Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
ba ƙaramin tausayi yaba Abban nasu ba, tamkar ya zubar mashi da kwalla haka yake ji, daurewa kawai yake yi
 Sai da ya shanye kusan rabin ruwan sannan ya janye mouth ɗinsa alamar ya ƙoshi, sannan Abban nasu ya rufe robar ruwan ya mayar da ita saman side drawer din ya ajiyeta,
 Sannan ya mayar da idon shi kan fawan dake ta faman sauke ajiyar zuciya yana fidda sound na radaɗin ciwo abakinsa,
 Haroon daka la6e acikin labule yace "shegen yaji dannar manya,an gaya ma jin ƙamshin mutuwa wasa ne,dole ka nemi ruwa yaro, ba don jatuminka ya faɗo cikin ɗakin nan ba, da yau saina aika ka barzahu wurinsu munkar, gskiya Abba ya kawo mun cikasss amma ba komai mu haɗe gaba,' ya faɗi yana cizon la66ansa,
 Haroon kenan duk da yana cikin tashin hankali amma hakan bai hana shi sambatun nan nashi ba, mutuwa ce kawai zata iya zuge zeep É—in bakinsa,Â
muryar shi na rawa yace "Abba ashe zan ƙara rayuwa? abba nasha wahala sosai tamkar bazan rayu ba,ashe da rabon na sake ganinku a idona"? Ya faɗi yayin da idonshi ke zubar da kwalla,
  shima Abban nasu jiki asanyaye yace"Fawan nasani wlh,nashiga damuwa sosai game da halin da kake ciki har nagaza runtsawa saboda son nazo naga wani hali kake ciki,kayi haƙuri fawan iya cuta dae sun cuce ka sosai sun raunata dukkan ga66an jikinka, amma nayi maka alƙawarin cewa ɗaya daga cikinsu bazai sha ba, wlh muddin ina da raina da kuma lafiyata saina ƙuntata duk wani jin daɗinsu na duniyar nan,"
 Lumshe ido fawan yayi tare da kwantar da kanshi a kafaÉ—ar Abban nasu yana sauke ajiyar zuciya sannan yace "Abban sunce fansa suke É—auka akan family É—in mu,wannan harin da suka kai mana, ba don kowa su kayi shi ba face saboda mu kawai,"Â
Jin wannan maganar ta fawan tasa zuciyar Abban nasu yin wani irin bugu duk da yasan maganar revenge É—in amma baisan cewa akan Æ´a'Æ´ansa bane abun zai afka,
 "Insha Allah, Allah bazai ta6a Basu nasara ba fawan,zamu tashi tsaye wurin ganin mun kawar da koma su wanene su,Kuma zamu dage da addu'a akan Allah ya tonu asirinsu ya Kuma Kare Mana zuri'ar mu da dukkan al'umar musulmi,"
 "Ameen Abbana," ya amsa mashi daker,
 Haroon dake a la6e bayan curtains duk yana sauraronsu gaba daya ya Æ™agu abban nasu ya fuce daga dakin shima ko ya samu ya gudu,tuni kafafunsa suka soma daskare wa suna mashi raÉ—aÉ—i saboda tsayuwar da yayi, ga wani irin fitsari daya matse shi, sai uwar zufa ke wanko masa daga fuskarshi, runtse idanun shi yayi yana cewa "wayyyo Allah na, ko yaushe wannan tsohon zai ware nima in samu in gudu,lallaima mutumin nan wato saboda wannan É—an shilan shine harya gaza yin bacci, ya wani kwaso kafafunshi yazo don ya gan shi,ina sane da komai wato ya daura son duniya ya aza masu,duk ranar dana hallaka É—aya daga cikinsu zanga in haukacewa zaiyi ko kuma zaiyi suicide ne,'Â
 Ya faÉ—i yana cizon lips dinsa yana wani irin huci, bude idonshi yayi tare da sa hannu ya sake bude labulen a hankali ya leÆ™a su, har time din abban nasu na zaune dirshan saman bedmattress din, fawan kuma ya kwantar da kanshi a kafaÉ—ar shi,da alama ma bacci yayi awon gaba dashi gaba É—aya ya lafe masa kwance luffff abunsa,Â
 Tuni ran haroon ya ƙara 6aci saboda takaici da baƙin cikin dayake ji aduk lokacin daya ga Abbansu na nuna ma ƴa'ƴan alexandra soyayya,zuciyar shi tafarfasa take yi saboda jin haushi, mayar da idon shi yayi kan pillow dinshi da yayi wurgi dashi kasa, nan gabansa ya faɗi tsoranshi kada abban nasu yaga fillon don za'a iya samun matsala,
 Bari dae in taƙaice maku zance,Abban su bai bar ɗakin ba anan bacci ya ɗaukesu su duka biyun azaune fawan kwance a shoulder ɗinshi,
 Kamar yarda suka kwana a zaune suna bacci haka Sir Commender Haroon ya kwana a tsaye ba bacci duk yarda yayi motsi zai fito sai Abban nasu ya buÉ—e ido, hakan ne ya hana shi fitowa daga bayan labule,Â
 ya kuke tunanin wanda ya kwana atsaye idonshi buɗe fuskarshi zata kasance, koda yake fa soja ne 😂
  (Wata dae tace commendern ƴan Iska dae, Bana sojoji ba)😹😹😹
****************************Morning
tun da sassafe sehrish tafarka daga guntun baccin daya É—auketa bayan Sallar asuba anan saman sallayar ta kwashe da bacci, duk jikinta amace tafarka sai faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji, gashi yesterday night bata samu enough sleep ba saboda tayi nafilfilin dare,
  tunawa da school yasa ta yin hanzarin tashi tashiga toilet shaf shaf tayi wankan ta,
fitowa tayi jikinta ɗaure da towel fari, a bakin ƙopar toilet ɗin ta tsaya tana kallon uniform ɗinta da sukayi uban squeezing tun jiya da tadawo school ta cicciresu ta jefar saman gadonta bata ninke su ba kuma anan tabarsu,girgiza kai tayi sannan ta ƙarasa agaban mirrow ta tsaya tana shafa body oil ɗinta,bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗinta, hannu tasa ta ɗauko ɗayan uniform ɗinta mai pencil skirt ɗin nan sannan ta dawo ta ajiyesu gefen gadon tashiga zura su ajikinta, tana cikin sa kayan maganar haroon ta faɗo mata aranta nace wa ta fara sallar dare domin neman tsari daga sharrin shi, tabbas maganarsa ta girgiza ta saboda tun daga lokacin da ta dawo daki at midnight tafarka tayi nafilfili saboda neman tsari daga sharrin shaiɗanin mutun irin haroon, ta jima tana jin cewa wasu abubuwa zasu faru tabbas acikin gidan!!!!! duba da irin mafarkin da tayi a baccinta na jiya, kuma taci Alwashin cewa ashirye take data fuskanci duk wani abu da zai taso ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wani da zaizo don tarwatsa rayuwarta ko kuma family ɗin SALAHUDDEEN HUSSEIN,
Hakan na nufin SEHRISH ta shirya zama AYYANA wato mai bama family É—insu kariyyya daga miyagu irinsu Haroon da kuma ire-irensa masu irin wannan mummunan kuÉ—irin,nace ba Allah ya ba mai rabo sa'a,Â
  Tana cikin wannan tunanin azmee ta kwankwaso ƙopar ɗakin tana cewa "Allah sa dai kin tashi,"
Murmushi sehrish tayi a lokacin ta kammala sanya uniform É—in, ba Æ™aramin kyau sukayi mata ba tafito É—ass especially skirt É—in da ya bi shape É—in jikinta sosai,Â
 ƙarasawa tayi ta buɗe mata ƙopar ɗakin tana cewa "ae tun ɗazu na tashi nama kammala shirya wa,"
 Bin ta da kallo azmee tayi tana jinjina kai kafin tace "To fa yau wankan skirt aka ɗauka? masha Allah kinyi kyau ƙanwata, ya maganar breakfast fa? ta tambaya tana kallon ta,
 Sehrish dake ta faman murmushi tace "aunty azmee yau a school zanci abinci na gaskiya,amma zansha koda tea ne,"
 Azmee tace "okey, shikenan bari na kawo maki tea ɗin,'
gefen gado ta Zauna tana jiran dawowarta,
A 6angaren haroon kuwa bashi ya samu damar barin ɗakin da fawan ya ke ba har sai wuraren sallar asuba bayan abbansu ya kwantar da fawan dake ta faman sharar bacci a kafaɗarsa, sannan ya samu yabar ɗakin don zuwa yin sallah, sir commender haroon na ganin haka ya lalalla6a ya fito ya sungumi pillow ɗinsa daya shigo dashi, sai da ya jinkirta abakin ƙopar ɗakin ya tabbatar da cewa sun harhaɗu sun tafi gabatar da sallar asuba sannan ya koma ɗakin shi, agalabaice ya hankaɗa kopar bedroom ɗin nasa yayi wurgi da filon hannun shi,sannan ya afka toilet don tuni mararsa ta ɗaure saboda fitsarin dayayi ta ruƙo har na tsawon awannni, fitowa yayi daga toilet ɗin har wani biji biji yake gani saboda yarda idanun shi suka galabaita sun kumbura sunyi jawur saboda rashin baccin da baiyi ba, saman gadon shi ya afka batare da tunanin yin sallar asuba ba, sai ma addu'a daya shiga yi yana cewa "ya Allah ka yafe mun,zan ɗan rama baccin da banyi ba da safe in na tashi zanyi sallar anjima,'yana faɗin hakan ya shiga sharar baccin shi,
Babu wanda ya tayar da junaid daga bacci saboda basu son kwata-kwata yaga fawan ko kafin su tafi yin sallar asuba sai da Abbansu ya buÉ—e door É—in É—akinsa ya same shi baje magashiyyan yana sharar bacci rungume da pillow, murmushi kawai yayi tare da rufa masa door É—in suka wuce mosque,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.