Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
  ɗagowa jahad tayi ta kalli hossana gaba ɗayansu jikin su yayi mugun sanyi, duk basu ji daɗin cewa ya omar yana da mata ba, sam hossana ta gaza jurewa komawa tayi saman 2 seater ta faɗa tare da kifa kanta tana kuka, jahad kuwa kitchen ta wuce saboda tabaro dankalin da take soya masu, ita kanta jurewa kawai take yi amma ba ƙaramin ɗaci taji ba na jin cewa ya Omar dinsu yana da aure, tsayawa tayi agaban fan din dake asaman gass sam ta kasa juya dankalin saboda tashin hankali, cikin sanyin murya tace"koma wacece matar shi ina tayata murna sosai, domin kuwa tayi dacen miji nagari........' kwalla ce ta zubo daga idonta ɗas ta zuba ƙasa, 😖
ï¿?
  Shigowa omar yayi cikin falon nashi, sehrish na ganin shi nan da nan ta shiga natsuwarta,Â
 "Ina kwana ya omar"?Â
 kallonta yayi tare da sakar mata murmushi yace"lfy lou Alhmdllh, ki zauna mana," ya faÉ—i tare da samun wuri ya zauna asaman 3 seater,Â
wuri tasamu itama ta zauna suna fuskantar juna,
  sunnar dakai tayi ƙasa tana jiran jin mai zai ce mata,
 Cikin natsuwa ya soma magana "Am really sorry abt wht happend last night, banji daÉ—in abunda sgr yayi maki ba, nasan abun zai tsaya maki aranki,amma inaso ki sani ba yin kanshi bane! wannan allurar ce da kika kai mashi ya sanar dani cewa ke kika kai mashi ita...........' hankali tashe sehrish take kallon shi a tunaninta sgr ya tuna abunda ya faru ne,Â
 Cigaba da magana omar yayi anatse yace"Calm down ur mind, sgr ba zai iya tuna abunda ya faru ba a yanzu amma fa dole ya tuna wata rana abun zai dawo mashi ne akan shi, so nake ki fadamun a ina kika samu allurar da kika kai mashi ? Da sanin ki kika kai mashi ita? Ya tambaya yana kallon fuskarta cike da tuhuma ,
 Lokaci guda duk ta dabarbarce ta rasa natsuwarta,Â
  " Tell me the truth who brought it to u? don nasan ba ke kika dauko ta ba, in fact bamu da irinta acikin gidan nan...'
  shiru tayi tana kallon shi zuciyarta na raya mata ta fada mashi gaskiya kawai,
  murya na rawa tace"Ya omar ni ba da sani na ba Allah, babban yaya yayi mun rubutu a paper ya bani, ko a lokacin sai da nace mashi ni bansan meya rubuta ajiki ba, amma yace mun naje na É—auko mashi kawai saboda baya cikin hayyacin shi ne, lokacin dana fito da takardar a hannuna ina zullumin meya rubuta ajiki shine kawai sai ga h.....h.....' wani irin ruÆ™o taji anyima maÆ™oshinta tamkar wani abu ya tokare wurin,nan take taji numfashinta na shirin É—aukewa gaba É—aya, kakari tashiga yi tana Æ™oÆ™arin furta sunan haroon amma sound É—in ya Æ™i fidduwa daga bakinta, abun mamaki abun al'ajabi,Â
 Ganin yarda zufa ke tsattsafo mata gefe da gefen fuskarta gashi sai faman numfarfashi take yi sama sama,
 Hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba cikin sauri yace"Ke lafiya meke faruwa ne? Ko baki da lafiya ne?
  cikin kuka tace"maƙoshina ne ke mun ciwo, nagaza furta sunan wanda yaban allurar raɗaɗi nake ji a wurin,
  tashi marshal omar yayi tare da ƙarasawa wurin frigde din dake a falon shi, buɗe wa yayi tare da ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya dawo ya zauna dab da sehrish ya buɗe murfin robar ya miƙa mata, cikin sauri ta kar6a tana sha sai da tashanye kusan rabi sannan ta janye tana faman sauke ajiyar zuciya,
 Hannu omar yasaka tare da kar6a robar daga hannunta yasanya murfin ya rufe sannan ya ajiye robar ruwan a ƙasa, mayar da idonshi yayi akan sehrish sannan cikin natsuwa yace"pls taimako nake so kiyi mana,bansan wacece ke ba amma har a raina naji, na yarda dake dan Allah karki sa na fara zarginki, ki fadamun gaskiya wanene ya baki allurar da kika kai mashi? allura ce mai haɗarin gaske a lokacin da Allah baisa na faɗo na ceceki a hannun shi ba tabbas ba zaki rayu ba....
  Hankali atashe sehrish ta ɗago idanunta tana kallon shi, nan da nan taji wasu hawayen sun sake wanko mata fuskarta cikin shessheƙar kuka tace"ya omar wlh ni bansan komai akai ba bazan iya cutar dashi ba kuma nima bazan so na cutar da kaina ba..........'
  jinjina kanshi yayi tare da cewa"to ki fadamun wanene ya baki allurar"?Â
 buÉ—e baki tayi zata furta haroon nan take ta sake ji an damÆ™i maÆ™oshinta saboda zafin da taji kawai saita fashe mashi da kuka saboda ta rasa yarda zata yi ta sanar mashi........'Â
 Zuba mata ido yayi yana kallonta tana ta faman shan kuka, tuni yaji tsananin tausayinta ya kamashi,musamman daya dinga ganin fuskarta kamar su jahad ne ke kuka,Â
  Cikin sauri ya dakatar da ita da cewa"its okey, kiyi hakuri banyi hakan dan na 6ata maki rai ba, inaso kawai na gano wanda ya baki allurar ne don inyi investigation akan shi, amma tunda bakison faÉ—i, zaki iya tafiya,Â
  tsagaitawa tayi da kukan tana kallon shi cikin sanyin murya tace"dan Allah kada ka zargeni wlh bazan iya cutar da wani acikin gidan nan ba, saboda na ɗauke ku tamkar ƴan uwana na jini na.......'
   murmushi Omar ya ɗanyi kafin yace"don't worry ur self nima kamar yarda kika ɗauke mu haka muka ɗauke ki, ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce insha Allah,amma aduk lokacin da kika tuna sunan wanda ya baki ita, ki hanzarta sanar mun pls......'
  "Insha Allah zanyi hakan," tashi tayi tare da yi mashi sallama ta nufi hanyar fita daga falo dinsa, a hankali take tafiya hannunta dafe da saitin zuciyarta, muryar shi ce, ta sake katse ta da cewa"yana buƙatar a gyara mashi bedroom ɗinsa yakamata ki je, a firgice ta juyo tana kallon shi, ganin yarda ta razana ne yasa shi cewa"ki kwantar da hankalin ki, kada abunda ya faru jiya yasa ki dinga jin tsoranshi, nasan ko wanene ɗan uwana, am really proud of him, ki saki jikin ki in ba haka ba zai gane cewa wani abu ya faru adaren jiya,
  jinjina mashi kai tayi tare da cewa"toh zanyi yarda kace," tana fadin hakan tasa kai ta fuce,
  Murmushi Omar yayi saboda tunawa da babban aikin da sgr yaso yayi jiya, tabbas da yarinyar ta rasa ranta don ayadda yake jin wannan ƙarfin ba ƙaramin illatata zaiyi ba,
  "godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da yabani ikon zuwa adai dai wannan lokacin har na ceci rayuwarta, na kuma taimaki ɗan uwana daga aikata wannan aika aikan," ya furta yana faman sauke ajiyar zuciya,
*************💋
Gaba É—aya sun hallara a saman dining chairs suna yin breakfast dinsu, Abban su tare da junaid, sai Ayaan da jahan ga kuma su irfan khaleed da jabeer da kuma Fawan, har yanzu bai fara sanya riga a jikinshi ba sai dae gajeran wando kawai yake zurawa yayi ta yawon shi,
 "Aunty azmee ina reesh take ne, banganta ba"? Junaid ya tambaya yana kallon azmee dake tsaye tana saving dinsu,Â
  Abbansu ma yace"tun ɗazu nake so in tambaye ta nima, yau banga daughter ɗita ba ina tashiga ne?
 Murmushi azmee tayi tare da cewa"tashiga sashen Omar ne,"Â
 cike da mamaki jabeer yace"wacece kuma sehrish? ko dai wannan yarinyar dana gani tana yawo acikin gidan nan? Ya tambaya yana kallonsu,
 irfan yace"nima ina taso na tambaya wlh, naga kyakkyawar yarinya tana ta yawo acikin gidan nan gwanin burgewa,"
 da buÉ—ar bakin fawan sai cewa yayi "Oh wai dama mutun ce? Ae ni nayi tunanin ko idona ne ke ganemun ita shiyasa ban ta6a tambaya ba," dariya suka fashe da ita gaba É—ayansu banda shi fawan din da yayi mgnr, saboda shi bada wasa yayi maganarshi ba, duk a tunanin shi ko ya samu ta6uwa ne shiyasa yake ganinta,Â
   "Sunanta Sherish tare da azmee suke aiki, amma na mayar da ita ƙanwarku ina fata zaku ji daɗin hakan, tunda dama baku da ƙanwa mace," acewar abbansu,
  kallon juna su kayi atare kafin fawan ya kuma cewa"ni duk ba wannan ba, wai ina tukur mai aikin mu ne? Nayi kewar shi sosai tunda muka dawo banga gifcin shi ba acikin gidan nan,"? ya tambaya yana kallon junaid dasu twins,
 murmushi suka shiga saki gaba É—ayansu batare da sunce komai ba,Â
  Khaleed yace"wannan sullu6iyon mai aikin namu, dama nasan bazai kai labari ba halan an kore shi daga aikine"?
  Junaid ne yace"kai yaya fawan yanzu kuna nufin baku gane wanene tukur ba? Wannan yarinyar fa itace fa tayi shigar maza tana mana aiki........'Â
 Saboda tsabar ruÉ—u har suna haÉ—a baki wurin cewa"Are u serious!? É—aga kai yayi tare da jaddada masu maganar shi yace"of course ku tambayi abba kuji,"Â
  Kallon abban nasu sukayi suna jiran jin bayani murmushi yayi tare da cewa"itace mai aikin da kuka bari a matsayin namiji,"Â
  cikin mamaki suke kallon shi sam sun gaza cewa komai saboda abun yafi Æ™arfinsu wai tukur mai aikinsu ne ya koma mace ? dama maca ce tayi shigar namiji kenan? Murmushi fawan yayi aranshi yace "lallaikam nama har gida," kamar abbansu yaji mai yace sai É—agowa yayi ya kalli fuskokinsu yace"ko da gigin wasa bana son wani ya ta6a mun É—iyata,ko kallon banza wannan ban amince wani yayi mata ba,"Â
  har suna haɗa baki wurin cewa"Insha Allah hakan ma bazata faru ba, ae ƙanwarmu ce," dariya junaid yayi ƙasa ƙasa saboda yasan halinsu sarai musamman fawan,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.