Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  Nan da nan ya shiga natsuwarshi tare da É—aga kiran ya kara a kunnan shi ya zabga sallama,Â
 daga can bangaren Ammi ta amsa mashi sallamar sannan tace"yaro na ya kake ya kuma jikokin nawa? Naji abunda ya faru da fawan shiyasa ma na kira don na tambayi ya jikin nashi,
  Tamkar yana agabanta cikin biyayya ya soma magana "lpy lou ammi suna cikin ƙoshin lpy,amma ba zaki zo gida ki duba jikin nashi ba?
 "Hmmmm ni me zanzo inyi agidanka? Ae yafi ƙarfi na, daga nan ma zan iya yi masa ya jiki ba sai na kwaso jiki nazo ba balle inga abun tashin hankali abun kunya,'
  nan da nan fuskar Abban nasu ta canza jin abunda tace,
  "Ammi dan Allah kidaina faɗin hakan bana jin daɗi saboda me zaki ce gidana yafi ƙarfinki bayan nikaina a ƙarƙashin ikonki nake ke fa kika haife ni, kuma wane irin abun tashin hankali da abun kunya kike magana akai"? yayi maganar fuskarshi a yamutse,
 tsoki taja tamkar zata fasa screen din wayar sannan tace "babu wani iko da nake dashi akanka hussein! Tunda har ban isa nasaka abuba kayi, wato son ƴa'ƴa ya rufe maka ido ko? ka daina ganin kowa da gashi? ba yarda banyi dakai ba akan ka tattara ƴa'ƴan nan duka ka haɗasu ka aurar kaƙi jin maganata, ka tara ƙattan maza,garada acikin gida sai sinturi suke yi acikin gidan ka,kaine jagoransu kai Gwauro su kuma tazurai gasu nan jibga jigba dasu kaƙi aurar dasu, daga anyi magana sai kace baka son ka takura masu ko kace ba su isa suyi aure ba don ka rainawa mutane hankali, dukansu kaf babu wanda in aka aura masa mace bazai iya yi mata ciki ba hatta wancan shagwa6a66en daka sangarta.......'
 runtse ido abbansu yayi tare da saurin cewa "Ammi dan Allah kidaina fadin hakan, aure fa lokaci ne kuma in yayi duk zan aurar dasu ne.....'
  wani tsokin ta sake buga mashi kafin ta kuma cewa "haka kullum kake faɗamin, narasa meyasa ƴa'ƴana duk basu jin maganata,daga kai har azeeman da wancan fitsararren da yayi hijra yabar ƙasar batare da sani na ba, ban ta6a tunain hussein zaka yi mun haka ba saboda duk kafi yi mun biyayya acikinsu amma yanxunn. .....' kukan da ta fashe dashi ne ya yasa ta kasa ƙarasa maganar nan take hankalin abbansu ya tashi, muryarsa har rawa take yi wurin cewa"Ammi dan Allah kidainamun kuka, ke fa mahaifiyata ce saboda me zakiyi mun kuka, hakan zai iya jefa rayuwata cikin matsala,dan Allah kidaina na roƙe ki mommyna indai akan wannan maganar ne yasa kike mun kuka wlh ashirye nake da nayi maki biyayya koba da son ransu ba, zan aurar dasu ne kawai saboda farin cikin ki !!!!!
 jin abunda yace ne yasa ta sassauta kukan nata tace "yaushe kenan zaka aiwatar da hakan? kasan natsufa sosai kada na mutu ba'ayi auran nan ba, dan Allah hussein ka tattarasu duka ka aurar a lokaci ɗaya in har kayi mun hakan zan shaida cewa kai hussein ɗinane dana haifa,'
  Ajiyar zuciya abban nasu ya sauke yana kara gyara wayar a kunnan shi yace "Insha Allah ammi nan bada jimawa ba,amma ki ban time saboda yanzu muna cikin fargaba game da waɗanda suka kaima su fawan hari,kin san sunce fansa suke ɗauka,kuma babban tashin hankalin ma maca ce AVENGER ɗin,'
 shiru ammi ta ɗanyi kafin tace "Shikenan hussein,nima na shiga damuwa dana ji hakan,dama nasan dole hakan ya faru saboda mahaifinku kafin yabar duniya ya tara maƙiya sosai kasancewarshi kwararren jami'en Soja sun halaka dubban masu tada ƙayar baya a ƙasar nan, shiyasa nake tunanin ko daga 6angarensa ne maƙiyan suke son ɗaukar fansa,duk da nasan cewa wannan mai shuɗin idon baya rasa maƙiya don mutun ne mai haɗarin gaske shima baya gajiya da kame ƴa'ƴan mutane yana kaisu lahira, kaga kuwa dole su ɗauki fansa suma,yakamata kasanya tsaro sosai agidanka, kuma akwai shawarwarin da nakeso na baka,"
  Abba yace "Ammi dan Allah kixo gida mana,ina ga zaifi in kika zo sai mu zauna mu tattauna akan matsalar tunda wannan abun ya shafi zuri'armu, kuma nama fi jin cewa akaina abin zai Æ™are tunda ni ne na tara Æ´a'Æ´a,"Â
  Ammi tace "shikenan zan fidda lokaci nazo insha Allah, amma inaso ka sani in zanzo saina tattara Æ´an matan family É—inmu gaba É—aya na kwaso su don suzo ayiwa Æ´a'Æ´anka baiko dasu,"Â
 dariya kawai abba yayi yana sauraronta sun jima suna fira kafin daga bisani su kayi Sallama 😊
 ya ajiye wayar gefen shi yana ɗan murmushi,
  A can kuwa junaid na isa ɗakin da fawan yake kwance yana bacci, cike da tausayi yake kallon shi yadda yake jan numfashi da ƙarfi da ƙarfi,
 ƙarasawa yayi tare da hayewa saman gadon yayi zaman cin tuwo tare da zabga uban tagumi yana kallon shi hawaye na zuba a fuskarshi,Â
 Jin shessheƙar kukan junaid a kunnan shi yasa shi farkawa daga baccin da yake yi, ya buɗe idon shi a hankali yana kallon shi, yarda ya tallabe fuskarshi hannu bibbiyu ya tasa shi gaba yana sharar kwalla,a hankali fawan ya furta "junaid "
 Kallon shi kawai junaid yake yana cigaba da matsar kwallo,hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda jikin fawan yayi ruɗu ruɗu da bulali wurin yayi jawur ya faffashe duk da anyi masa dressing na wurin an shafa masa magunguna,ga kuma ɗinkin da akayi masa a chest ɗinshi,
 dakyar ya daddage ya tashi daga zaune yana fuskantar junaid ɗin daya tasa shi gaba,
  "Junaid," fawan ya sake ambaton sunan shi a karo na biyu ganin yarda ya zabga tagumi yana kallon shi hawaye na zubowa gefe da gefen fuskarshi, zama su kayi suna fuskantar juna, kallon shi kawai junaid keyi batare da yace uffan ba,
 daÆ™yar fawan ya Æ™aÆ™aro murmushi yana kallon shi, hannun shi yakai tare da shafa gefen fuskar junaid yace "bari nabaka wani labari Æ™anina,"Â
junaid ya zuba mashi ido yana sauraron shi,
 fawan yace "lokacin da waɗannan miyagun suka ɗauke ni ko, suka shiga dani wani ƙogon dutse mai rikitarwa, suka ban za6i biyu, su kashe ni ko su azabtar dani wanne nakeso, kasan me nace masu? ya fadi yana kallon shi, girgiza kai junaid yayi alamar a'a,
 Fawan yaci gaba da cewa "a lokacin kai kawai ka faɗo mun araina, aranar da zamu tafi kai ta zabga kuka kana cewa babu inda zamuje ƙafarka ƙafarmu dakyar abba ya shawo kanka, ka tuna abunda ka faɗamun lokacin?
 shiru junaid yayi yana tuna lokacin daya cakumi rigar fawan yana ce "ya fawan kayimun alƙawarin cewa zaka dawo araye inaso na sake ganin ka,' a lokacin fawan yace mashi "junaid ae tafiya ba mutuwa bace, insha Allah zan dawo araye in Allah ya yarda," murmushi junaid yayi tuna wannan
 shima fawan murmushin yayi sannan yaci gaba da cewa "saina ce masu ni bana tsoran mutuwa, ban isa na hana kaina mutuwa ba in lokacina yayi, kamar yarda kuma baku isa ku hana kan ku mutuwa ba idan tazo maku, sai É—aya daga cikin su yace mun "Ka za6i ka mutu kenan? mu kashe ka kawai? Saina girgiza kai nace "a'a ku azabtar dani kuyi mun duk irin hukuncin da zakuyi mun amma kubar ni da raina saboda akwai Æ™aramin Æ™anina da nayi ma alÆ™awarin cewa zandawo da raina, inaso na cika mashi wannan alÆ™awarin nasa na gani na araye, bana so na karya mashi zuciya nafiso ko mutuwarce ma to na mutu agabanshi yadai ganni da raina...............' dakatawa fawan yayi da maganar saboda hawayen da suka zuzzubo mashi, junaid kuwa tuni ya fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai,Â
haɗe kansu su kayi wuri ɗaya suna faman shessheƙar kuka atare,
 dakyar fawan yaci gaba da cewa "Shine suka bankamun kayan maye sannan suka ɗaure ni tamkar dabba, su ka dunga zuba mun bulali da kaca a jikina har saida suka ga jini na zuzzuba ajikina amma hakan bai ishe su ba, ba don su babban yayan mu sun zo ba to da tabbas kashe ni sukayi niyyar yi a lokacin, Amma alhamdlh naji daɗi sosai da Allah yacika mun burina na ganin na rayu don na cika maka alƙawarinka......
.. murmushi junaid ya saki tuni ya ji sanyi ya ratsa mashi zuciyarsa,
 janye kansa yayi daga na fawan sannan yace "kana jin yunwa in kawo maka abinci"?
  girgiza kai fawan yayi tare da cewa "junaid a ƙoshe nake,ɗazu azmee ta haɗamun kakkauran tea tare da fruits na sha,naji daɗin su sosai,"
  "Bari nabarka ka huta sosai, na katse maka baccinka, amma ka sani zan dawo don atare zamu kwana," yayi maganar yana ƙara jaddada masa ayayin da yake sauka daga saman gadon,
 Murmushi kawai fawan ke bin shi dashi harya fice daga ɗakin,komawa yayi a hankali ya kwantar da bayansa saman filonsa tare da lumshe idon shi,
  Cikin sauri junaid ya fito tare da tunkarar hanyar fita saboda tunawa da sehrish wadda ke a school, lokacin tashin su yayi gashi time na salla na kokarin wuce shi, yana dab da fita daga Æ™opar Amani ta kwada masa kira, dakatawa yayi tare da juyawa yana kallon ta da murmushi a fuskarsa, cikin sauri ta Æ™araso gab dashi tana cewa "ina zaka je ne? Junaid yace "inaso zance masallaci ne nayi sallah, daganan zan wuce na dauko sehrish daga school,"Â
 ɗan jinjina kai tayi kafin tace "wannan yarinyar da muka gani ɗazu itace sehrish"? Ta tambaya tana kallon shi duk da tasan akanta yake magana
 "Yeah itace," ya bata amsa atakaice tare da fucewa yana cewa "Sauri nake aunty amani time É—in sallah zai wuce ni,"Â
  Juyawa amani tayi tana jinjina kai, a Æ™agare take da junaid ya dauko yarinyar daga school saboda tana son ta sake ganinta har ma ta yi magana da ita,Â
*wannan kenan*ðŸ˜ðŸ‘
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.