Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة ØØ¨ رومانسية بين Ø³ØØ±ÙŠØ´ ÙˆØ§Ù„Ø¬Ø±Ø§Ø Ø§Ù„Ø¹Ø§Ù… Ø±ÙØ§ÙŠØªðŸ’‹ðŸ’˜â¤ðŸ¤â¤ðŸ’•💖
Ansamu long page🥱
________________________Zuba mashi ido su kayi suna jiran amsa,Omar yace"pls ka faÉ—a mana gaskiya kawai,wacece wani abu ya shiga tsakaninka da ita har akasha wannan Love haka?kaga dai daga ni sai Abba babu wanda zaiji abun da ya faru,"wani irin kallo sgr ya wurga yana mashi Æ´ar harara yace"Omar bana so, ka fara ko"?
 Murmushi Abban nasu yayi kafin yace"abunda Omar ya faɗa gaskiya ne,Son bai kamata ka 6oye mana komai ba tunda Allah dai yasa yau asirikinka ya tonu munga komai,ashe kana kula mata har romance kake dasu asaman gado ko?faɗamun ƴarwa ka kwamushe acikin ɗakinka har akai abun arziƙin nan bansani ba,"cike da zolaya Abban nasu ke magana,
 ɗaure fuska Sgr yayi tare da haɗe girarsa wuri guda ya tsuke small lips ɗinshi yana kallonsu,yarda suka tasa shi gaba suna tuhumarshi kamar wani ƙaramin yaro ba ƙaramin hasala shi yayi ba,gashi sam ya rasa amsar da zai basu tunda bai isa ya ƙaryata abunda suka gani ba asaman ƙirjinshi,don shi kanshi a ruɗe yake da lamarin abun ya ɗaure mashi kai,taya aka samu jan bakin mace raɗau haka asaman ƙirjinshi!?bai gama zancen zucin nashi ba muryar Omar ta katse mashi tunani,
 "Abba zargi fa ya tabbata,kalli ka gani,"Omar ne yayi maganar yayin da yake ruƙo mayafin sehrish dake a ƙasan laps ɗin Sgr ya danne shi,
  dafe kirji abban nasu yayi cike da razana yace"ƙalu innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Rafayet!wannan fa?ya akai yazo wurinka"?ya tambaya hankali tashe yana kallonshi,
Runtse ido sehrish tayi daga 6oyen da take bayan labulen É—akin,hada Æ´an matan hawayenta saboda tsoran hukuncin da zata kar6a,
 Cikin sauri sgr ya aza eyes ɗinshi akan mayafin da Omar ya ruƙo a hannunshi just speechless,amace bakin shi ya mutu yama rasa bakin magana abun ya zarce tunaninshi,
 Omar ne yace"Abba tunda kaga yayi tsit ya gaza magana,to ya aikata ɗinne kasan mara gaskiya,ni fatan da nakeyi ma Allah yasa iya mayafi ya cire mata bai........'kasa ƙarasa maganar yayi saboda saukar pillow daya ji a saman fuskarshi,hannu yakai zai ƙara rarumar wani pillow abban nasu ya dakatar dashi da cewa"Wannan fa alamar rashin gaskiya ce,tun ɗazu kaƙi buɗe baki ka ce uffan,sai faman ƴan kame kame kakeyi mana,kaji tsoran Allah ka faɗa mana gaskiya,Rafayet yin hakan kuskure ne bai kamata don kana ra'ayin mace ka runƙa kawota har bedroom ɗinka ba asaman gadonka don ka rage zafi da ita ba,in kaga yarinya kanaso Ni zakayi ma magana sai aje masallaci ashafa fatiha kaga shikenan sai a kawo maka ita ɗakinka babu mai jin kanku,taka ce halak malak.....'
 Zare blue eyes ɗinshi yayi yana kallon Abban nashi,rai a6ace ya ciji la66ansa tare da ɗago pillown hannunshi ya ɗaga sama zai jefa ma Abban nasu a saman fuskarshi,sai kuma ya saki filon a saman katifar,
  Ganin ya dakata yasa Abban nasu cewa"ae fa kai yanzu komai ma zaka iya,saurayin da zai iya kawo mace ɗakinshi har saman gadonshi acikin gidan ubansa meke bazai iya ba Omar? Ya ƙarasa maganar yana kallon Omar dake ƙumshe da dariya yace"of course Abba,ina goyon bayan maganar ka,yanzu sai dai mu bishi da addu'a don na lura yarinyar ba ƙaramin zautar dashi tayi ba tunda gashi har ya gaza buɗe bakinshi yayi mana magana,rashin gaskiya dai baiyi ba,"
 gaba ɗaya sun gama hasala Sgr,yama rasa amsar da zai basu su dukansu,a ƙarshe ma daya rasa abunyi kawai sai ya fashe da dariya unexpected,tsananin mamaki ne ya kamasu ganin Sgr yana 6a66aka dariya yau shi da kanshi,yaushe rabon da suga sgr yayi dariya irin haka,white teeth ɗinsa sun fito rairasss,da wuya kaga yana dariya sai dai wannan murmushin nashi na gefen fuska shima kuma in kaga yayi wannan murmushin tofa zai bada horo ne,don ya iya murmushin mugunta,
  Hannu sehrish tasa a hankali ta ɗan yaye labulen tana leƙensu,ba ƙaramin bugun zuciya taji ba,kasa janye idonta tayi daga kallon kyakkyawar fuskar sgr da yake ta faman dariya kamar zautacce,gaba ɗaya dimples ɗin fuskarshi sun lotsa sosai abun ba'a magana sai wanda ya gani,suman tsaye sehrish tayi amace ta mace wurin kallon fuskarshi,aranta tana maimaita kalmar nan"tabarakallahu ahsanun khaliqin,"
  Har wani duƙar da kanshi yake yi ƙasa yana dariyar hakan yasa sumar kanshi ta ɗan yarfo ta gaban fuskarshi,
 Atare Omar da Abbansu suka haɗa baki wurin cewa"ikon Allah,abun mamaki abun al'ajabi,"
  Tsagaitawa yayi da dariyar lokaci guda ya ɗaure fuskarshi tamkar dariya bata ta6a wanzuwa a fuskarshi ba,takaici ne dama ya ishe shi shiyasa ya fashe da dariyar,
 Cikin sanyin murya yace"joking aside pls,abba nikaina bansan ya akai nasamu zanen lips ɗin nan asaman chest ɗina ba,sannan bansan ya akai mayafin nan yazo bedroom ɗina ba,na rasa ta yarda zansa kuyi understanding ɗina,gaba ɗaya kunyi confusing ɗina,kun tsareni da tambaya kamar wasu lauyoyi,that's why nayi shiru bance komai ba,"ya ƙarasa maganar a kasalance,
  Murmushi Abban su ya saki yana kallon face ɗinshi,bakomai ya faɗo mashi araiba face Mommynsu,komai na fuskarshi irin na mahaifiyarshi ne,yafi kama da ita amma akwai wasu abubuwan daya ɗauko na Abbansu,
  "Zan shiga toilet,"ya faɗi tare da saukowa daga saman gadon ya kama hanyar shiga toilet ɗin,
  Bin bayanshi su kayi da kallo har ya shige cikin toilet ɗin,
Sannan Suka janye idanunsu,cikin sauri Omar ya samu wuri tare da zaunawa yana fuskantar abbansu ya ruƙo hannunshi tare da cewa"Abba,dan Allah ka aurar damu tare, nida Rafayet,kayi mun wannan alfarmar"
 Murmushi Abbansu ya ɗanyi kafin yace"Omar bangane me kake nufi ba,har yanzu ɗan uwanka bai janye ra'ayin shi akan mace ba,ni kuma banson na takura mashi,duk da banda burin daya wuce wannan nima,inaso naga auran kowanne daga cikinku,musamman auran shi saboda ina tunanin cewa in soyayya ta shiga zuciyarshi zai rage wannan zafin kan nashi,zai sassauto ya zama tamkar kowa,idan har rafayet baiyi aure ba ya tsaya akan bakanshi,tabbas za'ayi asarar namiji har namiji Omar,bansan ya zanyi dashi ba,"yanayin da abban nasu yayi maganar zai tabbatar maka da cewa abun ba ƙaramin ciwo yake masa ba,
 "Abba kadaina cewa bakasan yarda zaka yi dashi ba,shifa ɗanka ne halak malak Allah ya mallaka maka,kuma kana da iko Akanshi,idan yau kaso Abba gaba ɗayanmu zaka iya yi mana aure batare da son ranmu ba ko batare da saninmu ba kuma dole muyi maka biyayya,"
  zuba mashi ido Abban yayi yana sauraran bayanin shi,
Ƙasa ƙasa da murya Omar yayi gudun kada Sgr yafito daga cikin toilet ɗin yaji abunda suke tattaunawa,
 Yasa shi yin hakan sannan yaci gaba da cewa"Abba,namiji irin rafayet,aure akeyi masu batare da saninsu ba,sai dai kawai suji an ɗaura auran... "
 Katse shi abban nasu yayi da cewa"baka tunanin cewa zai iya sakin matar anan take,kasan shifa ba'ayi mashi dole,"?
   Murmushi Omar yayi tare da cewa"Abba ka fahimta mana,kaifa kake iko dashi,ka sama mashi mace ta gari wadda kasan cewa bazaiyi dana sanin zama da ita ba,ko kuma ni kaban za6i zan sama mashi macen data dace da rayuwarshi,ka aura mashi ita batare da sanin shi ba,sai bayan an ɗaura auran ka ware rana ɗaya ka sanar dashi cewa Umarnine ka bashi amatsayinka na mahaifinshi,in ya kuskure kuma yasan sauran,"
 dariya sosai Abbansu yayi yana sauraron omar dakyar ya tsagaita da dariyar yace"Omar ka iya zolaya Allah kamar mahaifiyarku,yanzu rafayet kakeso nayima auren dole?so kake ya tashi bomb acikin gidan nan"?
 "Abba baka fahimce ni ba,tunda muka taso tare da ɗan uwana,komai namu iri ɗaya muke yinshi tamkar twins haka muke,duk abunda nayi rafayet sai yayi shi,haka shima duk abunda yayi nima saina yi shi,yanzu abba aure ne zai banbanta ni da ɗan uwana"?
 In serious matter Omar ke magana,wannan yasa Abban nasu ya gane cewa ba zolaya bace yake mashi,har cikin ranshi yake maganar kuma ba ƙaramin jin abun yake ba acikin zuciyarshi,bai gama zancen zucin nashi ba omar yaci gaba da cewa"Abba tuntuni ban ta6a sanar dakai ba,amma yau zan sanar dakai komai,najima inason na cika maka burinka na ganin cewa munyi aure, ba don komai ba sai don saboda farin cikinka,bakomai ne yasa nayi jinkirin yin aure ba face Rafayet!inason aure bawai banaso ba,rafayet shine dalilin dayasa naƙi yin aure,saboda ina ganin cewa kamar banyi mashi adalci ba,inna riga shi yin aure,saboda mun saba komai atare duk wani cigaban da zamu samu atare muke samun shi abba,taya zanso na samu wannan babban cigaban batare da ɗan uwana ba"? Ya ƙarasa maganar muryarshi asanyaye yana kallon Abban nasu,
Gaba ɗaya Omar ya gama kashe ma Abban nasu jiki,ba ƙaramin tausaya mashi yayi ba,lalle ba ƙaramar shaƙuwa bace a tsakanin shi da ɗan uwanshi ba,tun da har zai iya hana kanshi wani jin daɗi na rayuwarshi saboda ganin cewa tamkar baiyi mashi adalci bane,
  "Abba,na jima ina jiran ganin cewa ɗan uwana ya fara soyayya koya fara maganar aure,amma har yanzu ba wani sauyi abun ba ƙaramin ta6amin zuciyata yake ba,bana faɗi ne kawai saboda nasan faɗin bashi da amfani zan 6ata bakina ne kawae,sau da yawa ina janshi da fira akan mace don na bugi cikinshi naji koya fara ra'ayin yin aure amma kullum babu wani cigaba game da haka,Abba rafayet shine yasa Omar ɗinka ƙin yin soyayya tun da jimawa kuma shine ya hana nayi aure,wanda bani da burin daya wuce wannan arayuwata....,.......'
 Kasa ƙarasa maganar yayi saboda siririn hawayen daya zubo mashi a idonshi na hannun dama,
 Cikin sauri abban nasu ya sanya hannunshi tare da yin saurin goge masu shi yace"Omar ban ta6a tunanin haka ba,meyasa tuntuni baka sanar dani wannan maganar ba?meyasa nagaza fahimtarku amatsayina na mahaifinku?ashe shaƙuwar dake tsakaninku har takai haka?nagode ma Allah sosai da kuka kasance masu son junanku,ina matuƙar alfahari daku ƴa'ƴana," magana yakeyi yayin da idanunshi suke cike tab da kwalla,
 Sehrish kuwa dake la6e bayan labule sai faman shessheÆ™ar kuka takeyi ta rufe bakinta da tafukan dukkan hannuwanta,tsananin tausayinsu ne ya kamata,tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin Æ´an uwa masu matuÆ™ar Æ™aunar junansu ba irin ahalin salahuddeen hussein,akwai soyayya da shaÆ™uwa tsakaninsu,zumuncin dake tsakaninsu mai Æ™arfi ne sosai,da ace kowane ahali zasu kasance haka da ba Æ™aramin cigaba za'asamu ba,amma yanzu zamanin da muke ciki,babu wannan soyayyar atsakanin shaÆ™iÆ™ai ma,sai kaga na waje ma wani can yafika kusanci da É—an uwanka shaÆ™iÆ™inka,idan kuwa akazo kan shiga matsala ko damuwa tofa zaka ga mutum indai bashi ta shafa ba,babu ruwanshi da damuwa akan halin da É—an uwanshi yake ciki,sai ma ya kasance É—an uwanka yana cikin Æ™unci da matsanancin damuwa,amma kai kuma hankalinka kwance sai ma ajika kana ta faman tiÆ™ar dariya,mai makon arunÆ™a jajantawa juna,shiyasa dayawa zaka ga na waje ma wani yafika kusanci dashi saboda yafi damuwa da É—an uwan naka,wanda dayawa hakan ke jefa rayuwar É—an uwan cikin hatsari,ba'a janshi ajiki cikin gida tun daga iyayen har Æ´an uwan,bakamar salahuddeen hussein ba, ya É—auki Æ´a'Æ´anshi tamkar abokanan shi,Æ™aramin É—anshi ma tamkar amininshi ya mayar dashi,kuma hakan yasa basa jin shakkar sanar da mahaifinsu abu in ya same su,ko neman shawara awurinshi,wanda a yanzu zaka ga cewa wani a gidansu tsoro ma yake ji ya sanar cewa wani na cutar dashi awaje,saboda wasu iyaye basa tsayawa su fahimci Æ´a'Æ´ansu daga sun ji abu sai afara hantarar mutum in Æ™arami ne kaga an haÉ—a mashi da bugu ma,babu wannan shaÆ™uwar ta iyaye,da Æ´an uwantaka da har mutum zai iya faÉ—in damuwarshi acikin gidansu,sai dae ya nemi abokinshi ya sanar dashi halin da yake ciki instead of wani nashi nakusa dashi,daga nan kuma awajen in Allah yasa abokin ba nagari bane shine zaka ga anzo ana danasani, don mafi akasarin mutane na fadawa mugun hali ne ta sanadiyyar abokai,ku yi koyi da wannan ahalin wurin nuna ma junanku soyayya,ku zama naku ku kaÉ—ai babu mai jin kanku👌ðŸ‘
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.