Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
tunanin nata da cewa"dagaske ne abunda ya faɗa"? ya tambaye ta yana jiran amsa,ba komai yasa shattima sakin jiki da sehrish ba face tun da yaga yarinyar da suka shigo ta gaishe shi da ya kalle ta ba fuskar kowa ya gani ba a fuskarta ba face fuskar SGR bi ma'ana sun dace sosai,saboda tunda yake arayuwarshi bai ta6a ganin yarinyar da ta dace da Sgr ba face wannan yar matashiyar duk da ya lura cewa kamar tayi masa ƙanƙanta,yarinya ce ssae amma kuma tana da duk wani abu da namiji zai buƙata ajikin ƴa mace,🥱  A hankali sehrish ta buɗe bakinta tare da cewa"hakane gskya ya faɗi....." daƙer takai ƙarasa maganarta, cikin sauri tace"kuna buƙatar wani abu"? shiru shattima ya ɗanyi saboda ya lura da chanjin da yarinyar tayi,kuma yasan saboda kalaman sgr ne,may be tana son shi ne da alama, ya faɗi aranshi a fili kuma yace"just its okey zaki iya tafiya,mun gode da wannan,"  Murmushi ta ɗanyi sannan ta juya da sauri saboda kukan daya ciyo ta har takai bakin ƙopa ta ɗan juyo tana kallon shi, anatse yake yin wayarshi ya jingina bayansa ajikin kujerar,sa kai tayi ta fuce wuri tasamu anan upstairs ɗin ta zuƙunna ta cigaba da shan kukanta jikinta har rawa yake yi,tuni eyes dinta sun canza launi, fuskarta ta tur6une saboda kuka sai faman murzar hancinta takeyi kamar zata 6alle shi,sam ta manta da aikin dake gare su a kitchen su azmee nacan da amani sun taƙarƙare suna ta aikace aikace ba sehrish, gashi Amani sai faman tambayar azmee take yi na cewa har yanzu yarinyar bata dawo ba daga kai ma Sgr coffee,ko mai ta tsaya yi? Ita dae azmee bata ce komai ba, da tacika ta da tambayar ne tace"may be shi ya tsare ta,kinsan ita ke kula da apartment dinsa, Jin hakan ba ƙaramin tayarwa Amani hankali yayi ba,daure wa kawai take yi tana aikin,   Hawansa kenan upstairs ɗin ya miƙi hanya yana cikin tafiya yaji shessheƙar kukan ƴar mace,mamaki ne ya kama abbansu ganin yarinyar zukunne ta takure kanta sai faman matse hanci take yi tana kuka,tuni hankalinshi ya tashi ƙarasawa yayi inda sehrish take zukunne,a firgice ta miƙe tsaye lokacin da tayi arba da Abban nasu sam bata lura dashi ba sai da taji takon takalminsa na tunkarota,   lokaci guda ta rikice duk ta susuce tsoranta mai zata sanar mashi in ya tambayeta dalilin yin kukan nata,  Ko da ya isa dab da ita sai ya tsaya yana ɗan nazarin fuskarta,tsananin tausayin yarinyar ne ya kama shi,dama ita mace abun tausayi ce musamman in ta kasance ba'a gaban iyayenta ba,babu kowa nata a kusa da ita da zai lallashe ta ya kuma janyo ta jikin shi don jin damuwarta,ya mayar da ita yar shi amma kuma bai da isasshen lokacin jin abunda takeso ko me ke damunta,   Sunnar da kai sehrish tayi ƙasa murya na rawa tace"ina yini abba,"  bai amsa mata gaisuwarta ba sai cewa yayi"meya faru ne naga kina kuka? cikin en ina tace"babu komai," hannun shi yakai gefen fuskarta yace"ko da zaki yi ma kowa ƙarya,kada kice zaki yi ma abbanki,ga hawaye nan nagani suna zuba a idonki,kawai dai bakya son faɗamun ne," shiru tayi bata ce komai ba tana faman wasa da yatsun hannunta,  Murmushi yayi ganin tana ɗan satar kallon shi kamar wata mara gaskiya,  Cikin zolaya yace"faɗa mun gaskiya kodai aure kikeso ne?kin rasa wa zaki faɗamawa shine kika la6e anan kina kuka ko"? ɗagowa sehrish tayi taɗan zare ido can kuma ta fashe da dariya gaba ɗaya, shima dariyar yayi dama yayi hakan ne don yasata farin ciki yasan mata daga anyi masu maganar aure sai jin kunya da dariya,  ganin haka yasa shi ƙara cewa"hmmmmm dama nasani,mu aje wannan maganar a gefe nasan cewa akwai wanda kike so acikin ƴa'ƴana don na iya haihuwa gasu nan tubarkalla masha Allah ƴan mata sai rububi sukeyi hada masu kirana awaya duk safiyar Allah suna gaishe ni wai nan suna yi ma kansu ko ƴa'ƴansu kamun ƙafa,ni kuma har yanzu basu kwanta mun araina ba,Amma ke ɗin nan ko ta dabance in har kinaso in baki ɗaya daga cikinsu dole kema ki fara kamun ƙafa daga yanxu," Magana yake a natse sehrish kuwa ta kasa kunne tana sauraron shi,mamaki ya gama kamata yarda Abban nasu sukutun da guda yake fira da ita lallai ba ƙaramin wayayyen mutun bane,  bayan yakai ƙarshen maganar tashi tace"amma Abba,ni bansan yarda ake yin kamun ƙafar ba," ta faɗi cikin jin kunya,  dariya yayi tabi shi da kallo sai taga ya koma mata junaid saboda tsananin kamanceceniyar dake a tsakaninsu don dai shi fuskarshi akwai manyantaka, Bayan ya tsagaita da dariyar yace"kina nufin baki san yarda ake kamun ƙafa ba in mutun nasan abu,to ki tambayi AZMEE ta faɗa maki zata koya maki,  Jinjina kai tayi tare da cewa"insha Allah zan tambayeta,"  Murmushi yayi kafin yace"daga ynx zan fara zuba ido in ga yadda zaki fara kamun ƙafar naki,idan kinyi abu mai kyau sai na duba na gani wanne ya dace acikinsu na baki,idan marks ɗinki yakai matakin A1 to zan aura maki ɗaya daga cikin manyan ne, idan kuma Credit kika samu zan haɗaki da ɗaya daga cikin youngers ɗinsu,amma fa ki sani idan marks ɗinki yazo da matsayin(f)to zan aura maki Haroon ne........... " dariyar da sehrish ta fashe da ita ne ya hana shi ƙarasa maganar, zuba mata ido yayi yana kallonta sai ya dinga ganin kamanceceniyar fuskarsu da ta yarinyar sam yarasa gane dawa take masa kama nan da nan kan shi ya ɗaure yashiga mamakin kamannin daya gani kodae idonshi ne ke nuna mashi hakan tabbas fuskarta tayi tamkar photocopy ɗin fuskar ƙanwarsa AZEEMA,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.