Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
After some minutes,ta fito daga cikin toilet ɗin jikinta ɗaure da farin towel,jikin nan nata har wani ƙalli yakeyi saboda hasken fatarta ga gyaran da take sha,agaban mirror ta tsaya tana ɗaure sumar kanta mai tsayi da yawan gaske,tana da yalwataccen gashin kai wanda yakai har qugunta,tana cikin ɗaure gashin kan nan nata kwatsam taji anyi mata gyaran murya abayanta,a firgice tajiyo don ta ga kowanene,lokacin da tayi arba da mutumin da yayi mata gyaran muryar acikin ɗakinta nan take ta zazzaro ido amatuƙar tsorace take kallonshi,
 kwance yake asaman gadonta,ya miƙe ƙafafunshi yayin da hannunshi ke ruƙe da brazier ɗinta da ta cire kafin tashiga toilet,sae faman latsa breast curve ɗin yakeyi cike da tsokana,
 Hankali a matukar tashe abu tace"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...Nashiga uku....!'gaba daya taba ma ranta cewa al'jani ne shi,ba kowa bane wannan face saurayin nan daya tsoratar da ita da motarshi akan hanyarta ta dawowa daga islamiyya,shi da budurwarshi,
Muryarta na rawa tace"wa..wanene...kai dan Allah!me kakeso a wurina ne!taya akai kasan gidan mu har ka biyoni É—akina"?
 Ƙayataccen murmushi ya saki tare da cewa"bani da amsar tambayoyinki,ni dai kawai nagani inaso,in kika yi mun biyayya mu rabu lafiya,koda yake bazama mu ta6a rabuwa ba,saboda kinyi mun wlh," ya ƙarasa maganar tare da kai bakinsa ya manna ma bra ɗinta kiss
 Runtse ido abu tayi agigice ta fasa ihu tana neman ɗauki,akan azo a fidda mata aljanin dake aɗakinta,
 Da gudu ta watsa waje babban falon jikinta na kerma ta shiga cewa"Mommy!!mommy!!ya haris!daddy!!dan Allah kuzo ku taimake ni,Aljani aɗakina saman gadona....'
 Jin sautin kukan Abu yasa hankalin Hajiya ameena tashi,da saurin gaske ta sauko downstairs ta nufi wurinta tana cewa"Abu meya faru ne kike ta kwaɗa ihu?
Cikin shessheƙar kuka tace"Wani ne acikin ɗakina saman gadona,bansan ko wanene shi ba,a kan hanyar dawowata daga islamiyya ya tsoratar dani da motarshi,shine yanzu kuma bayan na fito daga wanka na ganshi kwance saman gadona,'
 Cike da mamaki hajiya Ameena tace"Wani kuma!acikin gidan nan saman gadonki?taya akai har ya samu damar shigowa cikin gidan nan....'
 Ba ta kaiga ƙarasa maganar ba,sae ga Abusufyan ya fito daga cikin ɗakin abun,fuskarshi ɗauke da murmushi,
 Ganin shi yasa abu yin saurin nuna shi da hannu tace"Ga shi nan mommy....wlh shine ..Aljani ne,"
murmushi hajiya Ameenatu tayi tana kallon Abusufyan tace"Son sai yau kaga damar dawowa gidan?irin wannan zuwan bazata haka?ka tafi kabarmu da kewarka ko?ko tunanin makaranta bakayi ba,ka kama hanya ka tafi kan abunda bai kai ya kawo ba,'
 Langwa6e kai abusufyan yayi yana tsuke bakinshi alamar an 6ata mashi rai,
...zuru abu tayi tana kallon ikon Allah,aranta tana cewa"Ashe É—an masu gidan nan ne,ni duk atunanina aljani ne shi,amma dae da alama baijin magana sosai,'
 "Pls mom just forget about it,komai ya wuce tunda dae nadawo,"
Jinjina kai hajiya ameenatu tayi,kafin ta mayar da idanunta kan Abu dake tsaye sototo tana kallonsu tace"Calm down ur mind Abuna,wannan da kike gani É—an yayata ne,sunan shi Abusufyan,bai jin magana amma kada wannan ya hanaki sakewa dashi,shima ki É—auke shi tamkar Yayanki Haris,'
 Jiki asanyaye tace"insha Allah mommy,"kafin ta ɗan wurga ido ta kallo shi har lokacin kashe mata ido yakeyi,hakan ba ƙaramin haushi yake bata ba,har tafara jin tsanarshi,
Tun daga ranar da Abusufyan ya dawo cikin gidan abu ta shiga uku dashi,ya hana rayuwarta sakat,duk inda ta sanya ƙafarta yana biye da ita,toilet ne kawai bai binta shi dai kawai burinshi ta sake dashi kamar yarda take shiri da haris,ita kuma tace bazata ta6a ɗaukarshi yayanta ba,saboda bai da kamun kai,bakomai yaja mashi hakan ba face Abubuwan da yake yi mata na rashin kunya,da kuma ƴan mata da take ganinshi tare dasu manne da juna,hakan ba ƙaramin ƙona mata rae yake yi ba,duk a tunaninta Abusufyan ɗan iska ne kamar yana bin mata,saboda ita tayi believing da abunda idanuwanta ke nuna mata,
Ana haka wata rana malamin nan nasu Sayyadi ya ɗaukota daga islamiyya asaman machine dinsa super cub,tun suna akan hanya motar abusufyan ke bin bayansu saboda ya hangota abayan mashin ɗin malamin,ranshi yayi mugun 6aci wani irin kashi ne ya lullu6e shi,saboda ya lura akwai soyayya tsakaninta da malamin nan nasu,babu yarda abusufyan baiyi da ita ba akan ta bari ya dinga kaita school amma taƙiya,da yake tana da kafiya sosai,mace ce mai wuyar sha'ani,
More Hausa novels
Aljanar Fatima Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Hayatul Mahayeen Part One Complete Hausa Novel
By Npeedy
Bakar Masarauta Part One Complete Hausa Novel
By Umar Faruq D
Bahiyya Book One Complete Hausa Novel
By Oum Ameera
Hibbatullah Book 1 Complete Hausa Novel
By Real Maman Teddy
Fadeelah Book 1 Complete Hausa Novel
By Bilyn Abdul
Search across the available chapters.