Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Follow this link to join my tiktok acct 👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
"What's it"? Omar ya tambaya yana kallon shi, ganin yarda Omar ke kumshe dariya yasa shi fasa yin maganar ya É—an É—aure face É—inshi yace"omar banason wasa fa pls tell me the truth, Did something happen last night? Naga bed sheet dina duk yayi wani squeezing kamar anyi dambe asaman shi,Â
  dariya sosai Omar yayi kafin yace"no ba wani abu just forget about it, na same ka ne kawai a wani yayi na ciwo so na ɗan taimaka maka ne har nasamu bacci ya ɗauke ka,"
ta6e baki sgr yayi yana kallon shi don bai yarda da abunda ya faÉ—a mashi ba, hakanan omar bazai tasa shi gaba yana mashi dariya ba just without any reason,
  miƙewa Omar yayi tare da kallon shi yace"bari na sauka down ko kana buƙatar wani abu ne nasa akawo maka"?
 juyawa sgr yayi ya kalli tray din da ke ajiye saman table ɗinshi yace"wannan yarinyar tazo ta tattara wannan kayan,ga bedroom dina ma inaso a gyaramun,"
  "Okey zan faÉ—a mata, ka huta my man,"Â
 Juyawa omar yayi zai fuce har yakai bakin door din ya waiwayo don ya kalli sgr karaf suka haɗa ido, cikin mamaki yace"Omar nifa wani kallo naga kana min irin kallon jarababben namijin nan......' ya faɗi yana tsuke mashi fuska,
 Fucewa omar yayi yana ƴar dariya, yamutsa fuska sgr yayi tare da cewa"Omar nason haukata ni, bansan wannan dariyar nashi me yake nufi ba," yayi maganar tare da kwantar da bayanshi saman lallausar mattress ɗin, kwakkwaran juyi yayi asaman gadon, kai tsaye idonshi ya sauka akan siraran gashin dake zube saman bedsheet dinsa, cikin sauri ya ɗago da kanshi tare da zuba ma gashin ido, mamaki ne ya kamashi taya akai gashin kanshi ya zuba don kuwa yana da tabbacin cewa sumar kanshi bata kakka6a saboda gyaran da take sha, hannun shi yakai a hankali tare da ɗauko siraran gashin guda uku ya zuba masu ido yana kallonsu, dogon gashi ne mai tsayin gaske, sak irin launin sumar kanshi wato dark brown colour, natsuwa yayi yana nazarin gashin, kafin yasanya hannunshi tare da ɗaukar siraran gashin a hannunshi,yunƙuwa yayi tare da miƙewa daga saman gadon, ya nufi gaban dressing mirror dinshi, zama yayi asaman front chair din madubin, sannan ya ajiye siraran gashin asaman shi, hannu yasa tare da tsinko gashin kanshi siriri guda ɗaya, sannan ya ajiye shi a gefen waɗancan sauran guda ukun, within 5 mins ya gane difference ɗin dake tsakanin su,tabbas wannan ba hairs ɗinshi bane to na wanene, asaman bedsheet ɗinshi kuma? hannu yasa ya ɗauki siraran gashinan guda uku, sannan ya tashi tsaye ya nufi bedside drawer ɗinshi, buɗewa yayi tare da buɗe jotter ɗinshi dake ajiye acikinta, a shafi na farko ya saka siraran gashin sannan ya rufe jotter ɗin, tare da mayar da drwer chest din ya rufe, wuce wa yayi wurin closet ɗinshi domin shirya kanshi,
***********💋Â
bayan fitar marshal omar daga part din Sgr kaitsaye down stairs ya wuce wurin dining area dinsu ya nufa ganin aunty azmee nata faman jera masu breakfast dinsu, tunkan ya Æ™araso ta soma sakar mashi murmushi tana cewa"Omar barka da fitowa fatan ka tashi lafiya,"?Â
  fuskarshi asake yace"lafiya lou Alhmdllh,"
  shiru ya ɗanyi kafin yace"am ina wannan yarinyar take ne sehrish"? Har sai da gaban azmee ya fadi rass jin abunda yace,dama tasan saiya tambayeta akan maganar nan,
  murya na rawa tace"bata jin daɗi ne tana a bedroom ɗinta,ni nace mata ta kwanta ta huta shiyasa bata fitowa. Ba.......'
 "Ta sanar dake game da abunda ya faru jiya"? Ya katse ta da tambaya,
  "Eh ta sanar dani komai," ta fadi adabarbace,
  Omar yace"okey ina son magana da ita, ki ce tazo tasame ni a part ɗina ina jiranta,"
 Cikin sauri ta amsa mashi da toh, sannan ta bar jera abincin da take yi ta wuce ɗakin sehrish,
  A hankali ta tura ƙofar tashiga da sallama, kwance ta same ta sai faman sharar bacci take yi, har lokacin jikinta bai daina yin kerma ba,
  matsawa tayi dab da ita tare da sanya hannu ta ɗan bubbugi kafadarta "Sehrish !!sehrish!!
 Har cikin dodon kunnanta taji kiran a firgice tafarka tare da miƙewa tsaye tana cewa"La'ila ha'ilallah.........' rufe mata baki azmee tayi tare da cewa"ki natsu ni ce" a hankali tashiga sauke ajiyar zuciya tana kallon azmeen da idanunta da suka canza launi saboda bacci,
 Janye hannu azmee tayi daga bakinta sannan tace"Omar ne ke son magana dake yace ki same shi a part ɗinshi yanzu,"
  zare ido sehrish tayi murya na rawa tace"Aunty azmee ni kuma.....na shiga uku....me zai tambaye ni......'. Katse ta azmee tayi tare da cewa"kada ki damu nasan game da allurar nan ne zai tambaye ki, kawai ki fada mashi gaskiya a wuce wurin,"Â
  fuskarta tamkar za tayi kuka tace"Aunty azmee ina tsoro fa kada naja ma kaina,"
  girgiza kai azmee tayi tare da cewa"ba wani tsoro omar zai fahimce ki, kina 6ata lokaci fa ki tashi ki tafi,
 Tana kai ƙarshen maganar ta juya ta fuce daga ɗakin, jiki asanyaye sehrish ta sauko daga saman gadon, hannu tasa ta ɗauki hijab ɗinta wadda ta ajiye asaman gadon milk colour ta zura ajikinta,
 Buɗe ƙopar ɗakin tayi ta fito tare da miƙar hanya ta wuce part dinsa, tsayawa tayi daga ƙopar shiga tana ƙoƙarin dai daita natsuwarta,sallama tayi mashi amma shiru ba'a amsa ba, ƙafa tasa tashiga daga ciki,babu kowa a falonsa komai anatse yake sai ƙamshi dake tashi,
  Shiga ciki tayi tare da samun wuri ta tsaya a kusa da royal sofa din dake a kewaye, gabanta sai faɗuwa yake yi kamar mara gaskiya,
  "Ya Allah ka bani ikon amsa tambayar da zaiyi mun,bana son nashiga matsala da kowa acikin gidan nan, nasan zasu iya zargina wayyo Allah na," ta furta tana faman yarfa hannunta, cike take da zullumin me zai biyo baya,
 tana cikin wannan tsayuwar wayar shi ta shiga ringing a firgice taɗan ja da baya saboda bata tsammaci jin sautin wani abu ba, bin wayar tayi da kallo tana ajiye asaman 3 seater din don anan yabarta,
  katsewa kiran yayi sai ga wani ya kuma shigowa, matsawa tayi a hankali saitin kujerar tana kallon wayar, ranta ne yabata ta ɗaga kiran taji wanene wata'kil kiran gaggawa ne,
  Tamkar ana tunzurata haka taji, hannu takai tare da ɗaukar wayar tayi picking call din tare da karawa a kunannta, tun kafin tayi sallama taji ance"Ya Omar shi ne jiya kace in ka koma zaka kira ni awaya amma naji shiru ko? Muryar hossana ce ke magana,
 Shiru sehrish tayi tana sauraron maganarta,. Â
 Acan kuwa jin tsit Omar ɗin yayi mata shiru yasa ta cewa"kana ji na kayi mun shiru ko, Allah idan bakayi magana ba yau ko breakfast bazanyi ba....' ashagwa6e tayi maganar,
  murmushi sehrish tayi jin yarda yarinyar ke magana, sai a lokacin tace"bashi bane, baya kusa ne,"Â
ï¿?
 Jin muryar mace yasa hankali hossana tashi ruƙe qugu tayi dama tana atsaye jikinta nasanye da kayan bacci riga da wando red colour, ta ƙara kara telephone din a kunnanta, tace
 "Æ™anwarshi ko budurwarshi ko matarshi wacece ke aciki ? ta tambaya a Æ™ule,Â
  "Matar shi ce," sehrish ta faɗi cike da zolaya, aikuwa nan take hankalin hossana ya tashi, muryarta tamkar zatayi kuka tashiga kwalama jahad kira tana cewa"Jahad!!Jahad!! ashe dama ya omar yana da aure shine bai fadamana ba,
  Yadda hossana ke kwala mata kira yasa ta fitowa daga kitchen cikin sauri ta nufe ta tana cewa"Hossana lafiya meya faru ne kike kwalamun kira? Ke da waye a waya? Ta tambaya a yayin da take ƙarasawa wurinta,
 duk sehrish ta kasa kunne tana jinsu,Â
Cikin shessheÆ™ar kuka hossana tace"Ashe dama ya omar na da aure bai fadamun ba,"Â
 Cike da mamaki jahad tace"kai haba wai dagaske?Â
 "Eh mana gatanan muna magana awaya," ta faɗi rai a6ace tana miƙa ma jahad telephone ɗin,,
 Hannu jahad tasanya ta kar6i wayar sannan anatse tace"Assalamu Alaikum,"
fuska dauke da murmushi sehrish tace"Wa'alaikum salam,"Â
 Jahad tace"ina kwana aunty,"Â
 "Lafiya lou," sehrish ta amsa,
 Jahad ta kuma cewa"dagaske ne kece matar yaya Omar"? ta tambaya tamkar tana a gabanta, Sehrish tace "eh nice,"
 jinjina kai jahad tayi tare da ɗan ta6e baki tace"Amma bai ta6a sanar mana ba, dan Allah sabon aure ne ko tsoho "
 Ƙiriss ya rage sehrish ta fashe da dariya daƙyar ta basar da ita tare da cewa"tsoho ne, mun jima atare ynx haka ma ina ɗauke da juna biyu ina fata zaku zo suna in na haihuwa,"
  Jiki asanyaye jahad tace"insha Allah idan ya barmu zamu zo, amma aunty baki faɗa mana sunanki ba"?
  Ƙara kashe murya sehrish tayi tare da cewa"sunana Zainab amma mijina yana kira na da Hayaty,"
KARANTA ZAFAFA 2022
✓Gurbin Ido... Na Huguma (Zafafa2022)
✓Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)
✓Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)
✓Babu So... By Billyn Abdul (Zafafa2022)
✓Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)
 Jinjina kai jahad tayi tare da kallon hossana wadda ke tsaye cikin ƙunar rai,
 Sun jima suna waya da sehrish kafin suyi sallama, mayar da wayar sehrish tayi ta ajiye saman seater ɗin, sannan ta koma tana faman tiƙar dariya,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.