Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Fitowa tayi daga kitchen ɗin hannunta ruƙe da tray mai ɗauke da ƙayataccen plate na fruits sai cup mai ɗauke da Hot tea sai faman tiririn Zafi yake yi,a natse take tafiya kai tsaye ta nufi stairs ɗin tana cikin tafiya kamar daga sama taji muryar haroon yana cewa"Wurin Namiji za'a ne"? A wani irin firgice ta juya tana neman ta inda zata ganshi,
 Yana zaune saman 3 seater shi kaɗai abunshi jikin shi na sanye da night dress riga dai dai guiwa,ya aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana faman sakar mata murmushi,
   Ba ƙaramin tsoro ya bata ba saboda bata tsammace shi a wannan lokacin ba,cikin sauri ta wuce upstairs gabanta na faɗuwa aranta tana cewa"Anya haroon Ba Aljani bane?in ba haka ba yaushe har ya shigo babban falon nan amma banga gifcin shi ba," tana tafiya tana sambatu aranta har ta ƙarasa part dinsa, sai da ta tsaya tare da dai daita natsuwarta sannan tashiga ciki, wayaam babu kowa a falon hakan na nufin yana a cikin bedroom dinsa,
Takawa tayi a hankali har zuwa ƙopar bedroom din nashi sannan tayi sallama,kusan sau uku ba'a amsa mata ba sai a na huɗun ne taji muryarshi ƙasa ƙasa ya amsa mata "come in,"
 a hankali tasa ƙafarta tashiga ciki,lokacin da ta ɗago da idanunta nan take taji faɗuwar gaba rasss!yanayin da taganshi yayi uban goho saman gadon yana fitar da numfashi daƙer daƙer ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tuni jikinta yayi mugun sanyi,ƙarasawa tayi ciki tare da ajiye mashi tray din saman table tace"Sannu da dawowa ga tea nan na kawo maka,ko akwai wani abu da kake buƙata"? shiru bai bata amsa ba sai numfashi kawai da yake fitarwa mai hucin zafi,bin shi tayi da kallo sumar kanshi ta rufe dukkan fuskarshi side by side,tana so ta tambaye shi ko lpy amma tana jin tsoro,
 Kusan 15 mins tana a tsaye bai ce komai ba ƙoƙari yake ya tashi amma sam jikinshi ya hana shi,sai da yayi dagaske sannan ya samu ya miƙe tare da matsowa ya sauko da legs dinsa ƙasa idanunshi a rufe rufff,fuskarshi ba ƙaramin canzawa tayi ba,jikin shi sai kerma yake yi tamkar wanda yashiga snow hatta pink lips dinsa sun gaza tsayuwa,tsananin tausayin shi ne ya kama sehrish saboda ta tabbatar da cewa bai da ƙoshin lpy sbd alamomin da tagani atattare dashi,tuni taji hawaye na ƙoƙarin zubowa daga idonta,
 muryarshi ce ta tsinkayeta da cewa"ki duba a cikin side drawer ɗina thete's a jotter wit pen pls bring it 4 me," cikin sauri sehrish ta matsa tare da kai hannu jikin side drawer ɗin,ta janyo gida na farko ajikinta, anan ta samu Jotter ɗin tare da biro,ɗaukowa tayi tare da miƙa mashi,
 daƙer ya cire hannunshi ya kar6a har lokacin eyes ɗinshi na'a rufe,aza jotter ɗin yayi daga gefen table ɗin gabanshi,buɗe papers din ciki yayi kafin ya aza biro din ya soma rubutu bayan ya kammala yayi tearing wurin da yayi rubutun ya ɗauko takardar ya miƙa ma Sehrish,cikin sauri tasa hannu ta kar6a tare da aza idonta kan rubutun wani irin handwritting gare shi domin koda ta kalla ko *A* bata iya ganewa ajiki ba hakan yasa ta kalle shi tare da cewa"Bangane menene ka rubuta ba,"ta faɗi a ɗan tsorace
"Go nd bring it 4 me," shine kawai abunda ya iya furta mata,
Cikin sauri sehrish ta kama hanyar fita daga bedroom É—in nashi tana waiwayonshi,
 Saukowa down stairs tayi tana faman cizon yatsa saboda tarasa gane menene ya rubuta mata,tamkar zatayi kuka,tana cikin wannan halin muryar haroon ta katse ta da cewa"Can I help u"? ɗagowa tayi aɗan razane tana kallon shi,fuskarnan tashi nadauke da murmushi yasa hannu ya kar6i takardar yana duba rubutun jiki,daga bisa ni yace"Ki jira ni anan yanzu zan dawo," yana fadin hakan yajuya da sauri ya shige part ɗinsu na nan downstairs,
ajiyar zuciya ta saki aranta tana Allah Allah saboda tsoron kada haroon ya tafka mata kuskure don tasan halin shi,bai da tabbas gajiya da tsayuwa tayi,don haka ta samu wuri saman last step na benen ta zauna tana jiran dawowarshi,.
Ba da jimawa ba sai gashi ya fito daga part din nasu, sai faman sauri yake yi irin da himmar nan hannun shi na ruƙe da syringe da kwalbar injection,tunkan ya ƙaraso sehrish ta miƙe tare da sa hannu ta kar6a tana yi mashi godiya,,
 da buɗar bakinsa sai cewa yayi"Ba sai kin gode mun ba,Aikin lada ne fa nidae burina ki kai mashi allurar ya hanzarta yi yanzu,in ma godiyar ce gobe da safe kinzo ki same ni kiyi mun ita," yana magana yana sakin wannan shu'umin murmushin nasa,
jiki asanyaye tasa hannu ta kar6a tana kallon fuskarshi shima kuma ita yake kallo da wannan murmushin nashi, cikin sauri ta juya tare da hayewa upstairs cikin sauri take tattaka matattakalar benen har ta wuce part dinsa
Ruƙe qugu haroon yayi tare da sakin wani irin bazawarin murmushi yace"Lokacin Bacci yayi bari naje na kwanta gobe da safe akwai labari zazzafa,ƴar shila zata zo miƙo mun godiya da kanta," ya fadi tare da sakin dariya ya wuce sashen shi
 Lokacin da sehrish ta koma ɗakin nashi yarda tabarshi haka ta same shi zaune idonshi a rufe, cikin sauri ta ƙarasa tare da miƙa mashi allurar da sirinjin tace"Ga allurar," hannu Sgr yasa ya kar6a daƙer ya iya buɗe idonshi sam baya iya gane wace kalar allura ce yarinyar ta kawo mashi saboda idanunshi biji biji suke gani hakan bai bashi damar karanta abunda aka rubuta ajikin ƙaramar kwalbar allurar ba,
  fasa bakin kwalbar yayi tare da curo sirinjin ya fiddo da kan allurar ya tsoma acikin kwalbar ya zuƙo ruwan allurar iya yadda yasan ya dace yayiwa kanshi,
.Tuni jikin sehrish ya soma rawa saboda tsoron allura gareta,cikin sauri ta kama hanyar fita daga dakin saboda ta bashi damar yin allurar,
 Muryarshi ce ta tsinkayeta da cewa"kada ki tafi," ya furta yana faman sakin huci daga bakin shi da hancinsa,
A bakin ƙopar ta tsaya idonta a rufe jikinta na kerma,muryarshi ta kuma ji yace"ki zo," cikin sauri ta koma ajiyar zuciya tasaki ganin harya kammala yin allurar, miƙa mata kwalbar allurar yayi tare da syringe din duka yace"kisa a dustbin," amsa mashi tayi tare da kar6a ta wuce wurin bedroom dustbin dinshi ta saka tarkacen allurar, sannan ta dawo ta tsaya tana jiran jin ko zai buƙaci wani abu tunda ya nuna baison ta tafi,
 Lokacin da allurar ta gama gauraye ko'ina na jikinshi da wani irin ƙarfi ya ware idanunshi azare,har sai da sehrish taɗan ja da baya saboda firgitar da tayi,bin yatsun hannunshi tayi da kallo ganin yarda yake wawwaresu suna miƙewa tsaye,tamkar dae yadda mutun ke komawa Zombie acikin film,gabanta ne yashiga faɗuwa saboda tsoran da taji murya na rawa tace"Zan iya tafiya"?
 ɗagowa yayi da wannan sexy blue eyes din nashi da launinsu ya ƙara Cizawa gwanin ban tsoro kai kana ganinsu kasancewa akwai matsala,ido cikin ido yake kallonta batare da ya kawar da idonshi ba hakan yasa zuciyarta ƙara karaya ga wani irin fargaba daya zo mata,ganin irin kallon da yake yi mata ne yasa nan take tadinga jin bugun zuciya,ja da baya ta soma yi jikinta na kerma har lokacin bai janye idonshi daga kanta ba bin ta kawai yayi da kallo,sai da taga taɗanyi mashi nisa sannan ta nufi hanyar fita daga bedroom din nashi da saurin gaske sai dai ina, kafin ta Ankara tuni SGR yayi wani irin kwakkwaran motsi tare da miƙewa tamkar wani Zaki ya bi bayanta azafafe yakai ma Waist ɗinta wani irin ruƙo ya ɗaga ta sama gaba ɗaya ta saki wata irin razananniyar ƙara mai rikitarwa bata gama rufe bakinta ba yayi wani irin wurgi da ita kai tsaye ta faɗa tsakiyar gadon shi yaraaaff tuni mayafin da tayi rolling dashi ya jima da barin jikinta !!!! Ba ƙaramin buguwa sehrish tayi ba daƙer ta iya tayar da kanta daga jikin bedmattress ɗin ta ɗago hankali a matuƙar tashe take kallon shi ganin yasanya hannayenshi tare da ruƙo shirt ɗin dake ajikinshi ya cire ta gaba ɗaya tare da yin wurgi da ita ƙasa,
  gabanta ne yasake yin wani irin mugun bugu tuni hawaye sun soma wanke mata fuskarta cikin tsananin tashin hankali take girgiza mashi kai tana cewa"innalalahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga uku !!!!"
  Sam babu alamar sassauci a tattare dashi kai kana ganin yanayin action dinsa zakasan cewa ba a hayacinshi yake ba, Hatta Æ™arfin jikinshi bana shi bane a matsayin shi na wanda bai da Cikakiyar lafiya, Ganin ya zame belt É—in wandon jikinshi gaba daya yayi throwing dinsa, tare da sa hannu yana Æ™oÆ™arin zame wandon dake jikinshi, hakan ya Æ™ara tsoratar da sehrish yunÆ™uri tayi da Æ™arfi zata diro daga saman gadon ta gudu,aikuwa batayi wani aune ba taji saukarshi saman gadon gaba É—aya ya afka mata tare da yi mata Rumfa da faffaÉ—an Æ™irjinshi tsulundum taji ta ajikinshi,🙆ðŸ½â€â™€
 nan fa ido ya raina fata,dukkan ilahirin jikinta rawa yake yi gaba ɗaya tagama rikicewa muryarta har wani shaƙewa take yi wurin cewa"Dan Allah kayi haƙuri kabarni na tafi,ni nasan cewa ba halinka ba....ba yin kanka bane.......' kasa ƙarasa maganar tayi saboda idonshi dake kallon cikin kwayar idon nata,SGR fa a halin yanzu zamu iya cewa baya ji baya gani,
  Wani irin huci yake yi yana groaning just like a hungry lion,runtse idonta tayi saboda bazata juri kallon cikin nashi ba yayin da idonta ke cigaba da zubar da hawaye...........🙆ðŸ»â€â™€ï¸ðŸ™†ðŸ»â€â™‚ï¸ðŸ˜?
Zuwa ga masu share na littafina lokacin da mutun zai sayi littafin nan ba muyi yarjejeniya nacewa zai turama wasu ba, amma sai gashi grp ba iyaka ana tura littafin koma waye yaje don kanshi kuma yasani akwai haƙƙina akanshiðŸ‘ya Allah kashiga tsakanina da koma waye,
*************
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.