Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Marshal Omar na kwance saman gadonshi yayin da idanunshi suke kallon saman ceiling bakomai yake tunani ba face hosanar shi,kowane hali take ciki yanzu?taci abinci kuwa?tambayoyi iri iri ya shiga yi ma kanshi,
yana cikin wannan tunanin wayarshi dake ajiye gefenshi ta shiga yin ringing,miƙa hannu yayi tare da daukar wayar,duba mai kiran nashi yayi ganin sunan Major ya bayyana akan screen din wayar yasa shi saurin ɗaga wayar tare da karata akan kunnanshi,
Ko sallama major baiyi mashi ba saboda tsabar tashin hankalin da yake ci,
"Yalla6ai yarinyar nan fa ta 6ace,an neme ta an rasa ko'ina na makarantarsu,É—azu osman ya kira ni awaya yake sanar dani cewa yaje É—aukarsu a school,hosana kaÉ—ae ya gani banda jahad,mun duba ko'ina babu ita,"
Waro ido waje Omar yayi ba arziƙi ya sauko daga saman gadon yana cewa"Major!ban fahimci me kakeson sanar dani ba!kayi mun da yaren da zangane,"
Major yace"yalla6ai,jahad ce ta 6ace a school,'
Rai a6ace Omar yace"Garin yaya hakan ta faru!taya akai Osman yayi gangancin da har ya bari jahad ta 6ace bai ganta ba!'duk inda take ku nemo mun ita in ba haka ba,ran kowa zai 6ace don bazan lamunta ba,"
Yana ƙarasa maganar ya kashe kiran,gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji daɗi,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoronshi kar ace jahad ta gudu ne don taje nemanshi saboda halin da hosana ke ciki,
Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin nashi,zuciyarshi nata tafarfasa saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,abubuwa sunyi mashi yawa,yana cikin damuwa sosai,ga kuma wata damuwar da major ya ƙara mashi,na 6atan jahad,
É—ago da wayar ya sake yi a hannunshi ya shiga dialing wasu numbers,
sannan ya dannama numbar kira,nan take kiran Ya shiga aka É—aga wayar,
tun kafin yayi magana wata murya kakkaura ta karaÉ—e kunnanshi da cewa"We are waiting for ur command sir,"
Cikin harshen turanci omar ya shiga basu bayani akan 6atan jahad,
Ya ƙarasa maganar tare da cewa yanzun nan zan tura maku da hoton ta,banason ta ƙara 1 hour awaje,duk inda take ku nemota,adawo mun da ita gida,"
"Okey sir,'suka amsa mashi,sannan yayi rejecting kiran nasu,
sai bayan daya kashe wayar sannan ya tuna cewa baida hotonsu,amma yasan baza arasa ba wurin osman,
Batare da 6ata lokaci ba,ya kira osman awaya,bugu É—aya osman ya É—aga kiran cike da fargabar abunda omar zai sanar mashi,
"Osman!"
Murya na rawa osman yace"Na'am yalla6ai,"
"Inaso ka turomin hoton jahad yanzu in kana dashi awayarka,inma babu ka É—auko mun hoton fuskar hosana,ina jiranka yanzu karka 6ata mun lokaci,'
yana kai ƙarshen maganar tashi ya katse kiran,cigaba da zagaye ɗakin yayi yana jiran osman,
within 15mins,sai ga kiran osman ya shigo,
É—aga kiran yayi tare da karawa a kunnanshi,
On the other hand Osman yace"yalla6ai na turo da hoton,ta cikin Whatsapp dinka,"
"Okey," ya amsa tare da katse kiran,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin duba whatsapp dinshi,anan yaga hoton da Osman ya turo mashi,zuba ma hoton ido yayi yana kallonshi,nan take yaji kewarta ta kama shi sosai,hoton hosana ne Osman ya É—auko mashi,da alama sabon hotone yayi mata da wayarshi,ko uniform dinta bata cire ba,fuskarta da alamun hawaye saboda kukan da tasha na 6atan Jahad,
Lumshe idonshi yayi tare da buɗesu akan hoton yana ƙare mashi kallo,a hankali ya furta"I love u so much hosana,nayi missing ɗinki sosai,kamar nayi hauka,nashiga damuwa sosai akan rashin sanyaki a idona,bazan iya jurewa ba hosana,kina buƙata ta a kusa dake,zanzo don na lallashe ki nasan zaki shiga damuwa sosai akan rashina da kuma rashin jahad akusa dake,
Tura masu hoton yayi sannan ya kira major awaya ya sanar dashi cewa ya jira shi a waje,gashi nan fitowa,
Yana kammala yin wayar cikin sauri ya fito daga part É—inshi,ya sauko downstairs,da sauri da sauri yake nufar hanyar fita daga main palour din,
yana ɗaga ƙafarshi zai fita yaji an ambaci sunan shi"Ya Omar,"
gabansa ne yaji yayi wani irin bugu,aranshi yace"wannan ae muryar Jahad ce,
da saurin gaske ya juya tare da kai idanunshi wurin da jahad take tsaye sanye cikin uniform tana kallonshi,fitowarta kenan daga bedroom din sehrish,cikin sanÉ—a take tafiya zata gudu daga gidan,kwatsam ta hango shi sai faman sauri yake yi zae bar gidan,
Kanshi ya gama É—aurewa binta yayi da kallo gaba É—aya ya rikice aranshi ya shiga tunanin cewa anya ba kunnan shi bane suka jiyo mashi muryar jahad!wannan ae yarinyar gidansu ce sehrish,muryarta ce tayi mashi gizo yaji kamar ta jahad,
Murmushi ya saki tare da nufarta yana cewa"Sister har kin dawo daga school É—in?ya karatun naku,ina fata kina mayar da hankali ko?
Kamar zatayi kuka tace"Ya Omar,Jahad fa ce! Nice jahad,ya Omar meyasa ka tafi kabarmu,"!
Zaro ido waje Omar yayi cike da mamaki yake kallonta, muryar shi na rawa yace"Jahad!dagaske kece kodae kunnena ne ke jiyemun ba dae dae ba"?
fashewa tayi da kuka tare da ƙarasawa wurinshi ta kwantar da kanta asaman ƙirjinshi tana cewa"Ya omar dama kana nan,da ranka da lafiyarka amma kadaina zuwa wurinmu?meyasa ya Omar?bakasan halin da muka shiga ba ni da hosana,na rashin ganin ka,'
tashin hankalin da ba'a sama shi date,
ruko hannunta Omar yayi tare da janta suka shiga cikin wani corridor inda ba kowa,sannan ya kalle ta cike da mamaki yace"Jahad!nagaza yarda cewa kece!taya akai kikasan gidan mu har kika zo?
cikin shessheƙar kuka tace"bani na kawo kaina ba,kawo ni akayi,wannan ƙanin naka junaid,wanda ka ta6a nuna mana hotonshi nida hosana a gida,shi ya ɗaukko ni daga school ya kawo ni gidan nan,bansan meyasa ya ɗauko ni ba,ya nuna kamar yasanni bayan bamu ta6a haduwa dashi ba.....'
Tun kan ta ƙarasa maganar Omar yace"subhanallahi!an samu matsala,junaid yayi kuskuren ɗauko ki jahad,Yarinyar gidan nan yaje daukowa a school,da yake kuna kama da ita sosai,komai na fuskarku iri ɗaya sak,shiyasa ya ɗaukko ki amaimakonta,'
mamaki ne ya kama jahad jin abunda Omar yace,sae lokacin ta tuna da sunan da Junaid ya dinga kiranta wato Reesh,taya akai suke kama da yarinyar gidansu har kanin nashi ya gaza banbantasu!" ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta,
"Jahad,muje na sauke ki gida,in yaso sai mu ƙarasa tattaunawa acan,"
Ya ƙarasa maganar tare da fitowa ruke da hannunta suka fice daga cikin babban falon,anan waje ya samu Major tsaye jingine da mota yana jiranshi,
Koda ya ganshi ruƙe da hannun jahad mamaki ne ya kamashi,dama shi bai ta6a ganin Sehrish ba,tunda ba shiga ciki yake yi ba,basu ta6a arba da ita ba,
Fuskarshi dauke da murmushi yace"Sir!anganta kenan"?
Omar yace"eh,ba rabon musha wahala,wai junaid ne ya É—aukota daga school shi duk atunanin shi wannan yarinyarce ta cikin gidan nan,da yake kamanninsu iri daya sak,'
major yace"ikon Allah,amma ni ban ta6a ganin yarinyar ba,'
ya ƙarasa maganar a yayin da yake buɗe masu mota suka shige ciki,sannan ya tashi motar yabar gidan ɗauke dasu,
_💋Boss Bature💋_
A 6angaren sehrish kuwa,tana cikin tsayuwar nan agefen titi tana jiran zuwan junaid,sai ga motocin waÉ—annan fusatattun sojojin da Omar ya turo don su nemo mashi jahad,ae koda sukayi arba da sehrish,suka duba hoton da Marshal Ya tura masu suka ga iri É—aya fuskar,sae ransu ya basu cewa itace yarinyar da Omar yace su nemo mashi,
Da sauri suka tsayar da motocin nasu tare da diddirowa daga saman motocin tamkar wasu zakuna haka suka tunkari sehrish,
Kamar ance ta juya,idanunta sukayi arba da waɗannan sojojin dake tunkararta hannunsu ruke da bindigu,bakomai ne ya fado mata a ranta ba face Ƴan boko haram da ƴan bindiga daɗin dake ta sace mutane agari,
ja da baya tashiga yi gabanta na faduwa
maimakon suyi mata magana cikin daÉ—in rae sai suka daka mata tsawa tare da cewa"ke zonan"!
Aikuwa a firgice sehrish ta watsa da gudun gaske ta saki jakar makarantarta ƙasa,bin ta sukayi da gudun gaske,tana gudu suna bin ta tamkar zata tashi sama,
yarda kasan wadda taci ƙafar kare haka ta dinga gudu,ita kanta batasan inda ta dosa ba,gudu kawai takeyi,
adaidai nan su Omar suka ƙaraso gidan uncle Abusufyan,Wayarshi ta shiga ruri,cikin sauri ya fiddota daga cikin aljihun wandonshi,yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanshi yayi sallama,
Muryar ɗaya daga cikin sojojin ce yaji yana cewa"Sir,munga yarinyar da ake nema,amma taƙi bari mu kama ta,'
Hankali tashe Omar yace"Kada ku bari ta kufce maku,kuyi ƙoƙari ku kamota,kuyi mata magana cikin sanyin murya,saboda yarinyar tana da tsoro sosai,kun firgitata ne shiyasa ta gudu,
"Okey sir,ya amsa mashi tare da katse kiran,
"Yalla6ai meya faru ne"!
Cike da takaici Omar yace"Major,an samu matsala!sojojin dana tura don su nemo mun jahad,sunyi arba da yarinyar gidan mu,dama na faÉ—a maka cewa kamanninsu sak iri É—aya,É—azu nace ma Osman Ya É—auko mun hoton fuskar hosana,saboda in tura masu suyi amfani dashi wurin nemo min jahad,to da wannan hoton su kayi amfani wurin nemanta shine Allah ya haÉ—asu da ita yarinyar da junaid yayi musanya da jahad,'
Tunda yasoma magana jahad ke kallonshi cike da mamakin wannan wani irin kamanni ne,dayasa har ba'a gane banbancinsu!?
Major yace"Amma nayi mamaki yalla6ai!wannan wata irin kamanceceniya ce atsakaninsu da har ba'a iya bambanta tsakaninsu"!
Omar yace"nikaina major abun ya jima yana ɗaure mun kai wlh,da farko nayi tunanin cewa saboda ƙaunar da nakeyi ma su hosana ne yasa nake ganin fuskarsu akan fuskar yarinyar,amma yau da junaid ya dauko jahad a matsayin ita yarinyar,sai na tabbatar da cewar ba gizau bane,tabbas kamanninsu ne ɗaya!
Major yace"abun mamaki abun al'ajabi!yalla6ai kada kace na cika ka da surutu,dan Allah yaya kuke da ita yarinyar?ko ƴar wurin uncle ɗinku ce,' ya ƙarasa maganar adaedae lokacin da yayi parking ɗin motar a cikin gidan Abusufyan,
murmushi Omar yayi tare da cewa"Æ´ar aikin gidanmu ce,sunanta Sehrish! Yarinyar tana da kirki sosai shiyasa Abbanmu ya mayar da ita tamkar É—iyarshi,yanzu amatsayin kanwarmu take............'
Waro ido waje Jahad tayi cike da tsananin mamaki ta furta"SEHRISH!!!!!!!!!!!!!!!!"
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.