Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
tun bayan da Drivern ya turama Amani adireshin wurin inda suke shiru bata ƙaraso ba,gashi dare sai ƙarayi yake,kuma babu wani passenger daya rage acikin station ɗin sai ita kaɗai kwallin kwal,sai kuma wasu daga cikin mazauna station ɗin,tana zaune acikin motar baiwar Allah ba ƙaramin galabaita tayi ba,ga gajiyar tafiya ga kuma ciwo da take fama dashi,don har yanzu zazza6in nan bai bar jikinta ba,ganin cewa zasu 6ata mashi lokaci gashi yana da wani uzuri mai mahimmancin da yake so yaje yayi,hakan yasa yace ma Amal ta fito daga cikin motar,daƙyar ta iya miƙewa tare da saukowa daga cikin motar ta fito waje tare da tsayawa tana jiran jin me zaice,
Ruƙo hannunta direban yayi sannan yajata izuwa wurin wani benci yace ta zauna anan ta jira ƴar uwarta tazo,kada taje ko'ina,shi zai wuce don yana da uzuri,
 Hankalin Amal ba ƙaramin tashi yayi ba ganin direban zai tafi yabarta acikin station ɗin gashi babu wata ƴa mace aciki sai ita kaɗae,
 Shi kanshi baiso hakan ba,saboda amanace aka bashi,amma ba yarda zaiyi,ya zamar mashi dole ya juya ya koma da motar,
  tana ji tana gani direban nan ya shige motarshi tare da janta yabar cikin tashar da ita,
 Lokaci guda wani irin sanyi ya lullu6eta,nan da nan jikinta ya shiga rawar ɗari,hatta haƙoranta sai faman kakarwa suke yi suna fidda sauti kaf kaf suna game wa da juna,ƙanƙame jikinta tayi tana ta faman ambaton sunan Allah abakinta,
 Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutane daga gefen hagunta,cikin sauri ta juya don taga su wanene,gabanta ne yayi wani irin faɗuwa ganin wasu giggan tantirai su uku suna tunkaro wurin da take,sai faman nunata sukeyi da hannu da alama ma abuge suke,sun sha takai masu karo suna tafiya suna tangal tangal kamar zasu faɗi,
  ganin hakan yasa Amal ta miƙe cikin sauri ta soma tafiya tana waiwayonsu,muryar wani daga cikinsu ne tajiyo yana cewa"kai karfa ta kufce mana,naga kamar tana so ta tsere mana," haba ina ae Amal na jin wannan maganar ta manta da yanayin da take ciki,takai hannu tare da tattare rigar jikinta ta watsa aguje kamar zata tashi sama,suma ganin ta fara gudu yasa suka bi ta aguje don su taddota,
  Gaba ɗaya duk tabi ta rikice tana gudu tana waiwayonsu hakan yasa ta hau saman titi batare da saninta ba,kafin tayi wani aune tuni wata mota tayi awon gaba da ita,wata irin razananniyar ƙara Amal ta saki yayin da ta baje asaman titin idonta na kallan sama,jini na zuba ta saman goshinta da kuma hancinta,da la66anta duka sun raunata,
  Waro ido waje tantiran nan sukayi ganin abunda ya faru,aikuwa a gaggauce suka zura da gudu don kar ace sune suka kashe ta,
   Hankali tashe suka tsayar da motar,sannan atare suka fito daga cikinta da hanzari suka tunkari wurin da yarinyar take kwance,gaba ɗayansu suna sanye da kakin sojoji ajikinsu,
   Zuƙunnawa daya daga cikinsu yayi yana kallon fuskar yarinyar dake ta faman faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"
  "bata mutu ba,har yanzu tana numfashi amma tana bleeding ya kamata muyi saurin kaita asibiti,"
  Na zuƙunnan ne yayi magana,sannan batare da 6ata lokaci ba,yasa hannunshi tare da sungumarta asaman kafaɗarshi cikin sauri suka wuce da ita cikin motarsu,a back seat ɗin motar ya zaunar da ita,sannan shima ya shiga daga gefenta ya zauna tare da ruƙota jikinshi,
 Shi kuma ɗayan ya shiga gaban motar tare da yi mata key,yaja ta aguje suka juya domin zuwa kai yarinyar asibiti,
  Adai dai lokacin da Motar tasu take ƙoƙarin shiga shantalelen titin dake a left hand dinsu,Motar Amani ta kunno kai ta titin dake a right-hand ɗinsu, a wani slow Amani ta zuge glass ɗin motarta tana bin tasu motar da kallo saboda kukan mutum da tajiyo acikin motar ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba,aranta tana cewa"Allah yasa dae ba wani mummunan abunne ke faruwa acikin motarcan ba,"
 Tana ƙarasa maganar taja motarta da gudun gaske ta ƙarasa cikin tashar motocin,wuri ta samu tare da yin parking ɗin motar,cikin sauri ta fito tana faman gyara mayafin dake ajikinta,hannu tasa tare da ciro wayarta dake acikin purse ɗinta,sannan ta dannawa direban kira,cikin rashin sa'a aka sanar da ita cewa numbar da take kira a kashe take,
  hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,
 A ruɗe ta soma cewa"kodai ƙarya mutumin nan yayi mani ne?amma meyasa zai kirani a waya ya sanar dani cewa ƙanwata Amal ya kawo Abuja,kuma sannan yanzu na kira wayar shi a switch off,Ya ilahi amma dae bai kyautamun ba wlh,"
  tana cikin wannan zancen zucin sai ga waɗannan tantiran guda uku da suka biyo Amal,ganin su yasa Amani tayi tunanin ko ta tambayesu may be a dace,
 da hanzari ta tunkare su tare da yi masu sallama,
  a firgice ɗaya daga cikinsu ya shiga cewa"wlh ba mu muka kashe ta ba,kawai mun ganta ne acikin tashar nan zaune ita kaɗae,shine muka biyota don mu tambayeta ina iyayenta suke ne...."tun kafin yakai ƙarshen maganar tashi wani daga cikinsu ya buge mashi baki tare da cewa"Ƙarya Haramun!Aunty bari na faɗi maki gaskiyar lamari,mu ɗinnan da kika ganmu 6arayi ne masu yankar aljihu,mun biyota ne domin mu kwamushe ƴan kuɗaɗen dake hannunta tana ganin mu sai ta watsa aguje,tana ta faman gudu kamar zata tashi sama kawai sai ga wata mota tayi Wuff ta ɗauke ta sama........'
 gaba daya basu acikin hayyacinsu da alama giyar ce takai masu karo,sai faman kora mata bayanin abunda bata tambayesu ba suke,
 Murya na rawa Amani tace"dan...Allahh ban gane akan me kuke magana ba?wacece kuma kuka bi aguje har mota ta buge ta?wace yarinya ce,!kuyi mun bayani,ni ina neman ƙanwata ne Amal,ɗazu wani driver ya kirani a waya ya sanar dani cewa ya kawota inzo in ɗauke ta kuma shine ma yaban addreshin wurin nan,"
 Har haɗa baki suke yi wurin cewa"ae itace yarinyar da muke yi maki magana akai Aunty,ae yanzu haka ma yarinyar tana acikin motar waɗanda suka banketa,yanzun nan suka bar wurin nan da ita,
 Tun kafin ya ƙarasa maganar Amani ta juya da saurin gaske ta nufi motarta saboda tunawa da tayi da Motar da tagani ta gifta ɗazu da kukan yarinya acikinta,
 buɗe motar tayi tare da shigewa ciki taja ta da gudun gaske,tana jiyo muryar waɗannan matasan suna cewa"Aunty Allah tsare hanya,"
 Â
   ***************************
SEHRISH
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.