Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Zaune suke acikin class sun natsu suna sauraron karatun da akeyi masu,malaminsu ne mai koyar dasu islamic studies,tun da ya fara karatun ya lura da yarinyar dake kwance tana yi mashi bacci acikin class,shiru kawai yayi baice komai ba,sai da ya kammala karatun sannan yace"wacece waccan yarinyar dake yi mun bacci acikin class"?ya tambaya yana nuna sehrish da maker É—in hannunshi,
 kamar jira ƴan class ɗin sukeyi ya tambayesu nan fa kowa yashiga bada bayani,
  "Uncle ae wannan yarinyar da kake gani sleeping sickness gare ta,ba'a ta6a yin darasi ba idonta biyu,kullum cikin bacci take kamar mai tsohon ciki," fashewa da dariya ƴan class din sukayi,
 Wani kuma yace"sir,da zarar tearcher ya shigo cikin class shikenan zaka ga ta fara hamma,daga nan sai bacci,"
  Bayan ya gama sauraron bayanansu,ya taka ya ƙarasa inda seat din sehrish yake,hannu yasa tare da ɗan bugun desk din,a firgice sehrish tafarka tare da ɗago da kanta daga saman desk ɗin tana kallonshi,
  jallabiya ce ajikinshi fara,ya tara dogon gemu,kana ganinshi zaka san cewa ba ƙaramin malamin addini bane,fuskarshi na manne da farin glass yayin da kanshi ke anaɗe da rawani,
   hankali tashe sehrish ke kallonshi tayi wuƙi wuƙi da ido saboda tsoran karya hukunta ta akan baccin da take yi mashi a class,
  Cikin harshen larabci yace mata ta miƙe tsaye,jiki na rawa sehrish ta miƙe tana faman zazzare ido,
  "Kalli cikin idona,"ya bata umarni,sunnar dakai sehrish tayi tana faman jin wani irin bugun zuciya,maimaita mata ya sake yi da cewa"bakiji me nace ba!ki kalli cikin idona!"
  ƙin ɗagowa tayi da idonta ta kalleshi,kuma nan take jikinta ya shiga yin kerma,
 Ƴan class ɗin duk sun zuba ido suna kallonsu,musamman amrish da tashiga damuwa ganin kamar malamin nason takurawa ƙawarta,
 Cikin sauri tace"pls uncle ayi mata afwa,bazata ƙara ba,'
 Batare da ya kalleta ba yace"Amrish ba laifi tayi mun ba,in fact nikeson taimakonta,shin wannan yarinyar ƴar wani gida ce"?ya tambaya yana jiran amsarsu,har lokacin sehrish na tsaye kanta na kallon kasa a matuƙar tsorace take,
  amsa mashi su kayi da cewa"bamu san a wani gida take ba,lokacin da aka kawota class ɗinnan tayi introducing ɗin kanta amman bata faɗa mana family status ɗinta ba,,'
 Amrish tace"nima bansan taƙamaimai daga inda take ba,amma akwai wani elder bro dinta dana sani sunan Shi Junaid romeo,muna shiri sosai dashi,'
 mayar da idonshi yayi kan fuskar sehrish yace"Ke!a wani gida kike?su wanene iyayenki?
 murya na rawa tace"Ni....ni..daga family din SALAHUDDEEN HUSSEIN nake Abban sojoji....'tunkan ta ƙarasa maganar malamin ya waro ido waje yana kallonta,bama shi ba hatta sauran student ɗin cike da mamaki suke kallonta,sun jinjinawa gidan da tafito bakomai yafi ɗaure masu kai ba face yarda ta kasance ba ruwanta da kowa haka,bayan duniya tasan da zamansu,
 "Kina nufin ke ƙanwar Surgeon genaral rafayet ce!da marshal Omar!"?
Amsa mashi tayi da cewa"eh,"kuma har lokacin bata É—ago da ido ta kalleshi ba,
 Jinjina kanshi yayi yana tuna wani abu daya ta6a faruwa dashi wanda ke da alaƙa da gidan,"
   gajiya da tsayuwa sehrish tayi nan take idonta suka soma shararo da kwalla,don bata da juriyar wahala irin hakan,tun lokacin data fara rayuwar hutu da jin daɗi,
  "Insha Allah bazan fasa ba,kamar yarda nayi kyakkyawar niyyar taimakawa tun a lokacin baya,don haka zan taimaka maki tunda Allah ya haɗani dake," malamin ne yayi wannan maganar,sannan ya mayar da idonshi kan amrish dake zaune a seat ɗinta tana kallonsu yace"Amrish idan na kammala yi maku karatu ki same ni a office ɗina zan baki ruwan addu'a kiba wannan yarinyar tayi amfani dashi,"
Amsa mashi tayi da toh sir,sannan yaja da baya tare da juyawa ya koma wurin board,
  Jiki asanyaye sehrish ta koma tare da zaunawa tana faman sauke ajiyar zuciya,aranta tana mamakin ruwan addu'ar mi zai bama amrish ta bata,gaskiya ni bazanyi amfani dashi ba,lafiya ta lou,koya ban zubarwa zanyi.......'
 Sai faman sambatu takeyi ƙasa ƙasa sam takasa samun natsuwa har sai da Malamin yabar Class ɗin,tashi amrish tayi tare da binshi don ta amso mata ruwan addu'ar dayace zai bata.
bayan mai taxi É—in ya sauke su,hannunshi ruke dana Amal suka shiga cikin gidan,gaba É—aya duk tabi ta susuce tana kallon katafaren gidan duk a tunaninta kodai gidansu ne ya kawo ta? Lokacin da suka shiga katafaren palourn babu kowa acikin shi,tsayawa yayi tare da ita atsaye yana jiran ganin ko wani zai fito,ita kuwa Amal wuyanta kamar zai tsinke saboda kalle kalle muryar Ayaan ce ta katse ta da cewa"har yanzu ciwon na maki zafi?girgiza kai tayi tare da cewa"a'a babu zafi ina lafiya,"
 "Okey,ki ɗan ƙara jira nasan matar gidan zata fito ne,bari na sake kiran layinta,"
 Hannu yasa tare da ciro wayarsa yana ƙoƙarin danna ma Amani kira,kunnan shi suka jiyo mashi takun takalmanta kwas kwas,ɗagowa su kayi gaba ɗaya suna kallonta,hannunta na ɗauke da tray da alama kayan breakfast ɗinsu da suka ci na safen nan ta fito dashi daga bedroom ɗinta dake a upstairs,jallabiya ce fara ajikinta ta yafa mayafin akanta,
 A hankali take saukowa down stairs sam bata lura da mutane ba,ƙura ido Amal tayi tana kallonta sam takasa gane wacece,juyawa ta danyi tare da kallon Ayaan tana neman ƙarin bayani,a lokacin shima idonshi na akanta yace"baki gane ta ba ko"?
 ɗaga mashi kai tayi alamar eh,murmushi yayi tare da cewa"Bari ta matso kusa,"
 Gyaran murya Ayaan yayi wanda hakan yasa Amani tayi firgit tana kallonsu,murmushi ta saki ganin Ayaan cikin sauri taƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin ta tunkaresu,zuba mata ido Amal tayi tana kallonta tabbas taso ta shaidata amma abunda yayi confusing ɗinta shine,taya zata kasance wadda take tunani tunda saurayin ya kawota gidan tafi tunanin ko Auntynshi ce,
 Tunkan Amani ta ƙarasa inda suke,hankalinta yakai ga Amal binta da kallo ta dinga yi cike da mamakin ina Ayaan ya samo wannan yarinyar haka,duk taji jiki kodai ya fara taimakon marayu ne,
 tsayawa tayi kusa dasu idonta na akan Amal ita ma kallonta takeyi,ji tayi gabanta na faɗuwa rasss rassss,cikin sauri ta mayar da idonta akan Ayaan murya na rawa tace"who...who is she pls?
  Murmushi ayaan yayi yace"i don't even know,ni dai ta bani numbar auntynta ne tace na kira mata ita,shine dana sa numbar Auntyn nata sai sunanki ya bayyana akai,that's why nayi deciding kawota wurinki,maybe adace.........'tunkan ya ƙarasa maganar a firgice Amani ta saki tray ɗin hannunta ya tarwatse ƙasa,zube wa tayi saman guiwowinta kusa da Amal ɗin ta ruƙo hannunta tana cewa"Amal kece dagaske nake gani,ko idona ne Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"!!!
 Tuni hawaye sun cicciko acikin idonta,
 Itama Amal ɗin tuni ta fara shararo hawaye saboda ta ganeta yanzu musamman data ambaci sunanta,
 Cikin shessheƙar kuka tace"Ni...Ni ce aunty Amani,ashe dama zan sake ganinki arayuwata.........'kukane yaci ƙarfinta hakan ne yasa takasa ƙarasa maganar,atare suka fashe da kuka suna yi kamar kamar me,
  Muryar Ayaan ce ta katse su da cewa"pls Aunty amani,ki lallasheta akwai wounds ajikinta idan tana kuka hakan zai ƙara mata raɗaɗin ciwon,"dakyar Amani ta tsagaita da kukan nata kallon fuskarta har izuwa jikinta,tayi matuƙar tsorata da ganin yarda yarinyar ta tsotse ta rame ta ƙanjame kamar kwarangwal,ƙashin wuyanta kamar zai ballo waje,komai na yarinyar da zai nuna cewa ita macece babu shi,sai dai ta hanyar shigarta ta mata da kuma muryarta,
  Janyota tayi ajikinta tare da rungumeta sosai tana ci gaba da ambaton sunanta"Amal amal ɗita ce ta koma haka?meya faru dake Amal ya akai kika 6ata,ki ka tafi kika barni inata nemanki Amal,"
 Ganin halin da suka shiga yasa Ayaan yanke shawarar tafiya yabarsu,juyawa yayi kawai tare da kama hanya ya fuce daga falon dama jahan sai doko mashi calling yake,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.