Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Idan ka samu kaɗan ka gode ma Allah gobe saiya baka mai yawa😠Cikon page din ɗazu dama 3 page nace zan haɗe maku, sa'an nan ku gyara zama 😱😨
Ina guga ina editing gashi nan har na ƙona mata hijabi ynx jira nake tadawo inga mai zatayi mun😇🤣
   Hafsat Bature
     (Boss Lady)
_💋Boss Bature💋_
Murmushi taɗanyi sannan ta kuma cewa "ka yafe mun junaid ɗin abbansa,ba don bana sonka ba na tafi nabarka, nafi kowa sonka junaid saboda ni na haifeka,duk da nasan cewa a wurinka bancancanta na amsa sunan mahaifiya ba, amma inaso kaa sani nikaina ba'a son raina nabar ƴa'ƴana ba, bakowa bane ya son da wannan ba saboda ba kowane zai yarda dani ba, amma an takuramun an ƙuntatamun ko bacci bana iyayi a ƙarshe ma naji ƙasar gaba ɗaya tafita raina na dinga jin tamkar ƙona fatar jikina akeyi wannan shine dalilin dayasa nabar ƙasar, kai kuma abunda yasa ban tafi dakai ba shine, soyayyar da mahaifinka ke yi maka,idan na tafi dakai ya zai ji a zuciyar shi? shi kan shi bai fahimci hakan ba kowa tunaninsa na tafi don son raina ne amma ba haka bane junaid, akwai wani 6oyayyen lamari dake faruwa acikin gidan nan,nayi ƙoƙarin na fahimtar da abbanku saboda ni ina da masaniya akan wani abu, amma abbanku sai ya nuna mun cewa kawai don na tsani baƙar fata ne yasa nake zargin wasu,bayan ba haka bane ni duk wanda na tsana hakanan batare da wani dalili ba to yana da wata muguwar manufa ne... '
 Shiru junaid yayi yana sauraronta, bai cika ɗaukar komai serious ba arayuwarshi amma maganar mommynsa taɗan ta6a shi kaɗan, bazai ce ƙarya take masa ba saboda shi kanshi ya jima yana tunanin dalilin dayasa mom ɗinsa tabarshi, saboda shi ya kasance yaron da kowa ke so mai farin jinin gaske, taya za'ace uwar da ta tsugunna ta haife shi, itace zata ƙisa ta guje shi just without any reason !?
ï¿?
 gaba É—aya ya tafi duniyar tunanin ya amince da zancen mahaifiyar shi ko kuwa, shessheÆ™ar kukanta daya ji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa cikin sauri yace "its okey mom,ni banason nayi sanadin da zan zubar da hawayen wani,bare ke da kike mahaifiyata ma,"Â
 Ajiyar zuciya alexandra tashiga saukewa jin kalamansa masu daÉ—in gaske, muryarshi ce tasake katse ta da cewa "pls wipe ur tears mom,"Â
 Murmushi ta saki tamkar tana agabansa,hannu ɗaya tasa tana share hawayenta kamar yarda ya umarta tayi,
ï¿?
. bayan ta gogesu tace "baka son ganin hawaye ne? amma meyasa baka amsa kirana duk in na kira wayarka, ko na kira wani nace ya baka muyi waya,a duk lokacin da hakan ta faru ina zubar da hawaye na sosai,
 Murya asanyaye take magana, har cikin zuciyarshi yake jin maganar mommyn nashi,
 "Mommy inaso zan aje waya,i wll call u next time,
Cikin sauri tace "ka haramta mun ganin fuskarka ko? Shikenan my romeo,ka faÉ—i kome kake so zan maka shi"
 "Komai nace kiyi zaki yi ne"? Ya tambaya yana jiran amsa
 "zan yi maka shi koma menene,"
 murmushi junaid yayi sannan yace"yaya ayaan da jahan suna son wani abu wurin ki, kiyi masu shi, sannan ki dawo gida ki bani kulawar da baki bani ba tun ina yaro,"Â
 Murmushi tayi sannan tace"shi kaÉ—ai kake so"?Â
Yace "eh,"Â
  Jinjina kai tayi tare da cewa"duk abunda kace zanyi saboda in tabbatar maka da cewa ina tsananin ƙaunarka my romeo,sannan koda daga bayane kaga wani abu kana so ka sanar mun, zanyi maka koma menene shi indae acikin duniyar Nan yake, sun jima suna yin wayar daga bisani su kayi sallama, bayan ya ajiye wayar ya dinga jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarshi ga wani irin kwanciyar hankali da yazo mashi yasan cewa duk saboda wayar da yayi da mom in shi ne yasamu wannan natsuwar,
Sai wuraren ƙarfe 4'dai dai sehrish ta farka tana faman yin hamma, ba ƙaramin daɗin baccin taji ba,saukowa tayi daga saman gadon nata ta wuce toilet jim kaɗan tafito da alwalarta, hijab ta dauko ta zura a jikinta sannan ta kabbara sallah, tun tana cikin yin sallar taji ana knocing ƙopar ɗakin nata, don haka tana kammala shafa addu'a ta miƙe a hanzarce ta buɗe ƙopar,gabanta ne taji ya faɗi rass ganin matar nan ta ɗazu,murya na rawa tace "ina yini," murmushi Amani tayi tare da cewa "lpy ya kike,"?
"Ina lpy," ta bata amsa ataƙaice,
dan ta6e baki amani tayi kafin tace"naso É—azu dana ganki da safe muyi magana amma naga kina cikin sauri ne zaki school," ta fadi a wayance
 Sehrish tace"eh hakane," duk tarasa natsuwarta, tsoranta me take son ce mata,
ï¿?
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.