Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
Cikin sauri Amani ta sauko down stairs jikinta har rawa yake yi ganin Azmee na jera masu breakfast a dining table, yasa cikin sauri ta wuce wurintaÂ
 Azmee naganin ta ta soma sakin fara'a tana cewa "aaa yau kune agidan namu? saukar yaushe,"
Batare da Amani ta amsa mata ba tace "Yawwa Aunty azmee dama akwai abunda nakeso na tambaye ki,"!
 Cikin mamaki azmee tace "meke nan"?
 "Ga me da Yarinyar dana gani acikin gidan nan, wata ƴar matashiyya shin ita ɗin jinin su Abba ce?
 murmushi azmee ta saki aranta tace "Gulma ajali, in ba'ayi ba a mutu," a fili kuma tace "abokiyar aikina ce a aka kawo don ta runƙa tayani aiki,"
 yamutsa fuska amani tayi kan ta yagama ɗaurewa ta kuma cewa "ƴar aiki fa kika ce? But i was confused ya akai naganta cikin uniform kuma har junaid na kiranta da ƙanwarshi? Kuma naji Abba ma ya kirata da My daughter,duk kuma a matsayin mai aikin?
 dariya azmee tayi ganin yarda amani ta ɗaga hankalinta akan sehrish
 "tabbas mai aiki ce itama, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyarsa,bata da banbanci da sauran ƴa'ƴanshi a yanzu, saboda yana son Yarinyar sosai,"
 Jin haka yasa Amani ɗan zaro ido waje bata ƙara cewa komai ba saboda wayarta da ta ƙara yin ringing, cikin sauri ta zura hannu tare da buɗe handbag din ta zaro wayarta, tare da duba screen din wayar don taga mai kiranta, sunan Aunty laila ne ya bayyana asama, kallon Azmee tayi tare da cewa "ina zuwa," tayi maganar tare da kama hanya ta danyi nesa da azmee sannan ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta tana cewa "barka da safiyya Auntyna fatan kin tashi lafiya,"
Murmushi Aunty babba tasa ki daga can 6angaren tace "Lapiya lou Alhmdllh my sister, nazo maki da labari mai daÉ—i ina fata kina da kunnan saurara,"
 Amani tace "nima ae ina tafe da labari zazzafan gaske, amma bansan wa zai fara bada labarin shi ba acikin mu,"Â
 Saurarawa tayi tana jiyo dariyar aunty babba ta cikin wayar sai da ta tsagaita da dariyar sannan tace "ina tunanin labarina yafi naki daɗi kuma zaifi ƙayatarwa, bari dae ni nafara baki,"
 murmushi Amani tayi tamkar tana agabanta tace ina sauraronki auntyna,
 gyaran murya Aunty babba tayi sannan tace "ina yaran nan da nake baki labari Omar ya kawo mun gidana?
 Amani tace "eh nagane su,"
Aunty babba taci gaba da cewa "ae tuni nasa an kwashe su, an jefar mun dasu bayan gari,yanzu haka hankalina kwance na rabu da alaƙaƙai, yanzu banda wata sauran damuwa saura target ɗina nagaba nake jira...." tunkan taƙarasa maganar Amani ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya,
Jin dariyar da amani keyi ne yasa aunty babba dakatawa da maganarta tana sauraronta ta cikin wayar, ganin cewa amani bata da alamar jinkirtawa da yin dariyar da takeyi ne yasata cewa "ke bana son iya shege, na ji kina mun dariya kodai daÉ—in labarina ne yasa ki jin daÉ—i har haka," ta tambaya tana jiran jin mai amani zata ce,
 daƙyar Amani ta tsagaita da yin dariyar sannan tace "Aunty laila an fa yanka ta tashi,labari da ɗumi ɗuminsa idan ma kina atsaye to wlh ki zauna don kar in sanar dake ki yanke jiki ki faɗi,"
 Jin maganar Amani yasa hankalin aunty babba É—ugunzuma,murya na rawa tace "ba atsaye nake ba,ina zaune saman 2 seater ne ina shan tea,dan Allah ki sanar mun wane irin labari ne wannan,"Â
 wani irin shu'umin murmushi amani tayi kafin ta soma cewa"Yanzun nan muka zo gidansu Abbas saboda mu duba jikin fawan da miyagu suka kai masu hari, ina fata kinsan wannan labarin"? Ta tambaya tamkar tana agabanta,
Aunty babba tace "eh nasani,ae muna nan muma zamu zo tare da ishaq don mu duba jikin shi,"
 Jinjina kai Amani tayi sannan taci gaba da cewa "Shin ko kinsan cewa akwai wata matashiyyar yarinya kyakkyawar gaske da muka tarar acikin gidan !!!'
 darammm !!!gaban aunty babba ya faɗi rasss a firgice ta saki cup ɗin dake hannunta ya tarwatse ƙasa, zumbur ta miƙe tsaye tana cewa "kamarya Amani ! Bangane abunda kike cewa ba anya ba kunne na bane suka jiyo mun hakan"?
 dariya amani tayi kafin tace "ba kunnanki bane Aunty laila,zahiran ne wannan nake faɗa maki, wlh da ido na naga yarinyar,kyakkyawar gaske har na tambayi azmee nake cewa wacece ita yarinyar kodai cikin danginsu Abba take, sai azmee ke sanar dani cewa house maid ce itama amma Abba ya mayar da ita tamkar ƴarsa, har fa school sun sanya yarinyar babban abunda zai tayar maki da hankali sai kin ga yarda Abba ke kiranta da ɗiyarshi, yarinyar ba ƙaramin wuri ta samu ba.......
Fuska a damuje aunty babba tace "nifa hanyanzu ban fahimta ba, shin yarinyar ƙarama ce sosai ko babba"?
 Amani tace "ina fa, wlh balagagga ce nace maki fa matashiyar budurwa kyakkyawar gaske mai cikar sura,ni kaina dana kalle ta sai da gabana ya faɗi to ina ga matasan gidan da suka kasance maza ne dukansu,
 Jin wannan maganar yasa aunty babba dake atsaye tana zarya a falon nata, aza hannunta na dama akanta, ɗayan kuma na ruƙe da wayar tashiga cewa "Ae shikenan wlh an yanka ta tashi, ni ina nan sake da baki ina murnar rabuwa da waɗancan tagwayen da Omar ya kawo min ashe abanza ga wata can ta riga ƙetare iyakar da bana so aje,amma an gama dani wlh ya akai har takai wannan lokacin gidan baki sanar dani ba,"? ta tambaya a kiɗime,
 Amani tace "nafa ce maki ni kaina bansan da zamanta ba, yau É—in nan muka ganta kwatsam tafito É—as da ita cikin school uniform wlh abun ba'a magana yarinya haÉ—aÉ—É—iyar gaske,tasamu wuri fa sosai agidan, kuma yarda naga Abbansu na kiran sunanta da daughter dinshi kinga kuwa hakan na nufin nan gaba ma da sunan Surikata zai kirata,"Â
 ƙasa Æ™asa amani ke sakin dariya tana sauraron aunty babba dake faman Zabga salati, dama dagangan take tunzurata don ta rikitar da ita,Â
"Nashiga ukuna,wannan masifar har ina matashiyar budurwa kuma agidan surikina, wlh hakan bazai ta6ayiyu ba, wlh saina son yarda zanyi na rabata da gidan, badai zamu zo da ishaq ba hmmmm zanganta ne !! zanga KOWACECE ITA 😳😳😳
 Sun jima suna waya da aunty laila kafin daga bisa ni sukayi sallama da juna amani ta koma daga ciki, ranta fess don tasan yau ko bacci aunty babba bazata iya yi ba har sai taganta a Abuja, gata ga yarinyar data bata labarinta,
Fitowa hafsat tayi daga bedroom ɗinta jikinta sanye da sleeping dress ganin mommyn nata tsaye tana ta faman zarya a falon tana zazzaga bala'e ita kaɗai kamar zararriya, hakan yasa hafsat ƙarasawa kusa da ita tana cewa "wai mommy lafiya kuwa kike ta faman tada jijiyoyin wuya duk akan wanene?
Uban tsoki Aunty babba ta saki sannan tace "wani mummunan labari amani ta sanar dani yanzun nan, wlh nagaza samun natsuwa, so nake kawai naganni a abuja wlh,"
 Wuri hafsat ta samu tare da zama saman 2 seater sannan tace "mommy wannan wane irin labari ne haka daya tayar maki da hankali haryasa kika fasa cup ɗin da kike shan tea dashi," tayi maganar ayayin da take kallon kofin da aunty babba ta saki ƙasa ya fashe,
 juyo tayi ta kalle ta rai a6ace tace "ba dole hankali na ya tashi ba, ina murnar rabuwa dasu hossana da jahad sai gashi yanzu Amani ta kirani awaya tana sanar dani cewa sunje gidan su Abba, sun tarar da wata matashiyar budurwa wai mai aikice fa, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyar cikinsa," tayi maganar tana huci,
 Shiru hafsat ta ɗanyi na wani lokaci kafin daga bisa ni ta saki ƙayataccen murmushi tace "Mommy kenan, dama kina tunanin haƙƙinsu hossana da jahad zai barki ne? to inaso ki sani haƙƙinsu ne yafara bibiyarki, kuma ba zaki ta6a cin nasara ba akan wannan yarinyar da aka baki labarinta yanzu, saboda mommy sam baki kyauta ma rayuwar yaran nan ba, basu miki laifin komai ba kinsa an kwashe su,ki kayi mun ƙaryar cewa gidan marayu za'a kaisu ashe zubar dasu kikasa ayi,yanzu wayasan wani hali suke ciki.........' hawaye ne suka soma zarya a fuskarta saboda raɗaɗin da take ji aduk lokacin da ta tuna dasu hossana da jahad,tun jiya da aunty babba ta sanar da ita cewa ba gidan marayu tasa akaisu ba, zubar dasu tasa ayi bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, abun namata ciwo azuciyarta
. kallonta kawai aunty babba keyi ganin yarda take zubar da tears ɗinta akan tsintattun yaran da bata haɗa alaƙar komai dasu ba,
 tsoki ta sake ja tare da cewa "kin dai ji haushin rayuwarki wlh, saboda waÉ—ancan marasa galihun kike ta faman sharara kuka,har kina ikirarin haƙƙinsu ne ke bi na,to ki zuba ido ki gani saina sa anyi waje da waccen yarinyar da amani taban labarinta,"Â
 afusace hafsat ta miƙe tana kallonta tace "mommy! Ina miki fatan nasara," tana fadin hakan ta juya tare da komawa bedroom ɗinta,
 Jinjina kai aunty babba ta shiga yi tana faman sakin huci kamar zakayan, afili tace "Tabbas dole nasan kowacece wannan yarinyar dake Æ™oÆ™arin tarwatsa mun plan É—ina, yakamata nasan abunyi dole na kira HAYAAM awaya in sanar da ita cewa ta tattaro kayanta itama ta koma gidan da zama, tunda har Æ´ar aiki ta samu irin wannan gatancin ina ga ita da take Æ™anwata !!!!!!ðŸ¤
 Sai faman balbali bala'e take yi ita kaɗae tana ci gaba da zarya a falon,
*******************************
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.