lokacin daya shiga a kwance ya samu Ayaan har bacci yayi awon gaba da shi,shima wucewa yayi tare da haurawa saman gadon ya kwanta daga gefenshi,
Yaushe rabon da suyi bacci irin na daren nan harsun manta,saboda fargabar haroon kullum da damuwarshi suke kwana,yau dae sun huta ma rayuwarsu tunda sun sallame shi,
A 6angaren haroon kuwa tun bayan da suka fita ranshi ya raya mashi cewa tabbas akwai alamar tambaya game da zuwan junaid bedroom É—inshi,saboda tun da yake junaid bai ta6a faÉ—owa É—akinshi ba irin haka,duk irin magagin baccin da junaid yake yi bai ta6a zuwa É—akin shi ba,amma sai yau kwatsam zai faÉ—o mashi É—akin shi adai² lokacin da suke tattaunawa dasu twins kuma? Anya ba turo shi akayi baâ?
  zama yayi daga gefen gadon nashi yana tunani,dakyar ya iya tashi yakai hannu ya kinkimi jibgegiyar jakar kuɗin,wuri yayi mata acan cikin ɗakin nashi ya 6oyeta,
  Sannan ya koma tare da hayewa saman gadonshi ya kwanta,
   *********************
Washe gariÂ
A hankali ya buɗe idanunshi da su kayi mashi nauyi saboda bacci,hannu yasa tare da yaye blanket ɗin daya lullu6a dashi,miƙa hannu yayi tare da ɗaukar wayarshi dake ajiye saman bedside drawer dinshi,missed calls ya gani nasu hossana da jahad,tashi yayi daga zaune yana kallon screen ɗin wayar tashi,jiya yaso yaje ya duba su amma bai samu time ba,
  danna musu kira yayi tuni tashi ga ringing,
 A lokacin Jahad ce acikin falon zaune saman 2 seater tana ta jiran kiranshi,hossana kuwa tana can tana sharar bacci,
  har ta fidda ran cewa zai kirasu saiga kiran nashi ya shigo,cikin sauri ta miƙe ta nufi telephone ɗin tasa hannu ta dauka tare da karata a kunnanta,
  Cikin sanyin murya tace"Assalamu Alaikum ya Omar an tashi lafiya,"
 murmushi yasaki tamkar yana agabanta yace"lafiya lou Alhmdlh,nayi laifi ko?jiya banzo na duba ku ba,ayi mun afwa ina busy sosai,amma kuna araina,"
  "Babu komai ya Omar,dama mun damune akan rashin zuwan naka,kuma mun kira wayarka jiya da safe,baka a kusa sai dai matarka Aunty zainab ta É—aga kiran,"Â
  "What!matata kuma? Wacece kuma aunty zainab?pls explain to me ni bangane me kike cewa ba,"
  murmushi jahad tayi tare da cewa"Ya omar meyasa ba ka sanar damu cewa kana da aure ba?baka so mu sani ne?
 Sam Omar baisan inda zanjen nata ya dosa ba,
  "Jahad nifa bansan me kike cewa ba! Wacece kuma matata?
 kafin jahad tace wani abu,sai ga hossana ta fito da saurin gaske jikinta sanye da kayan bacci,tana ƙarasowa tasa hannu ta kar6i telephone ɗin tare da karata a kunnanta cikin shagwa6a tace"eh mana ya omar ashe kana da aure,jiya da safe mun kira wayarka,mace ta ɗaga kiran tace mana kai mijinta ne kuma baka a kusa,sannan kuma tace mana tana ɗauke da juna biyu,kuma sunanta zainab amma kana kiranta da Hayaty,"
  tunkan ta ƙarasa maganar Omar yashiga 6a66aka dariya,natsuwa su kayi gaba dayansu suna sauraron sautin dariyarshi,
 "Ya omar kayi shiru baka ce komai ba," muryar hossana ce ta katse mashi dariyar tashi,daÆ™yar ya tsagaita tare da cewa"Am sorry na fahimci abunda kuke cewa,bazan iya yi maku bayani anan ba,insha Allah bayan na kammala breakfast dina zan shigo sai muyi magana ta fahimta ko?Â
 Atare suka haɗa baki wurin cewa"Eh muna jiran zuwanka,sannan in ka tashi zuwa kazo mana tare da Hayati ɗinka muganta,"
  murmushi kawai yayi tare da rejecting call É—in,sai lokacin ya duba kiran nasu da sukayi mashi jiya acikin wayarshi,cike da mamaki yaga kiran da sukayi mashi jiyan da safen kuma already an É—aga kiran,natsuwa yayi yana tunanin wanene ya daga mashi kira harya tsara wannan Æ™aryar,tabbas junaid zai iya yi mashi wannan aikin,. Â
 Miƙewa yayi tare da saukowa daga saman gadon nashi,ya wuce cikin toilet dinshi,within 15 mins ya fito ya wuce wurin closet ɗinshi,tsaf ya kammala shiryawa cikin shadda purple colour ba ƙaramin kyau tayi mashi ba yabi jikinshi duka ya feshe shi da turare,
 Bayan ya ɗauki wayar shi ya fito tare da wuce wa part ɗin Rafayet,da sallama ya shiga ciki,baya acikin falon shi don haka ya wuce cikin bedroom ɗin shi,
 Yayi mamakin ganin shi a kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi,jikin shi na'a sanye da bathrobe da alama bai jima da fitowa daga wanka ba,
  Shiga ciki omar yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna sannan ya ambaci sunan shi a hankali"Rafayet wai haryanzu bacci kake yi?
  Yamutsa fuska yayi alamar idonshi biyu sannan yace"Omar,yau lalaci nake ji ajikina,duba fa ka gani tun ɗazu nayi wanka amma nagaza tashi in shirya kaina,"
  sakin baki Omar yayi yana kallon shi tare da jinjina kai yace"nasan meye matsalarka,wato har yanzu abun nan bai bar jikinka ba ko?
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
  "Mekenan"? Sgr ya tambaya yana kallon shi daga kwancen da yake,
  Murmushi Omar yasaki batare da yace komai ba,
  Miƙewa Sgr yayi tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna shi da Omar yace"Na fa tuna duk abunda ya faru jiya a tsakanina da yarinyar nan,"!
 "dagaske"? Omar ya faɗi da ɗan mamaki a fuskarshi,
 "yeah,amma bakomai na tuna ba,so nake ka faɗamun gaskiyar abunda ya faru,time ɗin da ka tarar damu asaman gadon nan,shin na cire shorts ɗin jikina ko ban cire ba"?
  tunkan ya ƙarasa maganar omar ya soma sakin dariya,
 Ɗaure fuska sgr yayi tare da cewa"pls Omar banason wasa,just tell me the truth,cos banaso yarinya ta raina ni,"
  tsagaitawa omar yayi sannan ya zayyana mashi dukkan abunda ya faru tsakanin shi da Sehrish,
  hannu sgr yasa tare da dafe forehead ɗinshi yace"OMG!Omar ashe kaine ka katse mun jin daɗina a wannan lokacin!meyasa baka bari na ƙarasa aikina ba"? ya ƙarasa maganar yana jifar shi da harara,
  dariya omar ya kuma yi kafin yace"nifa taimakonka nayi,kisan kai fa zakayi,"
  tsuke fuska yayi tare da cewa"babu wani nan,ni narasa meyasa kake mun haka,"
 Yayi maganar tare da kai hannu ya dauki pillow ya wurga mashi shi a fuskarshi,tarbe pillow ɗin Omar yayi a hannunshi tare da cewa"Am sorry bro,bansan abun yayi hurting ɗinka ba,amma ae ko yanzu bata 6aci ba,kasan inason farin cikin ka,bari natashi naje na kira maka yarinyar sai ka ƙarasa aikin naka,"
 Yana kai ƙarshen maganar tashi ya mike tare da nufar hanyar fita daga bedroom ɗin yana karashe dariyar shi,yana jiyo muryar sgr cike da zolaya yana cewa"Am waiting,"
Kai tsaye bayan Omar ya fito daga sashen sgr down stairs ya sauko tare da fuce wa daga main palour din,ko breakfast din bai tsaya yayi ba ya wuce wurinsu hossana,
Wuraren ƙarfe tara kiran Amrish ya tashe ta daga dogon baccin daya ɗauke ta tun bayan sallar asuba,dakyar ta iya buɗe idanunta da sukayi nauyi saboda bacci,hannu takai tare da daukar wayar dake ajiye asaman side drawer ɗinta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta a kasalance tace"Assalamu alaikum Amrish irin wannan kira haka tunda sanyin safiya"?
  daga can 6angaren Amrish tace"Sleeping sickness wai kina nufin har zuwa yanzu baki tashi daga bacci ba?duba time ki gani kusan 9 fa yanzu,"
 Jin haka yasa sehrish sa hannu tare da janye blanket É—in jikinta ta tashi daga zaune tana kallon clock, É—an xaro ido tayi tare da cewa"subhanallahi wai har 9 tayi?meyasa aunty azmee bata tashe ni ba,ya ilahi,"Â
 dariya amrish tayi tare da cewa"kin cika bacci reeshi yakama kije kiga psychiatric doctor ya duba brain ɗinki,"
  ɗaure fuska sehrish tayi kamar tana agabanta tace"oh ashe dama kallon da kike mun kenan ko?
   muryarta cike da dariya tace"no ba haka bane inason lafiyarki ne shiyasa na baki shawarar kije aduba ki,"
  "Okey thanks for ur advise amma fa ni ba inda zanje,da raina da lafiyata bazan kwasa na tafi asibiti ba,salon su ja man bala'e,"Â
Æ™arasa maganar tayi tare da cewa"pls inason zan shiga kitchen yanzu,i wll call u later bye,"Â
  sallama su kayi da amrish sannan ta mayar da wayar saman side drawer ta ajiyeta,
saukowa tayi daga saman gadon cikin sauri ta wuce cikin toilet, brush tayi tare da wanko fuskarta sannan ta fito ta wuce wurin wardrobe É—inta,buÉ—ewa tayi tare da É—auko mayafi ta daure shi akanta kamar É—an kwali,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.