Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
**********************SEHRISH
tun da english teacher ɗinsu ta fita daga class ɗin, sehrish ta kifa kanta asaman desk din gabanta tana ta sharar bacci, har amrish ta gane mata daga jiya izuwa yau sam bata gajiya da yin bacci,alamu ma sun nuna cewa bata fahimtar komai kanta dashi da kwankwon ashana duk ɗaya suke,tashi amrish tayi tare da fitowa daga seat ɗinta ta ɗan sa hannunta tare da bubbuga bayan sehrish tace"ki tashi mu tafi time ɗin break yayi," kusan sau uku tana tashinta daƙer ta buɗe idonta da suka canza launi saboda bacci, miƙa tayi tare da yin hamma alamar yunwa take ji ga baccin ma bai isheta ba, fitowa tayi daga seat ɗin nata tana cewa"ashe har lokacin break yayi "
Amrish tace"taya za'ae ki sani, bayan baccinki kawai kike tasha, anya kuwa ma kina yin bacci a gida ne? Ta tambaya tana kallonta a yayin da suke fita daga class É—in,
 "Ina yin bacci mana sosai,"_
"To meyasa kike yin bacci a class?ko karatu ma bakya saurara salon azo yin test ko exam kiyi ta baza idanu kina kallon question paper kina cizon biro ko? Ta fadi fuskarta É—auke da dariya, itama sehrish din dariya tayi tana cewa "insha Allah hakan ma bazata faru ba,kafin lokacin zanyi karatu sosai,"
 Suna tafiya suna fira har suka isa Lunch room ɗin nasu atare suka shiga ciki, students duk sun hallara suna ta having lunch dinsu,
 ruƙo hannun sehrish tayi tare da kaita gaban table ɗin da zasu zauna,sai da rishi ta zauna saman table chairs din sannan amrish ta wuce ciki don ta amso masu abunda zasu ci,
 Ajiyar zuciya sehrish ta saki tana kallon students din dake zaune a wurin suna cin abincinsu suna shan fira abunsu,zahiri su take kallo amma abaɗi ba komai take tunawa ba face fuskar SGR ɗinta,murmushi ta saki aranta tana cewa "koyana ina yanzu?me yake yi?ko yaci abincinsa?Allah yasa dae baibar cikin shi da yunwa ba,
babu mai bata amsar tambayarta, cigaba da cewa tayi"bani da wani burin daya wuce naganshi cikin nishaÉ—i batare da wata damuwa ba,amma narasa dalilin dayasa kullum fuskarshi aÉ—aure baison yin fara'a,inaso na kawo sauyi a cikin zuciyar shi ya Allah ka bani wannan damar da zan zama É—aya daga cikin farin cikin ran shi,"Â
  Gaba ɗaya tayi nisa acikin tunaninta, batasan meke wakana ba kwatsam taji hannun mutun a ƙirjinta an shafa mata, a wani irin firgice ta buɗe idanunta gabanta na faɗuwa,
  Bin su da kallo tayi atsananin tsorace, kai kana ganinsu kasan tantiran ƴan iska ne,su biyu ne mata jikinsu na sanye da uniform riga da wannan mini skirt ɗin,kai kace ba musulmai ba saboda ko head babu akansu, iya gashi ne kawai suka ɗaure abayansu shima ɗin na ƙari ne, ga uban bleaching sun sha abun dae kawai ba'a magana,.
 Kallon juna su kayi suna dariya kafin ɗayar tace "wow gaskiya an mana nisa, Sofia tun yaushe aka kawo wannan zazzafar a school ɗinmu batare da sanin mu ba"? ta tambaya tana faman sakin murmushi gefen fuska, tuni jikin sehrish yayi mugun sanyi bakomai ta tuna ba face nasihar da kanal yusuf yayi mata kafin tafara zuwa school,
 wadda ta kira da sofia tace"ni kaina bansani ba, amma yanzu tunda Allah ya haɗamu da ita, zatayi mana bayani ne, ta faɗi tana kallon sehrish tare da kashe mata ido ɗaya tace"ƴan mata,naga kin ɗaure fuska may be don na shafa chest ɗinki ne batare da izninki ba,ae mun afwa irin salon tamu gaisuwar kenan,ya sunanki ne"?
  ƙara tamke fuska sehrish tayi jikinta na rawa Allah Allah take yi Amrish tadawo don tasan ita zata iya dasu,
  ɗan ta6e baki zeenat tayi tare da cewa"Can't u talk to us? May be don baki son ko mu su wanene ba a school ɗin nan ba,zamu yi maki uziri ne," ta faɗi tana yarfa hannunta, yatsun nan zira zira tayi fixing nails dogaye a hannunta,
  shiru sehrish tayi burinta amrish ta ƙaraso in ba haka ba tashi zatayi tabar musu table din gaba ɗaya ta koma Class, duk da yunwar da take ji acikinta,
 Suna cikin zaman ne sai ga Amrish ta ƙaraso fuskar nan ɗauke da murmushi ta ruƙo tray a hannunta mai ɗauke da plate biyu na abincinsu tare da coke,
 Sehrish na ganinta ta shiga sauke ajiyar zuciya,amma abunda ya daure mata kai time É—in da amrish ta Æ™araso kai tsaye bayan ta ajiye masu tray É—in asaman table din, sai ta miÆ™a ma Zeenat hannu suka gaisa tare da cewa"Am really glad to see u guys, nayi missing É—inki sosai my zeenat," murmushi zeenat tayi tare da cewa"nayi missing É—inki nima,bcox of u na matsa wa mommy sai mun dawo nigeria sbd a Æ™agare nake da na haÉ—u dake ko fa isasshen bacci bana samu saboda rashinki,"Â
  bin su da kallo kawai sehrish takeyi baki asake, yarda suke magana tamkar irin mace da namijin nan,
 Muryar sofia ce ta katse su da cewa "oh ni ba'a ma ta tawa ko Amrish? Zeenat kaɗai kika gani shikenan bari na tafi," ta faɗi tana ƙoƙarin tashi cikin sauri Amrish tayi holding hands dinta tana cewa"am sorry kada ki tashi pls, in naga zeenat ina mantawa da komai ne,"
 ɗaure fuska sofia tayi tace"i can't stay here,cos am getting jealous bazan iya jure yarda kike son Zeenat ba,
 Dariya zeenat tayi tana cewa"in dai akan Soyayyata da amrish ne ke 6ata maki rai sai dae ki mutu,"Â
  ta faɗi tana mayar da idonta akan sehrish da tayi zugudun tana kallon ikon Allah,
 wuri Amrish tasamu ta zauna, kusa da sehrish suna facing ɗin su Sofia da zeenat,
 ɗan kallonta amrish tayi tare da cewa"am sorry my friend nabarki da yunwa ko"? ta faɗi tana kallon Sehrish wadda jikinta ya gama mutuwa,
 "A'a" ta bata amsa a takaice,
Mayar da idonta tayi kansu zeenat tace"bansan zaku zo ba ae dana haÉ—o mana abincin tare,amma bari na tashi yanzu naje na Æ™aro mana yadda zai ishe mu,"Â
 cikin sauri zeenat tace"no ba sai kinje ba its ok ba mu jin yunwa a Æ™oshe muke,"Â
  murmushi amrish ta saki tare da kallon sehrish tace"bismillah mufara ci time É—in komawa class ya kusa,"Â
  Gaba daya hannunta kerma yakeyi a haka ta ɗauki spoon ɗin zata fara cin fried rice din da takawo masu shaqe da plate,tana ɗebowa shinkafar na zube wa saboda rashin natsuwar da take ciki ba don komai ba sai don zeenat data tsare ta da waɗannan manyan idanun nata zubin na karuwai a tsaitsaye suke ga eye lashes da tayi fixing sinsu kamar ɗiyar roba,
 Ganin yarda hannun sehrish ke kerma ta kasa kai koda one spoon ne yasa Amrish ɗagowa ta kalli zeenat wadda ta zuba mata ido ko kyafta su bata yi,
 ɗan gyaran murya Amrish tayi tare da cewa"Zeeta pls kidaina kallonta hakan na hana ta samun natsuwa,class mate ɗina ce jiya tafara zuwa school bata saba da kowa ba,"
 ƙayataccen murmushi zeenat ta saki tare da cewa"its okey,ashe new comer ce, tayi mun kyau ne shiyasa nagaza janye idona akanta,ina fata kin sanar da ita komai game da zama cikin team ɗin mu?
 Cikin sauri amrish tace"a'a pls mubar maganar nan,ita ba'a team ɗinmu take ba kawai class muka haɗa da ita,"
  zeenat tace"that's impossible amrish tun da har kina yawo da ita a school dole ta zama ɗaya daga cikin mu,not only that yarinyar ta burgeni sosai........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda ƙarar cokalin amrish data bugi gefen plate dinta dashi tace"Zeeenat! Nace kidaina wannan maganar agabanta bana so," rai a6ace tayi maganar sannan ta mayar da idonta kan sehrish tace"pls ki ci abincin ki,"
 gyaɗa kai sehrish tayi tare da mayar da hankalinta akan abincin dake gabanta,ci take amma batasan inda abincin ke zuwa ba,saboda tsoro da ruɗin da ta shiga,
 yunƙurawa su kayi su biyun atare suka miƙe, cikin sanyin murya amrish tace"Am sorry zeenat i don't mean to hurts u,just bana son muna wannan maganar agabanta ne,saboda batasan komai ba ko mutane batason shiga cikinsu," hankali atashe take maganar tana kallon su,
 atare suka yatsina fuska sannan zeenat tace,kinsan bana fushi dake amrish shiyasa kike mun duk abunda kika ga dama,amma ina so ki sani 6ata mun rai tamkar 6atawa mommynki raine, kuma kinsan mai zo biyu baya ya zama dole kibi umarnin duk abunda nace, don haka wannan yarinyar dole tashiga team ɗin mu !!!
 tana gama faɗin hakan taja hannun sofiya suka fuce daga lunch room din
 ita dae sehrish zuru tayi tana kallon ikon Allah bayan sun fuce ta mayar da idonta kan amrish wadda jikinta yayi mugun sanyi tuni kuma idonta sun cicciko da kwalla, amma bata bari sun zubo mata ba, sai ma kallon sehrish da tayi tare da ƙaƙaro murmushi tace"ki ci gaba da cin abincin ki mana,naga kin tsaya,"
 jiki asanyaye sehrish ta mayar da hankalinta kan abincin tana ci amma zuciyarta ajagule saboda halin da taga Amrish ta shiga akan waɗannan ƴan matan da suka zo,ko su wanene oho,
Ta tambayi kanta,
***************************Twins
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.