Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Jin shiru hayaam bata fito ba tsawon lokaci,yasa Azmee leƙawa ɗakinta,anan ta same ta zaune dirshan gefen gadon ta zabga uban tagumi,jin motsin mutun yasa ta ɗagowa fuskarnan a yamutse ta kalli azmee,
"Hayaam wai dama duk budurin nan da akeyi acikin gidan nan kina ɗaki ƙumshe"?
Jin abunda azmee tace yasa tace"hmmmm,to ina zani Aunty azmee?babban yaya ya kore ni daga gidan nan,nasan muddin na leƙa waje ya ganni sai yasa an kora ni daga gidan nan,'
Cike da mamaki azmee tace"Subhanallahi!taya akai hakan ya faru?laifin me kika aikata mashi da har ya koreki daga gidan nan?shi da ma bai damu da mutane ba"
ta6e baki hayaam tayi kafin tace"Ni banyi mashi laifin komai ba,Sehrish ce ta shiryamun makircin da yasa har ya kore ni,batare da nayi mashi laifin komai ba,"
Tunda tasoma magana azmee ke kallonta,ga rashin gaskiya nan ya bayyana ƙarara a fuskarta,taya akai ma Sgr yasan da zamanta da har zai kore ta?dole sai in itace tayi mashi shisshigin da yasa har ya ganeta kuma ya kore ta,
"Allah ya kyauta toh,!yanzu ya zakiyi kenan?kinfa san halin shi!dole fa ki tattara kibar gidan nan!in ba haka ba wlh zaki fuskanci mummunan hukunci daga wurinshi,'
Hankali tashe hayaam ta miƙe tsaye tana kallon Azmee tamkar za tayi kuka tace"don Allah aunty azmee ki taimaka mun,wlh banso in bar gidan nan!na saba da zama acikinshi,anan nake samun duk wani jin daɗin da nakeso,acan gidanmu duk babu waɗannan kayayyakin more rayuwar,nasan zaki taimaka mun,"
Dariya azmee tayi tana kallonta ko yaushe tazo da har zata ce tayi sabo da mutanen gidan ta ayyana a ranta,
"Aunty azmee dan Allah ki taimaka mun,in xauna acikin gidan nan,nasan yana jin maganarki,ki roƙa mun shi akan yabar ni in cigaba da zama,wlh bazan ƙara shiga shirgin kowa ba,zanyi rayuwata cikin salama,"
Azmee tace"Tabɗijancan!so kike kija mun bala'e ko?ina zaman lafiyata agidan nan,Wacece ni?da har kike tunanin Sgr zaiji maganata?kin manta matsayina ne acikin gidan nan?kefa kike da alaƙa dasu ko kin manta ne"? Da biyu azmee tayi mata maganar saboda wulaƙancin da hayaam tayi mata,
Magiya hayaam ta shiga yi mata tana roƙonta akan ta nema mata mafita tamkar zata zuƙunna mata saman guiwarta,don ita sam bata shirya barin gidan yanzu ba,tabb yo mima akai kenan"ta fada cikin ranta.
Sosai abun yaba azmee dariya,
"Hanya É—aya ce hayaam in zaki iya!idan har kinason cigaba da zama acikin gidan nan"!
jiki na rawa hayaam tace"Ina sauraronki aunty azmee,wlh koma manene zan iya ni,"
Azmee taci gaba da cewa"daga yau zaki dinga yin shigar maza,kinasa gashin baki kamar yadda sehrish tayi a lokacin da tafara aiki acikin gidan nan kinga sai kizama kamar sabon mai tayani aiki"
Waro ido waje Hayaam tayi tare da cewa"Haba Aunty azmee ni zanyi shigar maza?so kike na ƙasƙantar da kaina har yarinyar can ta raina ni"
Azmee tace"that's the only solution,if not sai dae fa ki tattara kayanki ki bar gidan nan!"ta karasa maganar tana jiran jin ta bakin hayaam din don tasan da kyar zata amince dama shiyasa ta fadi mata hakan,
gyaÉ—a kai hayaam tayi tace"shikenan zanyi tunani in ga in zan iya,kafin nan zanci gaba da 6oye ma ganinshi"
Azmee tace"to shikenan kiyi yadda kika ga yafi maki,ni dai gaskiya ba ruwana,kuma fa dole ki rika futowa kina taya ni aiki,indai kina a cikin gidan nan, don bazai yiwu ba ki zaune a daki baki komae gaskia "
Hannu hayaam ta aza akanta tana faÉ—in"Nashiga uku!
dariya Azmee tayi kafin ta kuma cewa"hayaam zamanki fa bazaiyiyu acikin gidan nan ba,Sgr ya riga da ya kore ki!muddin ya sake ganin fuskarki dole ya hukuntaki,kuma kinga gwaggonsu ta katsina tazo,!matar nan bazata ta6a bari ki zauna acikin gidan nan ba,in har taji cewa ke ƙanwar matar yayyansu ce,nan zaki ga tashin hankali,sae ta kunyataki acikin jama'a,shiyasa nace kiyi shigar maza kawai,Ni zan taimaka maki muna yin aiki atare inyaso duk wanda ya tambayeni xance mashi abokin aiki ne na samo,nasan babu wanda zai zargi wani abu,
Komawa hayaam tayi ta zauna gefen gadon cike da damuwa,gaba É—aya taji ta tsani kanta,da tana zaman lafiyarta acikin gidan,kwaÉ—ayinta da zalamarta su suka ja mata,gashi ita gskia bata jin zata iya yin wani shigar maza wannan ai kaskanci ne,
"Na manta ban sanar maki ba!"
Rai a6ace hayaam tace"Menene!"
Azmee tace"SEHRISH TAGA ƳAN UWANTA,ASHE ƳAN UKUNE SU,YANZU HAKA SUNA ACIKIN GIDAN NAN!BAKI GANSU BA,ABUN FARIN CIKI KAMANNINSU IRI ƊAYA SAK!BAKI TA6A BANBANTA SU,"
A razane Hayaam ta miƙe tsaye hannunta dafe da saitin zuciyarta tace"WAI DAGASKE AUNTY AZMEE?
AZMEE TACE"Zan maki ƙarya ne?yaran suna nan,kyawawan gaske,HOSANA DA JAHAD!!!!!"
Jiki amace hayaam ta koma ta zauna,gabanta na faÉ—uwa rasss rasss!tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi,
Murmushi azmee ta saki tare da juyawa ta kama hanyar fita daga É—akin,buÉ—e kopar tayi tare da sa kai ta fuce,
Kamar jira take azmee ta fita,nan fa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita,saboda tsabar 6acin rai,wani irin ƙululun baƙin ciki ne taji ya tokare mata maƙoshinta,komae ya jagule mata,tabbas tana bukatar tayi magana da Aunty laila,lokaci guda yadda sukai da yaya babbar ya shiga dawo mata, sambatu tashiga yi tana bugun bed mattress kamar wata zautacciya,
Bayan kammala sallar isha'e,atare suka dawo cikin gidan,a babban falon suka kuma zama kamar É—azu dae,
Gyaran murya Abbansu yayi kafin yace"Ina yaran suke ne?wani yaje ya kira mana su,domin jin ta bakinsu"
Miƙewa fawan yayi kamar dama jira yake yi,wucewa ɗakin sehrish yayi bayan ya isa ya kwankwasa masu ƙopa,jahad ce ta buɗe mashi kopar jikinta na sanye da hijabi da alama bata jima da kammala salla ba,
Fuskarshi É—auke da murmushi yace"Abba nason ganinku,idan ba damuwa ku fito mu tafi atare,"
Jahad tace"Toh,bari na kirasu,"ta fadi hakan tare da juyawa ciki ta kira hosana da sehrish wadda har lokacin bata motsaba,tana nan saman gadon ta ƙanƙame jikinta,
"Hosana kuzo Abbansu na son ganinmu!hada sehrish kema ki taso,"
Maƙe kafaɗa sehrish tayi alamar bazata taso ba,
"Sehrish dan Allah kidaina abunda kikeyi,nasan duk don saboda ganinmu ne,idan har baki so zuwanmu ba zamu bar gidan nan,"acewar jahad,
É—aure fuska Sehrish tayi tare da kawar da fuskarta gefe tana faman hura hanci,
babu yadda basuyi ba akan sehrish tabiyo su amma taƙi binsu,har fawan sae da ya leko yayi mata magana amma ko kallo ma bai isheta ba,
A ƙarshe suka ƙyaleta,suka bi bayan fawan ya shiga babban falon tare dasu,
gaba daya hankalin kowa ya dawo kansu,musamman Abusufyan dake zaune agefen abbansu,ji yake kamar ya tashi ya rungumosu ajikinsa,su twins kuwa dasu irfan zuba masu ido kawai sukayi suna kallonsu,haka Omar da Abbas da kuma hajiya azeema,kowa burinshi yaran su tabbata ƴa'ƴan abusufyan ne,duk sun ƙagu suji cewa yaransa ne,tabbas da ba ƙaramin farin ciki zasu ji ba,
Sgr dae tunda ya É—ago ya kallesu ya gane cewa babu sehrish acikinsu,bayan yaji cewar dukansu Abbansu yace a kira mashi,
Abbansu ne yace"Ina É—ayar take ne?ni bana gane ma wacece babu acikin ku!
Omar yace"waÉ—annan hosana da jahad ne!sehrish ce babu acikinsu,"
Abbas yace"Masha Allah,gaskiya banta6a ganin yara masu kamanni irin nasu ba,Allah dae yasa mu tabbatar da abunda muke hasashe akansu....'
"Meya hanata zuwa"?muryar Sgr ce ta karaɗe kunnuwansu,har sae da su jahad suka ɗan tsorata dashi,dama tunda sukazo hankalinsu ke kanshi saboda launin kwayar idonshi ba ƙaramin ɗaukar hankali takeyi ba,
Fawan yace"Ba yadda bamu yi da ita ba,amma tace bazata zo ba,kamar tana cikin damuwa sosai,ko kallona fa batayi ba,da naje kiransu,'
A zafafe Sgr ya yunkura tare da miƙewa daga saman kujerar da yake ya nufi sashensu Azmee,
"Kuzo ku xauna kusa dani,"hajiya azeema ce tayi masu magana yayin da takeyi masu nuni da hannunta,
Hannunsu ruƙe cikin na juna,suka ƙarasa wurin sofa ɗin da hajiya azeema take,a gefenta suka zauna,duk jikinsu asanyaye saboda basu saba dasu ba,tunda suka zauna jahad ke kallon Abusufyan,saboda tunawa da maganar gwaggon katsina da tayi ɗazu na cewa shine mahaifinsu,kanta ya gama ɗaurewa,tashiga tambayar kanta taya akai hakan zata kasance?meke shirin faruwa da rayuwarsu ne?dama suna da dangi ne?wai su wanene su?ya akai rayuwarsu take a birkice ne?
tambayoyi iri iri tashiga yi ma kanta waÉ—anda bata da amsar su,
ƙasa ƙasa hosana tayi da muryarta tare da kai bakinta saitin kunnan jahad tace"Wancan mutumin sai kallonmu yake yi jahad,ni duk nabi na tsargu wlh,tsoranshi nake ji,shi da wannan kyakkyawan mai wasu kalar kwayar idanu kaman aljani....'
"Dan Allah hosana ki daina mun magana a kunne na,wai ke bakya ganin mutanene kuma duk idanunsu na akanmu,ni kaina atsorace nake wlh,yaya Omar kaÉ—ae nake kallo naji dan sauki,da ace baya a wurin nan da tuni na gudu...'jahad ce tayi wannan maganar,cikin raÉ—a tayi mata ita don kar aji su,
A lokacin da Sgr ya ƙarasa bedroom dinta,tura ƙopar yayi tare da faɗawa ciki,tsayawa yayi yana kallonta,ta takure kanta,jikinta sae kerma yakeyi yayin da hawaye ke saukowa daga cikin idanunta,sam bata lura dashi ba har sae da yayi gyaran murya,a firgice ta wurga idanunta akan fuskarshi,gabanta ne taji ya faɗi rass,nan take kermar jikinta ya ƙaru sosai,
"Taso muje"!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,girgiza mashi kai tashiga yi tana cewa"bazan iya tafiya ba,ƙafafuna ciwo suke yi mun,dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni,inji da abunda ke damu na,'
Abun ya ɗaure mashi kai,yadda take yi mashi jayayya,tabbas akwai matsala hakanan dae yarinyar bazata ƙi bin umarninshi ba,
Bai tsaya wani 6ata lokaci ba,ya ƙarasa shiga cikin ɗakin har saman gadonta ya bita,sai faman ja da baya takeyi,gaba daya ya ɗaukota tare da azata asaman kafaɗarshi ya fito da ita,sai kuka takeyi mashi tana cewa ya sauketa ita bazata je ba,su rabu da rayuwarta,suna ƙuntata mata,har bugun bayanshi ta dinga yi da hannayenta don ya sauketa,duk yana jinta,
tashin hankalin da ba'a sama shi date!
"Ga babban yaya nan ɗauke da sehrish din daman nasan sai dae ya ɗaukota,"acewar fawan,jin sautin kukanta yasa kowa yakai hankalinshi wurinsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,ƙiri-ƙiri tana gudun ƴan uwanta,bayan duk alamu sun nuna cewa su ɗin fa ƴan ukune,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.