Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  katse kiran ayaan yayi tare da mayar da wayar inda ya ɗaukota ya ajiye,
 Cikin ƴan mintuna saiga Jahan ya fito daga cikin bankin hannunshi ruƙe da jaka,
 Yana ƙarasawa gaban motar ya buɗe back seat dinta tare da yin wurgi da jakar ciki, sannan ya rufe ya kuma buɗe front seat ɗin ya shiga ya zauna a gefen Ayaan dake zaune a driver seat,
 "Yau dae zamu jefar da kwallon mangwaro mu huta da kuda," acewar Jahan,murmushi ayaan ya saki yana kallon shi yace"baka ji daÉ—in da nakeji ba wlh,saboda a Æ™agare nake da mu bashi kuÉ—in nan mu huta da shegen nacin nan nashi,ya takurama rayuwarmu gaba É—aya,Haroon bai da imani jahan," fuskarshi a yamutse yayi maganar.Â
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
ï¿?
  Â
  "har yau in na tuna abunda yayi mana zuciyata tafarfasa takeyi mun saboda 6acin rai,haroon ya wulaÆ™anta arayuwarmu,Allah bazai ta6a barin shi ba, Insha Allah Æ™arshen shi bazaiyi kyau ba," acewar jahanÂ
 Jinjina kai Ayaan yayi kafin yace"amma Jahan kana tunanin in muka bashi kuɗin nan zai goge video ɗin duka?am just doubting about it,don na lura ba ƙaramin shaiɗani bane,
  jahan yace "ae ba zamu bashi kuÉ—in ba har sai mun tabbatar daya goge videon agabanmu mun gani,"Â
  "Duk da haka nidae ina fargaba wlh," cike da damuwa ayaaan yayi maganar,
 Sun jima suna magana kafin daga bisani Ayaan ya tashi motar suka miƙi hanyar gida,babu wanda ke ma wani magana acikin motar saboda duk sun tafi duniyar tunani, gaba ɗaya zulluminsu akan haroon,
 Koda suka ƙarasa cikin gidan basu shiga da kuɗin ba,acikin motar suka barsu cikin jakar saboda tsaro, sun ajiyeta ne da nufin in dare yayi suzo su ɗauketa su kai mashi,
  Bayan sun fito daga motar kaitsaye suka shiga cikin gidan tare da wucewa bedroom ɗinsu don rage gajiyar da suka kwaso,
Sehrish
Tasha kuka kamar kamar me,har sai da zazza6i da ciwon kai mai tsanani suka rufar mata sannan ta lalla6a ta haye saman gadonta ta kwanta,ta jima tana roƙon Allah akan yasa mafarki ne ba gaske ba,abunda ya faru tsakaninta da Aunty azmeenta,gaba ɗaya jikinta baya mata daɗi saboda dama can akwai fargar haroon dake damunta ga kuma wani ciwon kan ya taso mata na Azmee,duk ita kaɗae😢
 ta jima tana juyi asaman gadon amma bacci yaƙi ɗaukarta sai ma ciwon nata dake ƙara gaba,fuskarta harta fara kumbura saboda kukan da tasha,dakyar ta lalla6a ta tashi jikinta na kerma ta wuce toilet jin an fara kiran sallar la'asar,bayan wasu ƴan mintina tafito daga ciki tana faman ƙanƙame jikinta saboda sanyin daya rufar mata gashi ta ta6a ruwa,
  wurin wardrobe ɗinta ta wuce tare da buɗeta, ta zura hannu ta ɗauki hijab ɗinta ta zurata ajikinta sannan ta ɗauko carpet ta shimfiɗa,sam babu natsuwa ajikinta haka ta kabbara sallar tana karanta fatiha hawaye na wanko mata a fuskarta a haka ta kammala sallar tare da zama saman dardumar ta ɗaga hannayenta sama cikin shessheƙar kuka tashiga cewa"Ya Allah kasa aunty azmee tadawo cikin hayyacinta ta gane cewa ni ba ƙarya nake mata ba,bansan ya zanyi ba in ta juyamin baya,Ya Allah ka yayemun damuwar da nake ciki,ka kawomin sauƙi acikin rayuwata.........' sosai sehrish tashiga jera addu'o'i tana roƙon Allah akan abubuwan dake damunta,
Karanta>>>Â Kishi Da Aljan Complete Novel Document
  ta jima zaune saman dardumar tana tunanin maganganun aunty azmee,har lokacin tana kokwantan cewa anya Aunty azmee tana a cikin hayyacinta kuwa,
  Har kusan Æ™arfe biyar sehrish bata motsa ba tana zaune zugudun,sai da biyar da rabi ta buga,sannan ta tashi jiki a mace ta cire hijabin tare da naÉ—e carpet É—in duka ta haÉ—a ta jefa asaman gadonta,cikin toilet tashiga ta wanko fuskarta sannan ta fito ta É—auki mayafi acikin wardrobe É—inta ta yafa shi asaman kanta, sannan ta buÉ—e Æ™opar É—akin ta fito,Â
 Kitchen ta wuce saboda sanin cewa suna da aikin dinner,lokacin da ta ƙarasa kitchen ɗin tuni Azmee har tayi nisa a aikin nata,shiga ciki sehrish tayi tare da tsayawa tana kallon azmee dake tsaye agaban kitchen sink tana wanke naman da ta ɗebo acikin roba,
Gabanta na faɗuwa tace"Sannu da aiki aunty azmee," tamkar bata ji taba haka ta shareta, kusan sau uku sehrish na maimaita maganar amma taƙi amsawa,
  Jiki asanyaye sehrish ta ƙarasa gaban chopping board ganin ta jera vegetables ɗin da zata yayyanka, hannu takai zata ɗauki wuƙa,muryar azmee ce ta katse ta da cewa"kada ki ta6amun komai! Zanyi aikina ni kaɗai kamar yadda nasaba yi lokacin da baki nan,don haka ki fuce kibarmun kitchen ɗin....' fuska aɗaure tayi maganar batare da ta juyo ta kalli. sehrish ba,
. cikin tashin hankali sehrish tace"meyasa kika ce haka aunty azmee?tare muka saba yin aiki amma yau ke da kanki kike korata!?Â
  rai a6ace azmee ta ɗago tare da nuna mata hanyar fita tace"dan Allah sehrish ki fuce kiban wuri!aikine nace bana so ni zanyi kayana,bana buƙatar taimakon ki,
  ganin yarda azmee ke kwatsa mata tsawa yasata fashe wa da matsanancin kuka tana cewa"aunty azmee dan Allah kada kiyimun haka, nasaba dake na ɗauke ki tamkar mahaifiyata,wlh bazan iya yi maki ƙarya ba,ni bansan akan me kike magana ba,dan Allah kada kiyi fushi dani akan abunda banda masaniya akanshi,"!
 tunda tasoma magana azmee ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah,tamarasa me zatayi ma Sehrish ta huce,ƙiri ƙiri tana neman raina mata wayau,
  "Sehrish in har kinason na kuma yarda dake to ki faÉ—amun gaskiya waye kika bani acct number dinsa na tura kuÉ—in dana baki naira dubu É—ari tara da kikayi mun Æ™aryar cewa Æ´an uwankine basa lafiya!!?Â
 Jinkirtawa sehrish tayi daga kukan da takeyi tana tunanin wai ma ina takai kuÉ—in?bama wannan ba yaushe ta amshi kuÉ—in?Â
  "Ina sauraronki"! Muryar azmee ce ta katse ta daga tunanin da ta tafi,
  girgiza kai tashiga yi tana cewa"aunty azmee kiyi haƙuri amma ni bansan me kike magana akai ba,"
  tabbas in taci gaba da sauraron Sehrish ranta zai cigaba da 6aci ne don haka tace"ki wuce kiban wuri banasan sake jin wata magana daga bakin ki," jiki asanyaye sehrish ta juya tare da barin kitchen ɗin,
  a hankali take tafiya jikinta ba kwari,
 "Sehrish"! Muryar junaid ce ta katse ta,a hankali ta ɗago ta kalli gefen hagunta ta inda yake tunkarota,shigowar shi kenann cikin babban falon,
  tunkan ya ƙarasa ya lura da yanyinta,tsayawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta da tayi suntum saboda kukan data sha,
  Cikin sanyin murya yace"reeeesh! Meya faru ne kike kuka?
  ganin cewa bata da wanda zata faɗawa mawa face junaid tunda shine abokin shawararta, don haka ta sanar dashi dukkan abunda ya faru da ita, tsakaninta da aunty azmee
  Cike da mamaki junaid ke kallonta tamkar mai nazarin wani abu can dae yace"sehrish saboda me za kiyima aunty azmee Æ™arya?meyasa zaki ce mata baki da wasu Æ´an uwa?Â
  gaba ɗaya sehrish tagama ruɗewa cikin tashin hankali tace"junaid wlh bani da ƴan uwa,ni bani da kowa ba ƙarya nayi mata ba,'
  harara yaɗan watsa mata kafin yace"idan har dagaske baki da ƴan uwa,to su wanene kike kira a wayata? Lokacin da kike ɗaukar mun phone ɗina batare da sani na ba?kin manta last time har na nuna maki message ɗin da ƴar uwarki ta turo a wayata?sannan har kika roƙeni akan na kaiki ki gansu? A lokacin nace maki ki bari sai babban yayanmu sun koma Us ni da kaina zan kaiki ki gansu ko shi ma duk kin manta? Ya ƙarasa maganar cike da tuhuma,
  wani irin jiri sehrish tadinga gani a indonta,a hankali tashiga furta "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!!!" ganin tana ƙoƙarin zubewa yasa shi yin saurin ruƙo shoulders ɗinta yana cewa"ko baki da lafiya ne"? Ya tambaya yana kallon eyes ɗinta dake a rufe,
.....daƙyar ta iya furta cewa"junaid inaso nashiga bedroom ɗina,inaso na kwanta,"
  gaba ɗaya sehrish tayi confusing ɗinshi lamarin ya ɗaure mashi kai,ruƙo hannunta yayi ya taimaka mata suka nufi bedroom ɗinta,buɗe mata yayi tashiga ciki, sai da yaga ta kwanta saman gadon sannan ya rufo mata ɗakin,
 Cikin sauri ya wuce kitchen wurin Azmee,da sallama yashiga kitchen ɗin a lokacin tana tsaye agaban gass tana motsa farfesun data ɗaura,jin muryarshi yasa ta juyo wa fuskarta babu fara saboda ruɗin da sehrish ta jefa ta aciki,
Amsa mashi sallamar tayi sannan tace"junaid kana buÆ™atar wani abune"?Â
  girgiza kai yayi alamar a'a Sannan yace"dama kan maganar sehrish ne,ta faÉ—amun duk abunda ya faru,bansan meke damunta ba,ni kaina tayi confusing É—ina,"Â
  "Junaid sehrish tayimun Æ™arya,ban ta6a tunanin haka daga wurinta ba,meyasa za tayimun Æ™aryar cewa tana da Æ´an uwa,bayan ba haka bane saboda kawai ta cimma wani buri nata shine ta shiryamun plan,"!Â
Karanta>>>Â Shakuwa Ce Complete Novel Document
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.