Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
ba ita bace ya gani acikin daji ba sume cikin ciyayi,ba don akwai dressing na ciwo a forhead dinta ba, da bazai iya shaida taba, .murmushi kawai yayi tare da miƙa mata ledojin hannun shi, cikin sauri tasa hannu ta kar6a tana yi masa godiya,  Har ya juya zai fita sai kuma ya juyo ya kalle ta yace"pls game da abunda ya faru da ku a gidan yayan Omar,wurin matar yayan shi kada ku sanar dashi komai don nasan zai tambaye ku ne,  Murmushi jahad tayi tace"insha Allah ba zamu sanar mashi ba,"  "Yawwa" ya faɗi tare da juyawa yasa kai ya fuce,   Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajiye ledojin a saman table,tana jiran su kammala kimtsa wa su fito suci atare,   Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana faman sakin murmushi,bakowa ne ke faɗo mata aranta ba face yaya Omar dinsu,ta ƙosa ta sashi a idonta saboda tayi mashi godiya sosai,kuma tayi missing din wannan kyakkyawar fuskar tashi,   tana cikin wannan tsayuwar sai ga Camila ta fito fes abunta har ta canza kayan jikinta,v neck shirt ce ajikinta fara sai wando jeans, ta ɗaure sumar kanta da ribbom,fuskarta asake ta ƙaraso tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna tana kallon jahad tace"kina so ciwon naki ya dawo sabo mu koma asibiti gobe ko?  Girgiza kai jahad tayi tare da cewa"a'a bansan na take ta bane,ciwon bai mun zafi yanzu ina ji kamar naji sauƙi ma,"   Tace "duk da haka yakama ki kula just in case,"  Amsa mata tayi da toh sannan tace "ga abinci nan,an aiko mana shi," ta fadi tare da ƙarasawa wurin table ɗin ta matsar mata dashi kusa da kujerar da take zaune,   Sannan itama ta samu wuri ta zauna a kusa da ita,hannu camila tasa ta buɗe ledar ta farkon,kayan ciye ciye ne gasu nan chips, bugger, shawarma da sauran wasu tarkacen, ɗayar ledar kuma da ta bude masu fried meat ne (tsiren nama) mai yawan gaske yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,  Dole ne su buƙaci plate don haka jahad ta tashi tare da cewa "bari na ɗauko mana plate," camila tace "plate yayi kaɗan tray zaki samo mana," Amsa mata tayi sannan ta tunkari doors din dake a cikin falon tana neman kitchen babu alamar kitchen na a wurin,  "Ki duba down stairs baza arasa acan ba," acewar camila,  Cikin sauri jahad ta hau benen da zai sauke ta a dowm stairs tana sauka cikin sittingroom din ta hango kitchen ɗin, tasha mamakin ganin yarda aka ƙawata ɗakin,  Cikin hanzari ta wuce kitchen ɗin an tsara shi sosai,ƙarasawa tayi jikin kitchen shelves anan ta samu trays a jere ta ɗauki ɗaya,komai na cikinsa sabone wasu acikin kwalinsu wasu kuma a buɗe suke, tare da cokali ta haɗo masu da knife saboda taga tsiren naman basu zuge shi ba acikin tsinken shi yake,zasu buƙaci su yayyanka shi in zasu ci,  Fitowa tayi daga kitchen ɗin sannan ta koma upstairs ɗin, tunkan ta ƙarasawa ta samu hossana zaune agefen camila hannunta ɗauke da tsiren naman nan ta tura abaki sai ci take kamar kura,hankalinta kwance, bakomai bane ya burge jahad ba face ganin yarda hossana tayi wani irin kyau cikin gajeran skirt mini tare da riga ƴar t shirt tabi shape din jikinta, hada ƴar hoda ta shafa ma fuskarta da jan baki,   Ganin jahad ta soma washe mata baki, girgiza kai jahad tayi tare da cewa "dama nasan dole kiyi ƙara'e hossana irin wannan ɗaukar wanka haka,"   "Kaɗan kika fara gani ma,aunty camila ma tace in ta samu hutun aiki zata kaimu saloon a gyara mana gashi tare da ƙunshi ma duka za'a yi mana,"  murmushi jahad tayi a lokacin taƙarasa wurin table ɗin, aza tray ɗin tayi asaman shi sannan ta samu wuri ta zauna itama suka saka Camilla a tsakiyarsu,   ita ta baje masu tsiren acikin tray ɗin ta jera masu shi,sannan ta zuba masu chips ɗin daga gefe,   Nan fa suka gyara zama duka ukun suka tasar ma kayan lashe lashen, ba baka sai kunne, ba kaji komai sai sautin taunar shi da suke abakinsu,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.